← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 71

Sashe 7

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta miƙe ta fice, ɗakinsa ta nufa ta na buɗe ƙofa ta hangoshi dunƙule akan gado da alama koh sallah bai yi ba, ɗan murmushi ta yi ta karasa ciki, ta zauna daga gefen gadon ta ɗan shiga bubbuga shi "Honey! Honey ka tashi Safiya ta waye." "Honey breakfast is ready." Buɗe idanunsa ya yi a hankali suka haɗa ido, murmushi ta sakar mishi ta na miƙewa "Ka tashi Safiya ta waye, and don't forget ka yi sallah." Daga haka ta fice ta bar masa ƙamshin ta mai rikitarwa.

Ya daɗe ya na kallon kofar da ta futa kafin ya miƙe toilet ya wuce Ya yi wanke har zai fito sai ya tuna ta ce ya yi sallah, shi ya mance when last ya yi sallah wallahi, alwala ya dauro ya fito, bayan ya shirya ya yi sallah, sallar ma gata ga kamar ta don bai iya ba, bayan ya kare ficewa ya yi, a kan dining ya ganta zaune, tashi ta yi ta na murmushi ta karaso in da yake ta ja hannunsa zuwa dining ɗin ta ja masa kujera ta zaunar da shi.

Ta tsaya ta bayansa ta ɗan ɗuko tare da dafa kafaɗunsa daidai saitin kunnensa ta ce "Good morning Husby, hope u slept well?" Ta karashe ta na hura masa iska a kunne, jinjina kai ya yi, janyewa ta yi daga bayan shi ta dawo ta buɗe warmers tare da jawo plate ta ɗìbar masa abinci, ta ajiye a gabansa sannan ta janyo cup ta shiga haɗa masa shayi sai kallonta yake yi ya ma kasa fara cin abincin, bayan ta ƙare ta miƙo masa cup na tea ɗin bata bari ya amsa ba ta saki cup ɗin ashe bai kama ba, ai kuwa cup din ya faɗo tea ɗin mai zafi ya watso masa ajiki.

Bai yi wata wata ba cikin hasala ya ɗago ya sauke mata wani lafiyayyen mari, da sauri ta dafe wajen jikinta ya ɗan shiga rawa "Ka.....ka yi haƙuri. " Ta ce ta na cire ɗan kwalin ta da sauri ta shiga goge masa jiki, ya na nan tsaye ya hasala, bayan ta ƙare ta dago ta saki wani irin murmushi "Ka yi hakuri ka zauna ka ci abinci Husby ka da ya yi sanyi."

ÆŠan kallonta ya yi cikin mamaki ganin yanda take murmushi duk da marin da ya yi mata "Zauna, zauna mana ka ci abinci." Ta ce ta na zaunar da shi, shi dai sai kallonta yake yi da mamaki, sai kuma ya mai da kallon sa kan abincin da ta ajiye, ya É—auki fork a hankali ya soma cin abinci, ba laifi ya yi daÉ—i kam, tass ya canye komai saboda dama ya na shaye shaye so ya na bukatar abinci da yawa.

Bayan ya kare yasha tea É—inshi sannan ya wuce É—aki, sai da ta gyara wajen tass sannan ta bi shi, ta iske shi ya canza wasu kaya ya na saka agogo, karasawa ta yi ta taya shi sakawa, sannan ta duka ta na É—aure masa igiyar takalmin shi da yake kananan kaya ya saka.

Dagowa ta yi ta na gyara masa kwalar rigar sa a hankali cikin kwantar da murya duk da muryarta a kwance take saboda low pitch sosai take da bata daga murya ta ce "Husby ka ga ban da waya, it's a disgrace a ce matar ka bata da waya, matar the whole Bilal Boukar Sahabi."

Ɗan kallonta ya yi "Ok." Murmushi ta yi "Na gode." Ficewa ya yi bayan ya dauki car key ɗinsa, har ƙofa ta raka shi sannan ta dawo, a palor ta yi zamanta ta kunna TV ta na kallo, ba wai kallon take yi ba tunani take yi.

9:30pm

Ta na zaune palor, ta canza wasu kaya don har girkin dinner ta yi shi kaɗai take jira ya dawo, buɗo ƙofar palor Bilal ya yi ya shigo, ta na ganinshi ta miƙe a hankali ta ƙarasa in da yake "Barka da zuwa Honey." Ta ce ta na amsan ledodin hannun shi, "Yawwa barka." Ya ce ya na wuceta ya zauna saman kujera, ajiye kayan ta yi saman centre table ta nufi kitchen ta ɗauko masa ruwa da drink, zuba masa ta yi acikin cup ta ba shi cikin respect, amsa ya yi ya sha, amsan cup ɗin ta yi bayan ya shanye, murmushi ya yi "Kayan da ke cikin ledar naki ne."

"Ni?" Ta ce ta na nuna kanta sai kuma ta jawo ledodin ta buɗe, sabuwar waya lapatop da kuma headphone, washe baki ta yi "Wow duk nawa ne, Na gode na gode sosai husby, thank u so much." Ta ce cikin Jin daɗi ta na kallon kayan, sai kuma ta tashi a hankali ta zauna saman kujera kusa da shi, ta janyo kanshi ta ɗora saman kafaɗarta ta na shafa kanshi, lokaci daya ta canza murya, munipulatively ta ce "Dama ni na sani, na san ba haka halinka yake ba, mutane kawai sun kasa ganewa ne, Ni na san u will be good to me, and I promise I will be an understanding wife, wacce baka taɓa yi ba, i will be a submissive wife, the way u will never expect, I'll never say no to u, ka ji Husby."

Ta ce ta na ɗago kanshi ta yi kissing goshin shi, "Muje ka yi wanka koh?" Ta ce ta na miƙewa ta kama hannunshi suka yi sama, bayan sun shiga daki ta haɗa masa ruwan wanka sannan ta fito ta bar shi aciki, dakinta ta wuce ta na tunani kwana biyu, Bilal ɗin ya bar shaye shaye kamar yanda ya saba yi, ba wai ya dai na ba gabaɗaya ya rage ne, don idan ya fita ya kan je ya shawo abun shi ne ya yi tatil sai dare yake dawowa, koh yanzu high yake sai dai baza ka gane ba don sun fara sakin shi.

Bayan kwana biyu, babu wani tashin hankali a tsakanin su, babu duka babu zagi don ta kwantar da kai sosai ta na yi masa biyayya komai ya ce ya na so babu musu take yi masa shi, kamar yanda ta ce ne she will be a submissive wife haka kuwa aka yi, ta na yi masa biyayya sosai, kwana huÉ—u da ta yi a gidan sa, zata iya zayyano halayensa, karantarsa take yi, ta na saka ido sosai akan shi, yanzu ta sani ya na da saurin hasala duk yanda kuke da shi idan ya hasala in bai kai hannunsa jikin ka ba baya jin daÉ—i .

Kamar abun ya na saka sa nishadi everytime ya daki mutun it brings him joy, so ta na karantar brain É—insa ne, why is he like that, why does he finds pleasure Idan ya na duka ko kuma ya na assaulting mutun, sannan ya na da kishi mugun kishi ne da shi, ko da wasa ba ya so ya ga matar shi ta na magana da wani namiji, kamar yanda ta ce tun farko, it's going to be educational zama agidan shi, don experiment É—inta ne na Uku bayan su Kawu, her third experiment.

Dole in oder to survive him she most study him like a university course, ta hakan ne za ta iya kare kanta, daga gare shi.

Kamar yanda ta saba yau ma ta na zaune palor ta na jiranshi, don anan take jiran shi har sai in ya dawo sannan ta shige koh karfe nawa zai kai awajen ta na nan ta na jiranshi, saɓanin kullum yau ta na waya ne waya suke yi da Taufeeq besty hadda dariar ta, wanda har ya shigo bata sani ba, ita kuma dai dai ta na cewa "I missed u sosai Taufeeq can't wait na koma makaranta nexweek." Ai kuwa sai a kunnen Bilal ɗin.

Cikin hasala ya taho kamar wani zaki ya kwace wayar hannunta ya na dubawa kuwa ya ga besty ya wani irin yi wurgi da wayar, miƙewa ta yi cikin tashin hankali bai yi wata wata ba ya sauke mata wasu lafiyayyun maruka hagu da dama, da sauri ta dafe wajen jikinta na daukar rawa, hawaye na zubowa daga idanunta, dukanta ya shiga yi ta ko'ina "Uban waye kike waya da shi har kina cewa kin yi missing ɗinsa ashe iskancin da kike yi kenan ban sani ba."

Da karfi ta ce "Ka yi haƙuri wallahi ba kowa bane abokina ne na makaranta tare muke karatu a library. " Hasala shi ta sake yi wai abokin ta, abokinta namiji, da auren shi a kanta take cewa wai ta na missing wani gardi, lilis ya yi maga har bata iya tashi sannan ya tsallakata ya barta wajen.

Ta daɗe a wajen kwance sannan ta miƙe da ƙyar ta wuce ɗakinta ta saka masa key toilet ta wuce ta hada ruwan zafi ta gasa jikinta sannan ta fito daure da towel in da sauri ta nufi wardrobe ɗinta ta buɗe ta na saka hannayenta ta ƙarƙashin kayanta ta jawo keypad, ko da ta duba ta missed call din Taufeeq sun fi ashirin, ta na ƙoƙarin bin kiran sai ga kiran shi ya sake shigowa, ɗagawa ta yi.

Cikin tashin hankali Taufeeq ya ce "Besty hope lafiya kike, bai ni miki rauni ba?" Numfashi ta sauke "Lafiya qlu nake ka da ka damu." Ajiyar zuciya ya sauke "Pls ki kula da kan ki, Naila." Lumshe ido ta yi "Ok na ji." Shuru suka yi, sannan a hankali ta ce "Proceed with the plan accordingly, zuwa gobe da dare." "Ok shikenan." Daga haka suka yi ending call din.

Wucewq ta yi gaban madubi ta tsaya ta na kallon fuskarta da ta kumbura ta yi ja, É—an murmushi ta yi ta na shafa fuskar tata, sai ta É—auki cream dinta ta shiga shafawa, ta saka kayan bacci ta hau gado ta kwanta, jikinta duk ciwo yake yi mata.

Washegari.

11:23pm

Da ƙarfi ya banko ƙofar palorn, ɗagowa ta yi daga ya kar akaifar da take yi ta kallesa, abuge yake kuma da mace ya zo da alama anan gidan zasu kwana, ɗauke kanta ta yi ta cigaba da abun da take yi, ita kuwa yarinyar sai kallonta take yi a ɗage irin na shigo gidan ki babu yanda zata yi, ta na jin su suka haɗe sama zuwa ɗakin shi.
Chapter 7 · 0% Book details