← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 71

Sashe 53

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ƙarashe maganar shuru naila ta yi ta ma kasa magana ga yanda Taj ya tsareta da idanu, da alama ya yi sensing akwai matsala, jin Naila ta yi shuru ya saka Nanee ja numfashi ta ce "Wallahi ki yar da da ni ba haɗin baki bane, wallahi insha Allahu Sadeek ne ya ɗauki Ayan, bana da shaida but zan turo miki abun da zai saka ki yarda dani, ki shiga WhatsApp ɗinki." Daga haka ta katse wayar, da sauri naila ta shiga what's app ɗinta dai dai, message ɗin Nanee na pictures da videos na shigowa.

Su da kansu suka buÉ—e da kansu hannunta na rawa ta danna videos É—in, video ne na secret room É—in sadeek wanda ya cika da hotunan Naila Taj Ayan da ma Æ´an gidan su Taj É—in gabaÉ—aya, sake É—aukar rawa jikinta ya yi hankalin ta na tashi sosai saboda yanda take ganin hotunan ta da ita karan kanta bata san an É—auketa su, ita bata ma san yaya ko kuma wani lokaci aka É—auki hotunan ba.

Taj dake kallon ta ganin reaction dinta ya saka ya amshi wayar shi ma dai abun ya tayar masa da hankali duk da kuwa ya san da hotunan Naila da sadeek ɗin ke ajiyewa, but bai taɓa zaton obsession ɗin sadeek ɗin akan naila ko kuma akan family ɗinsa ya kai har haka ba, da har zai ajiye ɗaki ɗaya kawai ya manna hotunan su, ya na ganin sadeek na da wani kalan mental illness.

Ya na tsakar tunanin ne Nanee ta sake kira wannan karon handsfree aka saka, ana ɗauka ta ce "Yanzu kin yarda da ni koh? Idan baki yar da ba ki ma iya cema taj ya yi tracking number ɗinsa, za'a san in da yake." Buɗe baki naila ta yi ta ce  "Hass....." saurin katseta Nanee ta yi "Ka da ki ce komai har sai kin yi confirming abun da na faɗa miki." Daga haka ta katse wayar.

Kallon taj naila ta yi wanda shi ma kallonta yake yi, kwankwato ne cike aransa ya na hana kansa but zuciyarsa na ingiza shi, dole fasa cin abincin suka yi aka saka numbers É—in sadeek É—in duka aka shiga tracking ai kuwa ga shi nan maganar Nanee ta tabbata don kuwa akwai in da yake zuwa a cikin Abuja wanda yake very suspicious don kuwa wajen garin Abuja ne, a take taj É—in ya shiga kiran wayoyi da sauran su, in da yake ba da umarni aka soma binciken wajen bayan an tura location É—in.

Daga nan kuma aka datsi wayoyin sadeek ɗin duka aka shiga bincike, har wani juwa Taj yake saboda ɓacin ran abun da yake yi ta tonowa, da wayoyin sa sadeek ɗin ya yi da komai ya na ciki, da wasu abubuwan da sadeek ɗin ya yi masa wani kalan ɓacin rai ne da tashin hankali suka taso ma Taufeeq da Taj lokaci ɗaya.

Anan palorn suka kwana hadda naila wacce ta koma gefe ta na kallon su su na aiki ita fatan ta ɗaya la da wani abu ya samu ayan ɗin ka da sadeek ya yi ma Ayan ɗin wani abu, ita ma ɗin ranta a ɓace yake yi ta na jin akwai sirrukan da ta ajiye da ba zata taɓa iya rufe su ba tun da abun ya kai haka dole sai ta tona su, har aka yi sallar asuba su na nan suka je suka yi salla suka dawo suka cigaba daga in da suka tsaya.

Around 7:30am aka bugo ma su Taj ɗin akan an gano in da Ayan yake, da sauri ya miƙe ya zari key zasu fice naila ta taso itama ta na biyo su juyowa taj ya yi zai yi magana Naila ta yi saurin cewa "Don allah don allah taj kuje dani don girman allah, I know its dangerous but pls." Ta faɗa ta na haɗe hannayenta, gyaɗa kai ya yi ya na wucewa gaba da sauri ta bi bayan shi, mota ɗaya suka shiga ita da shi sauran kuma mota ɗaya daga nan suka dauki hanya.

Sun yi kisan tafiyar 40mnt kafin su isa wajen wata anguwace da babu gidaje sosai duk rabin ta, daji ne, ko da suke isa wajen ga jami'an tsaro na both sojoji da ƴan sanda, Ayan da aka fito da shi ya na ganin su da sauri ya sauko daga in da yake zaune duk ya rame ya yi baƙi idanunshi sun faɗa sosai,  da sauri ya ƙaraso in da suke kawai ya wuce mahaifin ya ƙaraso in da naila take tsaye ya rungume ta ita bata taɓa expecting haka ba haka ma su Taj ɗin rungumeshi ta yi ita ma tsam ta na ƙanƙame shi ajikinta nan da nan idanunta suka tara ruwa don Ayan ɗin na rumgumeta kuka ya saki sosai mai taɓa zuciya.

Kawai ita ma ta saki wani irin kuka ta na sake rungume shi don ta san kidnapping ɗinsa da aka yi trauma ɗin zai zauna a memory ɗinsa har ya ƙare rayuwar sa especially in an yi maltreating ɗinsa, kuka take yi sosai ta na rumgume da shi, a hankali taj ya ƙaraso wajen ya na haɗe su gabaɗaya da ita da ayan ya rungume su ya na ɗan bubbuga bayanta coz duk abun da zai saka naila kuka ba ƙaramin abu bane.

Sun É—an daÉ—e a haka kafin ya raba hug É—in ya na da umarni akai su gida tare da securities da komai gudun wani matsalar, shi zai zauna anan saboda case É—in babba ne sannan an samu nasarar kama duk waÆ´an da aka gani anan wajen, wato waÆ´an dake tare da ayan É—in, waÆ´an da sadeek ya bama aikin.

Ko da su naila suka isa gida su Mami da mom na nan na jira sai Mami ta baka tausayi saboda ita ma hadda kukanta, Naila da kanta ta yi ma Ayan wanka ta canza masa kaya sannan aka bashi abinci yanda yaron ke cin abinci bama gaskiya ba coz hannu baka hannu akushi yake yi, wani irin tausayi da ɓacin rai ne ya taso ma naila take saboda yanda ayan ɗin ke cin abinci da alama starving ɗinsa suka yi, and yanda ayan ma baya wani son cin abinci sosai sometimes sai dai ya yi wasa da abincin ko kuma ka ga ya ci kaɗan ya rage but yau yanda yake cin abincin a yunwa ce sai ya baka mamaki ya na gama cin abincin ya sha ruwa take wani amai ya taso masa aikuwa ya shiga kwarara shi anan wajen.

Bayan ya ƙare ta gyara masa jikin sa tare da wajen wanda zuwa wannan lokacin zazzaɓi mai ƙarfi ya kama shi, sai da ta haɗa wasu allurai ta basa wanda ta na gama bashi ya yi bacci ya na kwance kan cinyarta ya wani rirriƙeta ya laƙe mata kamar za'a ƙwace masa ita, and tun da ya dawo ya na biye da ita sai sake shige mata yake yi.

A haka Taj ya dawo ya iske su wanda ita ma baccin take yi wanda bata yi ba jiya, ya dade ya na kallonsu kafin ya fice ya wuce part É—in sa ya yi wanka ya canza kaya coz abubuwa sun yi masa yawa bai ma san ta in da zai fara ba, coz abubuwan da ya gani dake cikin wayar sadeek É—in sake ta da hankalin shi yake yi.

Bayan ya shirya kwantawa ya yi saboda ya yi kwanaki bai yi bacci ba kansho ciwo yake yi from all the stress da ya kwasa a kwanan, baccin awa biyu ya yi ya farka saboda kiran la'asar da aka yi wanka ya sake yi ya shirya ya fice, sai da ya fara zuwa part ɗin Mami wajen su Ayan wanda har yanzu bacci yake yi shi da naila ɗin wacce take rungume da shi tsam, ta da naila din ya yi wanda hakan shi ne sanadiyar ta shin Ayan ɗin wanda zazzaɓin shi ya sauka sosai sa sosai, bayan ya ta da su ya fice zuwa masallaci, ita kuma naila din wanka tasake yi ma ayan ita ma ta yi wanka sannan suka yi sallah tare.

Daga nan suka fita zuwa neman abincin da zasu ci, sai wani lallaƙe mata ayan ɗin ke yi sannan yanzu abu kaɗan ke saka shi zabura, ya na buƙatar therapy ƙwarai da gaske.

Da dare tare duk aka ci dinner hadda Taslim da ta dawo daga wajen buki ranar wacce ita bata ma san da batan ayan ɗin ba tun da bata nan babu wanda ya faɗa mata sai bayan ta dawo ne ta san da ɓatan na sa.

Naila part É—in Mami ta koma ita da Ayan saboda har yanzu ta na part É—in Mami, Mami bata ce ta koma part din Tajuddeen ba, ita kuma ba zata iya komawa ba saboda kunya, and haka kawai sai ta tashi ta koma part É—in Taj bayan Mami ce ta ceceta daga taj É—in.

Around 11:30pm ta na zaune ayan na kan cinyarta ya yi bacci ta na shafa kanshi daga ita har shi suna sanye da kayan bacci marar nauyi kala É—aya idan ka gansu kamar É—a da uwa, danne danne take yi a waya kawai kira ya shigo wayarta, Sadeek shi ne sunan dake yawo akan screen É—in wayar, wani kalan faÉ—uwa gabanta ya yi tare da wani fargaba ta ma kasa É—aukar wayar har sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta É—auka.

Ta kara a kunnenta without saying anything for some seconds sannan Sadeek ɗin ya ce "Hmm u don't want me to hear ur voice kenan." Shuru ta yi bata amsa ba ya yi wani irin murmushi mai sauti ya ce "Na san ba zaki yi magana ba, Ameenatu, Hmm ki na ganin komai ya zo ƙarshe ne?" Har yanzu bata amsa shi ba sai sauraren shi da take yi, wanda recording ne take yi coz ta riga da ta saka recording.
Chapter 53 · 0% Book details