← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 71

Sashe 12

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠan kallon shi ta yi, ga yaro mai kyau fari da shi, maganar nurse din ne ya katse mata tunani "Dr ki na ganin yaron nan zai kai labari?" Jinjina kai ta yi "Zai kai insha Allah. "

Daga haka ta fice zuwa office, bata jin zata iya zuwa gida saboda har an kusa yin asuba, zama ta yi saman kujera ta na ɗora kanta saman table ta gaji sosai bacci take ji ba kaɗan ba, surgery huɗu ta yi yau, gashi washegari ma ta na da surgery ɗin, sai da aka kira asuba ta miƙe ta shiga toilet ta yi alwala ta yi sallah, sannan ta saka labcoat saman scrub ɗinta ta fice, shi ne patient na farko da ta duba, koh da taje ta iske ƴan gidan su kan sallaya a corridor na ICU ɗin saman sallayah sun sallame sallah.

Gaida su ta yi sannan ta shiga ta duba shi ta fito, sannan ta wuce kan sauran patient É—inta, around 8:30am kuma ta shiga wani surgery yau ma uku ta yi wanda duk ta gaji she is exhausted ga yanda kanta ke yi mata ciwo.

Around 5 na yamma ta fito zata wuce sai kuma ta dakata tunawa da patient ɗinta, juyawa ta yi ta nufi hanyar ICU ɗin, ta ajiye jakarta ta shiga ciki, ta na tsaye ta na monitoring ɗinta kamar ƙyeptawar idanu hannun sa ya motsa , sannan idanunwan sa suka buɗe rufe su ya yi haske ya yi masa yawa, sannan ya sake buɗe su, yawo da idanunshi ya shiga yi ba su faɗa cikin na kowa ba sai nata, ɗan yamutsa fuska ya yi don bai ma santa ba.

a hankali Mom da tashigo tare da ita ta ce "Son ka farka?" Bai yi responding ba kamar ma bai ji ba, Naila ne ta ce "Alhamdulillah he is conscious now, sai dai mu jira ya sake dawowa daidai." Ɗan motsi hannunshi ya yi, ya dunƙule hannun sai kuma ya buɗe ya na kama bed sheet cikin rashin ƙarfi, nurse dake wajen ta ce "Dr Ameenatu muryan ki fah yake bi."

Kallon shi kawai ta yi sai kuma ta juya ta kalli nurse din "He is orienting, minimal stimulation, let him come back at his own pace." Ɗan ƙyepta idanu ya yi sai kuma idanun nasa suka rufe, bakinsa ya buɗe kamar ya na son yin magana ɗan duƙawa Naila ta yi saitin da yake ta ce "Its ok, ba sai ka yi magana ba."

Daga haka bacci ya dauke shi, miƙewa ta yi ta juyo ta kalli Mom ɗin "Ya farka and shine abun da muka fi buƙata, a san zai farka ɗin." Daga haka ta fice bayan ta ɗauki jakarta,0 direct ficewa ta yi daga asibitin zuwa parking lot ta shiga motar ta ta fice.

Daga can cikin asibitin kuwa, Mom ce ta kalli É—ayar matar wacce suke ce ma Mami, ta ce "Yaya ki na ganin lafiya qlu ne, ki na ganin ba za'a samu matsala ba, kin san TAJUDDEEN ko kaÉ—an baya son asibitocin Nigeria indai akan lafiyar Ayan ne, ki duba ki gani koh magani baya so a bashi anan balle a kai ga an yi masa aiki, Ayan ya faÉ—i bai sani ba, sannan ba da sanin shi ba aka yi ma ayan aiki, ki na ganin haka ba zai fusata shi ba kuwa?"

Numfashi Mami ta sauke "Ni ma ban sani ba Zainab, ban san yanda zai yi reacting ba, amma ko ma dai mene ne, abun da ake so shi ne Ayan ya ji sauƙi Ayan ya samu lafiya." Ta ce a hankali, a hankali Taslim ta ce "Kuma Mami tun jiya nake kiran Yah Taj wayarsa bata shiga, and it's not like him." Duk shuru suka yi cikin jimami.

Bayan kwana biyu, condition É—in yaron ya yi improving sosai, ba kaÉ—an ba, ya kan É—an farka ya buÉ—e idanunshi especially in ta na nan saboda ya na responding to voice É—inta ko don maganarta ya fara jinbayan ya yi regaining consciousness oho, amma mostly in ta na nan ya fi farkawa, sometimes ta kan yi mishi magana don ta ga yanda zai yi responding, ta kan É—an bashi short labari da dai sauran su.

Ta lura iyayen yaron masu kuÉ—i ne irin sosai coz ta na lure da yanda sauran abokan aikinta suke wani nan nan da su don hadda MD na asibitin sai da ta zo ya ga yaron hadda cewa pls ta kula da shi sosai, ita dai babu ruwanta, she treat all her patients equal, patients É—inta É—aya suke awajen ta, babu ruwanta idan ka na da kuÉ—i mene ne menene, she treats them equal.

7:45pm

A hankali yake saukowa daga matattakalar jirgin, hannunsa mai sanye da _Patek phlippe watch_ ya saka ya gyara baƙar _Balenciaga _face cap ɗin dake kanshi wacce ta rufe masa idanu rabin face ɗinsa kawai ake gani, sanye yake cikin soft _Beige Cashemere_ hoodie Daga _Loro piana_ wacce bata da logon komai, amma sai tsada, ya saki hular hoodie ɗin abayanshi.

Ya na sanye da wando dark tailored joggers na _Zegna_ Charcoal grey color, kafanshi sanye da sneakers na_ Cammon project Achilles low_ crisp white, ya na rataya da _Bottega veneta_ leather backpack deep expresso brown, sai ƙamshin turaren tomford yake yi mai suna Oud wood.

Saukowa ya cigaba da yi ya na tafiya, akai akai yake duba agogonshi har ya fice daga Airport ɗin, ya na fita wani security ya ƙaraso in da yake "barka da zuwa Mr TAJUDDEEN." Ya ce cikin girmamawa, jinjina kashi kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, security ɗin na batun amsan backpack ɗinsa ya dakatar da shi, matsawa baya ya yi sannan ya ce "This way sir." Sannan security ɗin ya yi gaba, baya ya bishi har zuwa wajen wata mota, ɗan dakatawa ya yi ya kalli security ɗin.

Da sauri security ɗin ya ce "Sorry sir wannan ce kawai muka samu that doesn't look expensive. " Bai ce komai ba sai miƙa hannunshi da ya yi, da sauri security din ya bashi maƙullin motar, buɗewa ya yi ya shiga tare da ajiye jakar sa a seat ɗin mai zaman banza, rufe mishi kofar security din ya yi, take ya yi ma motar key ya juya ya bar Airport ɗin da gudu.

Naila
Driving take yi da ɗan sauri saboda ta na gida aka kirata aka ce patient ɗinta ya farfaɗo she was so happy na jin haka, ta so ta bari sai gobe amma ta kasa saboda patient ɗin ya ba da wani gurbi acikin zuciyarta, tun da take bata taɓa treating case irin nashi ba, duk da ta san condition ɗin acikin littafi sai dai bata taɓa ganin shi a zahiri ba, haka na faruwa akwai cututtukan da a zaman mutun na likita koh nurse ko kuma health care provider, ba za ka taɓa ganin su ba koh kuma sau ɗaya za ka ga case ɗin a zahiri.

Wani ma har ya ƙare years na service ɗinsa ba zai taɓa ganinsu ba, so hakan ne ya faru da ita don kuwa condition ɗin sa is rare, duk da ta na nuna kamar bata damu da patient ɗin nata ba but ta damu, don kuwa duk lokacin da ta yi sallah addu'a ɗaya take yi masa Allah ya sa yaron ya samu lafiya Allah ya sa ya rayu, saboda me? Saboda shi ne wanda ta fara experiencing wannan condition a gare shi.

Ta na tsakar driving kawai kanta ya yi wani irin sparking kamar irin an haɗa wata waya da wata wacce bata dace ba toh haka ta ji sparking ɗin acikin ƙwaƙwalwar da ya saka da mistakenly ƙafarta ta taka burki ai kuwa motar ta tsaya cak motar dake bayanta ta daketa.

Kamar almara kuma sparking ɗin ya daina kamar irin a kashe abun, dama ta kanyi irin haka don ta na fama da wani irin masifaffen ciwon kai, wanda a shekarun baya ya sameta, bata taɓa mantawa ranar ta na zaune ta na karatu, Allah ya so a palorn ƙasa take, kawai ta ji kanta ya wani irin sara mata kafin ta ji wani irin sharp pain ya ziyarce ta a kanta, wani irin ciwo yake ji kanta na yi kamar zai fashe, haka take ji kamar an saka driller ana drilling ƙashin kanta, ana fasa ƙashin kanta ba tare da an yi mata anesthesia ba.

Wani irin ciwo da raɗaɗi da tun da take bata taɓa jin shi ba, wata irin azaba da har yanzu koh kwatan shi bata taɓa ji ba, har yanzu kuwa, akan baza ta iya ɗaukar azabar ba suma ta yi wanda kwananta biyu a asibiti bata san in da kanta yake ba, toh tun daga ranar take jin ciwon kai da sparking a brain ɗinta, an yi test an yi scanning ko wane iri amma babu abun da ya nuna, kanta brain ɗinta lafiya ƙalau yake.

Kuma haka take jin ciwon idan ya taso kamar an kunna shi sannan lokaci ɗaya zata bar jin ciwon kamar irin an kashe shi, sannan wani lokaci ta na zaune za ta ga hawaye sun fito daga idanunta kuka fah, koh kuma ta kama jin kanta emotional, zuciyarta ta yi ta yi mata ciwo kamar akwai ɓangarenta ɗaya da yake cikin wani hali abu dai kamar mai aljannu.

Da sauri ta fito daga motar ta na so ta bama wanda suka yi karo da shi hakuri, dai dai shi ma ya fito daga ta shi motar "Ka yi hakuri don Allah. " Ta ce cikin murya mai sanyi , kawai ya na ƙarasowa wajen cikin zafi ya ce "What the hell is wrong with u? do u know how dangerous that was?"

Ɗan ƙyepta idanunta ta yi jin ya na mata faɗa ita ma ta ce "Ba fa laifi na ba ne taka burki na yi, ai naga kai ke bi na baya a laƙe koh?" "Excuse me." Ya ce ya na wani irn kallonta "Kin wani tsaya a tsakiyar hanya yanzu kuma laifi na ne?"
Chapter 12 · 0% Book details