← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 71

Sashe 28

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta na shiga kitchen ɗin ta iske masu aiki har sun fara shirye shirye, ƙarasawa ta yi ciki, cikin girmamawa suka gaisheta amsawa ta yi a natse sannan ta kalli babban cikin su wacce take incharge na komai acikin kitchen ɗin mai suna Hauwa ta ce "Me za'a dafa yau?" Cikin girmamawa Hauwa ta ce "Hajiya babba (Mami) ta ce tuwon semo take so da miyar egusi, Hajiya ƙarama (Mom) kuma pepper soup take son ci na naman rago a haɗa mata da white rice da cabbage souce, sai Miss Taslim da kuma Mr Taufeeq yawanci abu iri ɗaya suke ci sannan za'a yi musu pepper soup na cat fish, Sai Mr Taj baya cin abinci mai nauyi da dare yawanci light food yake ci shi ana dafa masa....."

"OK naji zaku iya tafiya." Ta katse Hauwa ɗin ɗago kai Hauwa ta yi ta kalleta "Na'am. " "Ku tafi kawai yau ni zan dafa abincin." Kallon juna masu aikin suka yi sannan suka juya ɗaya bayan ɗaya suka soma fita har Hauwa ta kai ƙarshe Naila ta ce "Ke tsaya zaki ta ya ni wasu abubuwan."

Nan suka shiga shirya haɗa abincin in da Mai aikin taya ta yanka abubuwa kawai take yi ita ke haɗa komai, a natse take komai cikin tsabta, su na tsakar dafa abincin ne Taslim ta shigo "Wow wai me ake dafa mana ne ƙamshin abinci duk ya cika gida." Zaro ido ta yi ganin Naila cikin kitchen ɗin "Laa Anty Ameenatu ke ce kike dafa mana abinci, wai kin ji ƙamshi kuwa?"

Murmushi kawai Naila ta yi bata ce komai ba Taslim ta sake cewa "Wallahi am eager to eat this food na matsu." "Me ke faruwa anan?" Suka ji maganar Taj juyowa suka yi dukan su, ya na tsaye bakin ƙofa dawowar shi kenan daga office, murmushi Taslim ta yi ta na cewa "Yah Taj Anty Ameenatu ce take dafa mana dinner yau baka ji ƙamshi ba?" Jinjina kai ya yi "Eh na ji." Ya faɗa idanunsa zube kan Naila dake tsaye sanye da apron sai hannunta dake riƙe da cibin miya.

Ajiye spoon ɗin ta yi ta jawo towel ta na goge hannunta, a hankali ya shiga takowa cikin kitchen ɗin "Sannu da zuwa." Ta ce ta na kallon face ɗinsa "Yawwa ya aiki. " "Lafiya qlu." Ta ce ta na ɗan matsawa baya saboda yanda yake sake matsowa kusa da ita, ɗan yamutsa fuska ta yi "Honey mana, ka ga fah acikin kitchen nake duk na yi warin hayaƙi." "I don't care." Ya ce ya na riƙe hannunta zai rungumeta kenan suka ji muryar Haulat da ƙarfi "Yah Taj!!" Duk kallonta suka yi.

Shuru ta yi ta na so ta yi calming kanta kafin ta É—ago ta kalleshi ta ce "Mami na kira." Jinjina kai ya yi "Ok." Sai kuma ya juyo ya kalli Naila hannunta ya yi kissing sannan ya juya ya bar kitchen É—in.

Ya na ficewa ita ma ta juya ta ɗauki cibin miya ta shiga motsa miyar ta ta yi kamar bata san Haulat ɗin na cikin kitchen ɗin ba, "Hmm na ga alama bazawara ta fara ƙoƙarin zama matar gida. " Haulat ɗin ta ce cikin sigar jan magana juyowa Naila ta yi fuskar nan a haɗe kamar irin ita ma zata mayar mata da magana sai kuma ta saki murmushi "Oh wallahi na manta sis Haulat ke me zaki yi dinner da shi, koh kuma kawai ki na iya ci cikin na su Taslim ko na Mom koh kuma na Mami. "

Ta ce ta na sake faÉ—ada murmushinta, wani kallo Haulat É—in ta yi kata sai kuma ta juya ta fice ta na sakin tsaki.

Murmushin gefen baki Naila ta yi ta na juyawa ta cigaba da aikinta, don dama su Taslim sun fice tun lokacin da Taj ya shigo kitchen É—in.

Bayan ta kammala ficewa ta yi ta nufi part ɗin su, ɗakinta ta wuce direct ya shige toilet wanka ta yi tare da alwala din an fara kiran sallar magrib, bayan ta fito ta shafe jikinta da mai da kuma turaruka masu ƙamshi sannan ta saka doguwar rigarta marar nauyi tare da hijab ta kabbarta sallah.

Sai bayan isha ta fito daga ɗakinta sanye cikin wata black Kuwait abaya mai shegen kyau, ta yi rolling veil ɗin abayar, sai ƙamshi take yi, fuskarta ta babu kwalliya komai sai lip gloss da ta shafa.

Ficewa ta yi zuwa palor don lokacin dinner ya yi, ta na fitowa babban palor dining room ta nufa, nan ta sami an gama jera komai, wucewa ta yi kitchen ta É—auko drink da ta yi na fresh fruits kusan kala biyu ta ajiye, su Taj ne suka fara isowa dining room É—in shi da Ayan da kuma Taufeeq, "Dan sammin drink É—in nan." Cewar Taufeeq ya na jan kujera ya zauna.

Zuba masa drink ɗin ta yi a glass cup ta ba shi "Thanks besty." Ya ce ya na murmushi ya kai cup ɗin bakinsa, wanda bai sauke cup ɗin ba sai da ya shanye drink ɗin, "God drink ɗin nan ya yi daɗi ƙara min." Ta ɗauko jug zata ƙara masa kenan Taj ya riƙe hannunta, juyiwa ta yi ta kalleshi "Ni ma ki saka min." Ya ce ya na miƙa mata cup, kallon Taufeeq ta yi sai kuma ta juya ta na saka ma taj drink ɗn, waro ido Taufeeq ya yi "Lallai besty shi ne kika saka ma mijinki koh."

"Sorry." Ta ce ta zo zata zuba mishi ya jaye cup ɗinshi, ai kuwa taj ya sakar mishi wani harara, "What are u doing kamar ƙaramin yaro." Ya faɗa ya na amsan jug ɗin daga hannunta "Idan ba zai saka ma kanshi ba ya bari." Sakin baki Taufeeq ya yi ya na kallonshi, duk abun da ya faru akan idon Haulat da ta ķaraso wajen ya faru, "Maganar me ake yi haka?" Ta ce ta na zama wajen, "Yau Anty Ameenatu ce ta dafa mana abinci."

Taslim da ya karaso wajen ta faɗa, taɓe baki Haulat ta yi "Toh Allah ya sa abincin ya yi dadi." "Dole abinci ya yi daɗi saboda mata ta ta dafa shi." Taj ya bata amsa sannan ya kalli naila "Ki sa min abinci yunwa nake ji." Murmushi ta yi "Toh farin cikin Ameenatu." Sakin baki daga Taufeeq har taslim suka yi, Taufeeq ya ce "soyayya ruwan zuma."

Ita kuwa Haulat wani baƙin ciki ne ya turnuƙeta, serving dinsu ta shiga yi, su na haka ne su Mami da mom suka ƙaraso wajen, su ma ta yi serving ɗinsu sannan suka zauna suka shiga cin abincin sai santin abincinta ake yi, don Taufeeq plate biyu ya yi, ayan kuwa ya canye wanda aka saka mishi, don dama bai da cin abinci, haka ma taj tass ya canye abincin plate ɗinta.

Bayan an ƙare dinner ɗinne kowa ya watse.

10:12pm

Zaune take kan sofa sanye da kayan bacci riga da wando sai small hijab ɗin da ta saka a sama laptop ɗin na kan kan cinyar ta ta na operating Taj ne kuma ya na zaune kan gado sai dai shi wayar shi yake taɓawa, ɗagowa ya yi ya kalleta ya ce "Ban za ci kin iya dafa abinci ba." "Me ya sa?" Ta ce ba tare da ta ɗago ba "Saboda you don’t look like wacce ta iya girki." "Ai ban san ana iya gane mutun ya iya girki from his appearance ba."

Ɗan murmushi ya yi ya na girgiza kai bai sake cewa komai ba ita ma haka, kusan 5mnt ta ɗago tare da cewa "Mr Tajudden zo ka ga wani abu." A hankali ya sauko ya ƙaraso in da take ya tsaya bayanta, da yake da jingina ga hannun kujerar ne ta miƙar da ƙafafunta kan kujerar, ɗan ɗuƙowa ya yi har ta na jin numfashinsa gafen fuskarta, bata mai da hankali ba sai bayani da take yi masa na abun da ta gani ɗin.

Shi kuma tun da ya sauke idanunsa kan lapatop É—in nan da na idanun nasa suka yi ja saboda bacin rai, ita bata ma sani ba sai baya ni take yi ma, ganin ya yi shuru bai amsa ba ta juyo ta kallesa sai da ta tsorata, É—an ja baya ta yi saboda fuskar su da take kusa "Mr Tajudden. " Ta kira sunansa ganin yanda ya kafe screen É—in da ido.

Bai amsa ba sai kallon screen É—in da ya cigaba da yi "Mr Tajudden. " Ta sake kiran sunan shi, nan ma shuru, a hankali ta É—aga hannunta ta shafa gefen fuskarsa tare da cewa "Mr Tajudden." ÆŠan numfashi ya sauke ya na mai da idanunsa kanta "Me ya sa kika yi haka?" Ya tambayeta "Bincike na yi." "Eh i know bincike kika yi, but me yasa kika yi? Kin kuwa san hatsarin da ke cikin haka? kin kuwa san me kika saka kan ki? Me ya sa kika bincika tun farko?"

Kallon shi kawai take yi one thing about him is baya É—aga murya duk fushin da yake ciki tun ba yau ba ta lura da haka, shi É—in ba mai É—aga murya bane sai idan ta kama, a hankali ta ce "Ka na damuwa ne aka na binciko wannan sirrin?" Rumtse idonsa ya yi "Of course no am worried about ur safety Ameenatu, coz they wont seat back idan har suka san kin san da wannan abun, Ameenatu I cant afford to loose u too."

Ya ƙarashe maganar ya na miƙewa tsaye, ita kuma shuru ta yi ta na kallonsa coz she was shocked da magana da ya faɗa ta karshe, kallon da take yi masa ne ya saka shi gane abun da ya yi, lumshe ido ya yi ya na kauda kanshi "I mean in rasa ki matsayin ki na musulma ƴar uwata." Daria ta fashe da shi sai kawai ya tsaya ya na kallonta coz bai taɓa ganin ta yi daria irin haka ba.
Chapter 28 · 0% Book details