← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 71

Sashe 14

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kuma ya shiga ƙoƙarin saukowa saga kan gadon da sauri ta rikoshi ai kuwa ya rungumeta tare da ƙanƙameta, Taj dake kallon su tun ɗazu ya ƙaraso wajen, ya miƙa hannu zai kama shi Ayan ya yi saurin riƙe ta ya na kallonshi "Abbi I want to stay with her." Shuru ya yi wani abu ya tsaya mishi ga wuya ya na kallon yanda Ayan ɗin sai wani rirrike ta yake yi, shi dama ya san za'a yi hakan tun farko shirin su.

Sake kai hannunshi ya yi zai ɗauki Ayan din amma yaron nan ya sake riƙe ta "I want to stay with mh pretty Dr." Numfashi ta sauke kafin ta fito da shi daga jikinta "Ayan." Ta kira sunan shi, kallonta ya yi hawaye na zuba daga idon shi, ga shi kuka is not good for his condition "Ka saurare ni, ba wai ba zamu sake haɗuwa bane everytime ka zo asibiti u will see me ka ji, ka je gida ka ga mom da mom su na so su tafi gida, sun gaji da zama asibiti, ko kana so wani abu ya samesu ne?" Girgiza kai ya yi "Ok ka je gida ka ji, za ka je gida?"

Gyaɗa kai ya yi "Amma tare da ke zamu je koh." Lumshe ido ta yi ta na rasa yanda za ta yi da yaron, haɗe fuska ta yi ta miƙe "Ok ka je gida an jima zan zo." Sai kuma ta kalli su Mami "Sai anjima Allah ya ƙara sauƙi. " Daga haka ta nufi hanyar ficewa da sauri ya miƙe zai bita Taj ya kamoshi ya na jin zuciyar shi kamar zata fashe saboda takaici, ta na jin kukan yaron ko da ta fita amma dole ta barshi.

Taj kuwa ba zai iya hak'uri ba saboda idan akwai abun da baya so aduniya toh kukan Ayan din ne, saboda haka ko me Ayan ɗin yake so ko da baya son shi sai ya yi mishi shi in dai bai saɓa ma addini ba, ga shi yaron ya na kuka akan wata, wata that is not worth it, kuma kukan baya da kyau kwata kwata ga condition ɗin yaron, bayan son Dr Ameenatu kwata kwata bata yi masa ba, amma me yaron sa ya na sonta ya zai yi dole ya yi ma yaron nasa abun da yake so.

Ajiye Ayan É—in ya yi kan gado ya ce Taslim ta duba masa shi kafin ya dawo, daga haka ya fice, hango ta ya yi ta na tafiya É—aga kafarsa ya yi domin ya cimma ta "Dr Ameenatu." Ya kira sunanta hakan ya sa ta tsaya cak tare da juyowa don bata ma san shi ne yake kiranta ba.

"Na'am. " ta amsa a hankali "I need to have a word with u." "Idan akan bayanan ɗanka ne everything is already........" "This is not about the paperwork. " Shuru ne ya ratsa tsakanin su sannan ta ce "Ka taƙaita ina da aikin yi." Kallonta yake yi cikin wani hasala da jin haushi ya ce "U crossed a line."

"I beg ur pardon. " ta ce irin bata ji ba É—innan "My son." Ya cigaba da cewa "is emotionally attached to u which is unacceptable. " Shuru ta yi ta na kallonshi sannan ta ce "ÆŠan ka." Sai kuma ta dakata "is a six year old child who went through a near fatal neurological crisis and a high risk surgery, Attachment is not a crime."

Sai kuma ta saki murmushi "saboda haka i did nothing wrong." Matsowa ya yi kusa da ita "You are young." Ya ce a daƙile "Too young, and frankly......" Ya kalleta daga sama har ƙasa "Ba ki yi kama da wacce zan yarda da ita akan ɗana ba na lokaci mai tsayi. "

Hannunta ta saka acikin labcoat dinta ta na sakin daria "Oh really? You trusted me enough to cut open his skull." Ta matso kusa da shi "Or have you forgotten that part?"

Dunƙule hannunsa ya yi "Family nane suka yanke wannan hukuncin, ba ni ba." Ya ce tsakanin haƙoransa, kallon shi ta yi straight to the eye da irin kallon nan nata da ta ajiye bayan ta zama likita ta ce "Kuma Ka ga ɗan na ka ya na raye."

Shuru wajen ya ɗauka wani irin shuru sannan ya ce "Ban yarda da likitocin Nigeria ba." Ya ce a daƙile "I made that clear long before today, My son’s medications, his monitoring, his future care all of that will be handled abroad."

Yamutsa fuska ta yi mockingly ta ce "Oooo har na ji ban ji daÉ—i ba." Sai ta nuna kanta "Wow did i brake that recod." Ta ce ta na murmushi mugunta.

Kara hasala shi ta yi "I want you to stop seeing him, Effective immediately." Wani kallo ta yi masa don ita ma yanzu ta fara hasala ta ce "Ba kai ne zaka yanke wannan hukuncin ba." "Not medically."

"Nine zan yanke hukuncin komai akan É—ana."

Takowa ta yi zuwa gabansa "A'a. " ta ce "You don’t, You decide where he lives, who raises him, Makarantar da zai tafi, Amma idan maganar brain ɗinsa ne, the thing that nearly killed him, you don’t outrank physiology."

Wani irin kallonta yake yi "Ki na tunanin ban da ikon da zan yi replacing É—inki ne?" "Na san ka na da." Ta bashi amsa "kuma ban damu ba."

Tsayawa kawai ya yi ya na kallonta.

"I didn’t spend years studying neurology because of your child." Ta cigaba da cewa "I didn’t stand in an operating theatre for fourteen hours because I wanted your approval, I did it because this is my calling."

Ta ja baya ta na bada gab tsakanin su "Idan ka na son wani likita, find one, ni kuma zan bada file É—in yaron ka ba tare da gardama ba."

Ya ce "Zan biya ki ko nawa kike so."

Murmushi ta yi "No amount of money, babu kalan kuɗin da zasu saye ni." Kallon face ɗinta yake yi ya na so ya ga weakness ɗinta "Idan ɗana yaƙi fah?" Nan da nan jikinta ya yi sanyi ba don shi ba sai Ayan da ya faɗo mata arai, amma ta dake ta ce "Then u deal with that, ai kai babanshi ne."

Numfashi ya sauke "You don’t understand the world I live in." Kallon shi ta yi idanu a karo na karshe ta ce "And you don’t understand the one I saved him from." Daga haka ta juya ta yi tafiyarta.

Kallon ta ya tsaya yi da mamaki, da gaske bata saurare shi ba, da gaske she turned down his proposal, ko bata ji ba ne, ya ce zai bata ko nawa take so, why is she denying it, da gaske ne kuÉ—i ba sa gabanta? Coz he really don't understand juyawa ya yi ya koma cikin É—akin, ayan na ganinshi ya shigo ba tare da Naila ba ya soma kuka.

ÆŠaukan shi ya yi dama sun kai kaya mota ficewa suka yi amma sai kuka yake yi.
*___*
A hankali ya shigo corridor ɗin da aka faɗa masa ɗakin da yake, bai ɗade da shigowa ƙasar ba ya na karasawa gida aka ce masa ai ƴan gidan basu dawo daga asibiti ba, he was surprised don tun dazu ya kamata ace sun dawo gida, makullin mota ya ce a bashi, ana ba shi ya fice zuwa parking lot ya shiga mota ya fito zuwa asibiti, kallon room number yake yi.

Tun daga nesa ya jiyo kukan shi hakan ya sa ya ɗan taka da sauri dai dai Taj na karasowa ɗauke da shi, da sauri ya saka hannu ya amshi yaron daga hannun Taj "Hey." Ya na kallon face ɗin Ayan "me ya sa kake kuka wai ya taɓa mun kai?" Cikin kuka ayan ya ce "Uncle Tee i don’t want home i want her." Kallon shi ya yi "Wace." "Pretty Dr i want her."

Shuru ya yi ya buɗe baki kenan zai yi magana ya hango ta Naila sanye da labcoat "wow ta kare school kenan?" Ya tambayi kansa cikin zuciyarsa, ita bata ma san suna wajen ba, ta wuto ne ta na taɓa wayarta, ɗaga kanta da zata yi idanunta ya sauka a kanshi zaro ido ta yi ta na kallonshi, Ya ƙara tsawo ya ƙara jiki da ma shekaru, sannan ya ƙara kyau.

"TAUFEEQ!!" Ta ce cikin mamaki "Naila.'" Ya ce ya na murmushi ya kalleta from head to toe kamar dai yanda ya saba ya ce "U are really here?" Ta ce "Kai da ka ɓace fah aka bar jin labarin ka." "Ba ki yi replying massege ɗi na ba." "Massege ɗin da ka turo 3yrs later." Daria suka saki, sai lokacin ta lura da Ayan dake hannunshi, shi kuma Ayan so yake a saukar da shi sauke shi ya yi ai kuwa ya yo in da take,ya na kama gefen labcoat ɗinta ita wallahi ta zaci sun wuce.

Da mamaki Taufeeq yake kallon ayan ɗin saboda ya san ba kasafai yake yar sa da mutane ba, "Hey come here." Maƙe kafaɗa ya yi "Idan na zo wucewa zata yi ta bar ni." Kallon Taufeeq Naila ta yi "Ka san shi ne?" "Eh he is my niece, ɗan ɗan yaya na ne Tajudden wanda nake baki labari. " nuna in da Taj ke tsaye ta yi "Wancan?" "Eh yaya na ne." Taufeeq ya karashe mata.

Kallon Ayan ta yi ta sake kallon Taufeeq no wonder take ganin kamar shi da wani wanda ta sani ashe Taufeeq ne.

Kallon labcoat É—inta Taufeeq ya yi "Wow sai da kika zama Neurologist, My pretty psycho." Daria ta yi "Stop it mana." "Kin É—an canza fah, u smile easily yanzu." "No ba haka bane kawai dai i was happy ne, naga old friend É—ina. " Jinjina kai ya yi "Ashe kin É—auke ni as friend É—in ki." "Eh mana tuntuni." Ta ba shi amsa
Chapter 14 · 0% Book details