← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 71

Sashe 1

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[21/09, 11:43] Amina Khaleel: https://www.arewapen.com/chapter?id=6a765bf456862e967f66aee6

Mrs Tajuddeen Abad

By Meemziey

page 1️⃣

Bismillahi rahmanir raheem

Wannan labarin is a work of fiction babu abun da yake ciki that is real, idan labarin ya yi dai dai da rayuwar wani arashi aka samu

1999

Dare ya tsala sosai, da yake ana tsakiyar damuna ne, wanda ba'a daɗe da ɗauke ruwan sama ba, a wannan lokacin da ya kamata ace ko wani bawa ya na hutu ma'ana bacci, a wannan lokacin ita ma take kwance saman gadon asibiti wanda bata daɗe da haihuwa ba, don kuwa ana tsakar goge jaririn da aka haifo ne, bayan an gama goge su, midwife ɗin wacce kwata kwata bata yi kama da ƴar Nigeria ba don tafi kama da arab, ta ɗauko jaririn ta fito waje da su, da sauri wata mata ta ƙaraso in da Midwife ɗin take ta amshi jaririn, kallonsu take yi hawaye na sauka kan kuncinta, ɗagowa ta yi a hankali cikin yaren larabci ta ce "Ina mahaiyar jaririn? Lafiya take?"

"Ta na lafiya ta samu bacci ne." Jinjina kai matar ta yi ta na sake kallon jaririn, sai kuma ta kalli nurse É—in kafin ta juya ta yi hanyar fita daga ward É—in rungume da jaririn, ficewa ta yi daga asibitin gabaÉ—aya ta na tafiya cikin sauri sauri ta na kuka sosai, sanyin damuna ya na ratsata, ta san abun da take yi ba mai kyau bane, ta san abun da zata yi bata kyauta ba, toh amma yah zata yi? Hakan da take yi shi ne the only option É—insu, tafiyar fiye da minti talatin ta yi sannan ta kawo wajen wata anguwa da babu hayaniya infact babu gidajen mutane da yawa a wajen.

A hankali ta karasa wajen wasu kujerun shan iska ta zauna ta na ajiye jaririn awajen, shuru ta yi ta na kallon jaririn kafin ta yi masa addu'a ta shafa masa sannan ta miƙe a hankali har ta juya zata bar wajen kawai ta fashe da kuka ta dawo ta ɗauki jaririn ta na furta "Aa, A'a, Allah na tuba ka yafe min astagfirullah, Allah na tuba, ba zan iya barin yaron nan ba kuma." Shi ne abun da take cewa ta na sake rungume jaririn, sai kuma ta sake cewa "Koh babu komai atleast ɗayan ku ya tsaya a garin da mahaifin ku yake." Ta ce ta na tafiya a hankali, haka ta na kuka ta koma asibitin ko da ta tafi mahaifiyar yaron bata koh farka ba, sai ta fara tunani da ace ta bar yaron can me zata faɗa ma mahaifiyar sa idan ta farka.

Allah ya gani ba da niyar cuta ta yi hakan ba, allah ya ga zuciyarta,

Washegari ko da mahaifiyar jaririn ta farka, ta na juyowa suka haɗa idanu da wannan matar, a hankali ta furta "Hauwa, ina jaririn yake? me na haifa?" Ta ce idanunta na tara ruwa, ita ma hawaye Hauwa ɗin ke yi saboda da ace ta bar wannan yaron a wajen nan jiya bata san me zata faɗa ma Umaima ba, cikin kuka ta ce "Mace kika samu Umaima, mace kika samu." Sai ta miƙe ta nufi in da jaririn yake kwance ta ɗauko sa ta ɗora mata kan jikinta, wani irin sanyi Umaima ta ji lokacin da aka ɗora mata wannan jaririn, ta na jin zafi da kuma farinciki at the same time, zafin da take ji na bata san da wani ido za'a kallesu ita da ƴarta ba, bata san wace kalar rayuwa za su yi ba ita da ƴarta, sanyi take ji aranta da Allah ya bata ƴar, rungume ƴar ta yi tsam ajikinta wani irin so da kuma ƙaunar ƴar na cikata, sannan ta shiga yi ma ƴar tata addu'a, addu'o'i kala kala don kuwa bata son ƴarta ta yi irin rayuwar da ta yi.

*********

Early 2000

Ta kai kusan minti goma sha biyar a tsaye a bakin ƙofar gidan tun ɗazu take wajen a tsaye riƙe da roba ta kasa shiga, kallo ɗaya zaka yi mata kasan da cewa tsoro ne ya cika ta a wajen, don jikinta wata irin muguwar rawa yake yi, hannunta riƙe da robar niƙa, yarinya ce da ba zata wuce shekara 7 ba, ta na sanye da wani kuɗaɗɗen hijab da doguwar rigar atamfa da bata ida kai mata har ƙasa ba ita ma a koɗe take.

Tun dazu sai leƙen cikin gidan take yi sai dai ta kasa shiga, fuskarta ta yi wata irin jar tashin hankali Kasancewar ta fara, haka idanunta da ƙwayar su ta kasance blue sun wani canza launi zuwa ja, daga sama out of no where ta ji an riƙe ta, cikin kiɗima ta yarda robar hannunta ai kuwa duk niƙan dake ciki ya zube, ta na ɗagowa suka haɗa ido da Kawunta, wani irin yawu ta haɗiye ta na ɗauke kallo daga garesa zuwa niƙan da ta zubar hawaye na taruwa a idonta.

"Kutmar buro'uba ke ƴar banza me kike yi anan? niƙan da aka aike ki kika zubar don baki da mutunci. " Ya ce cikin hargowa kafin ya yi sama da ita zuwa cikin gida, a tsakiyar gida ya yi wurgi da ita, ai kuwa ta mulmula har bakinta na bugewa da turmin dake ajiye a wajen, take jini ya ɓalle daga bakin ta.

Cikin wani irin tashin hankali ta miƙe tsaye ta na share bakinta, kuka na ƙwace mata ganin jini "Wayyo Allah kawu ka yi hakuri, innalillahi wa'inna illahi raji'un, kawu don Allah ka yi hakuri." Ta ce ta na yarfe hannunta, matar kawunta ce ta fito daga ɗaki wacce suke ce ma Inna Hafsatu, ganin Kawun da kuma ita tsaye ta ce "Ah ah ya dai me ta yi kum....." maganarta ce ta laƙe sakamakon ƴar ta Faiza da ta shigo riƙe da emty robar niƙa.

"Ƙutt niƙan da na aike ki ne kika zubar dan ubanki da ba'a san waye shi ba." Ta ce ta na karasowa in da yarinyar take tsaye, wani kalan ƙamewa yarinyar ta yi cikin tsoro ta riga da ta sadaƙar don ta san yau taron dangi za'a yi mata, Allah ne kaɗai zai ceceta.

Ai kuwa Inna Hafsatu babu ɓata lokaci ta same ta ta kama jibga kamar ta samu kayan wanki, shi Kawu wucewa ya yi cikin ɗaki don Hafsatu kaɗai ta ishe ta, lilis ta yi mata har bata iya tashi sannan ta ce "Ki tashi ga wanke wanke nan ki yi, kuma billahillazi idan kayan nan basu wanku ba sai na darje ki a gidan nan, shegiya mai idanu kamar mayun turawa." Daga haka ta yi wucewarta cikin ɗaki.

Da ƙyar ta iya tashi ta wuce in da kayan wanke wanke suke ta shiga haɗa kwanoni, jikinta duk ciwo yake mata idanunta sun kumbura sun yi ja face ɗinta ma haka, idan ka ganta sai ta baka tausayi.

Ga wanke wanken mai uban yawa haka ta tara wanke wanken nan ta wanke tass, ko da ta ƙare an kira magrib alwala ta yi wa wuce ciki, ɗakinsu ta nufa ta karasa can gefen ɗakin in da ƴar Ghana most go ɗinta take ta ciro wasu kaya ta canza da yake, kayan jikinta sun jiƙe sakamakon wanke wanken da ta yi.

Bayan ta canza kaya ne ta ajiye waÆ´an nan a gefe ta shimfiÉ—a sallaya ta yi sallah duk da wa wani iyawa ta yi ba amma a haka take yin abun ta, ai tafi ba'a yi ba gabaÉ—aya.

Bayan ta kare sallah ne ta fita da kayanta da ta cire ta É—auraye su babu sabulu bale omo ta shanya su haka nan, don gidan haka suke treating É—inta kamar wata karya marar galihu, daga kawunta yayan mahaifiyarta zuwa, matar kawunta Inna Hafsatu.

Bayan Isha.

Zaune suke a palor su na kallo su na cin abinci, Kawunta, Inna Hafsatu da ƴaƴan su guda uku, Hafiz shine na farko mai shekara goma sai Fa'iza mai bakwai, wanda ita ce sa'ar ta, sai kuma autan su da ko yaye shi ba'a yi ba, su na ce mishi Jabeer, ita ta na daga can gefe rakuɓe, don ƙa'ida ne sai sun gama cin abinci sun rage sannan zata ci abinci, kuma wanda suka rage ne za ta ci.

Haka kuwa aka yi don su na ƙarewa Inna ta haɗo mata wanda suka rage ta miƙo mata haka ta zauna ta na cin abincin cikin sauri saboda wata irin mahaukaciyar yunwa take ji.

Da dare kuwa da aka zo kwanciya a kwai babbar katifa a dakin su amma ta yi kaÉ—an ta kwana anan don ta na fitsarin kwance, wata yamutsatsar katifa ta dauko ta ajiye gefen É—akin ta É—auko wasu raggogi wai zannuwa ta shimfiÉ—a, sannan ta hau abunta ta kwanta, koh zanin rufa bata da haka nan take kwana komai sanyi kuwa.

Wani irin sanyin asuba ne ke ratsata har cikin ƙashin ta take jin shi wanda ya haɗe da sanyi fitsarin kwancen da ta yi, ta na kwance a wajen ta na wani irin kyarma daga sama ta ji an watsa mata wasu irin ruwa masu mahaukacin sanyi.

"Tashi maza shegiya ƴar iska, yau ma fitsarin kika yi?" A firgice ta miƙe jikinta ya na rawar sanyi da ma tsoro, bata ida dawowa daga duniyar ruwan sanyin da aka watsa mata ba, ta ji saukan wani lafiyayyen mari a kumatunta, sai da walƙiya ta gitta a idanunta, wani kalan dafe kumatunta ta yi, ta na fasa wani kuka a gigice ta fice daga ɗakin sai tsakar gida, biyo ta Inna ta yi ai kuwa ta iske ta tsakiyar gida sai shawagi take yi akan gigicewa da marin da aka yi mata.

Jinjina kai Inna ta yi ta ja ƙofarta ta rufe ta barta anan tsakiya gidan sanyi na dukan ta, duƙawa ta yi awajen ta na haɗe jikinta don dama an saba yi mata haka da ta yi fitsari da ka da ta yi fitsarin duk asuba sai an watsa mata ruwan sanyi an barta a tsakiyar gida sanyi ya kwashi rabonsa.
Chapter 1 · 0% Book details