← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 71

Sashe 32

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce ta na ƙarasowa in da Haulat ɗin take "Na zaci yaranci ne ke damun ki, ashe harda daƙiƙanci da rashin hankali." Wani irin juyowa Haulat ta yi ta ɗaga hannu zata mari Naila ɗin amma koh ƙyeptawa Naila bata yi ba, sai kallon Haulat ɗin take yi ta ma kasa magana, kafin ta ce "Kam bala'i, da baza ki sake marin wani ba kuwa har duniya ta naɗe."

Sauke hannunta Haulat ta yi cikin rashin kunya ta ce "Wajen Yah Taj zan je." "Na sani na san wajen shi zaki je, but baki da hurumi shiga ɗakin nan da sunan kin tafi neman sa coz ɗakin auren mu ne." "Ai ni ma auren shi zan yi." Daria Naila ta kwashe da shi "Au haba? Da gaske? Ai ni ban sani ba." "Soon zaki sani." Riƙe ƙugu Naila ta yi mockingly ta ce "Toh ki bari idan ya aure ki ya gina miki naki part ɗin, sai ki yi duk abin da zaki yi, amma ayanzu wannan part ɗina ne, kuma ni nan ni ce ke amsa sunan Mrs Tajuddeen Abad, Mrs Tajuddeen Abadddd." Ta kira sunan sau biyu tare da jan sunan sannan ta kwashe da daria kafin ta dake cewa "Seriously har na ji kunya, wallahi na ji kunya, na sani u want to marry him but ki na tsoron ka da a kashe ki koh, oh ashe ba son shi kike yi ba, amma ni da kika ga ina son shi na aure shi, kuma zan haifa masa ɗiya ƴan dugwi dugwi masu kyau iri na."

Ta ce ta na rolling idanunta haɗi da taɓe baki, sai kuma ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe ta tsaya abakin ƙofa ta ce "Babu ke babu shiga ɗakin nannnn." Ta ƙarashe ta na yi mata gwalo sannan ta rufe ƙofar ɗakin, kam bala'i haushi kamar ya kashe Haulat, ta juya afusace ta fice, Naila kuma na shiga suka haɗa idanu da Taj da ya fito toilet, ɗauke idanunta ta yi ta na rolling ɗinsu ta wuce ta hau kan gado ta zauna ba tare da ta ce ƙala ba.

Shi ma wucewa ya yi ya fita daga É—akin ba tare da ya ce da ita komai ba.

Bayan kwana biyu...

Tsaye take cikin kitchen riƙe da cibin miya, paten dankali take coz haka kawai yau ta ta tashi ta na marmarin shi, rufe tukunyar ta yi bayan ta gama motsawa ta ajiye cibin miya ɗin cikin bowl dake gefe, sannan ta rage wuta, ta fito daga kitchen ɗin ɗaki ta koma, about 7mnt ta dawo kitchen ɗin, gaban gas ta tsaya har ta kai hannunta zata ɗauko cibin miya ɗin sai ta dakata, sai kuma ta ɗauki spoon ɗin ta buɗe tukunyar ta motsa abincin, sai kuma ta kashe gas, plate ta ɗauko ta ɗebi abincin, sannan ta ɗauki ruwa a fridge da spoon ta shige ɗaki.

15mnt later
Kwance take tsakiyar ɗakinta ta na kokawa da numfashinta wanda yake barazanar ɗaukewa, jikinta ya yi wani irjn jaa sosai bakinta ya yi blue ya na fitar da kumfa, ga plate da ta saka pate aciki nan watse a gefenta, numfashi take fitarwa da ƙyar ta na so ta ɗauko wayarta amma ta kasa saboda jikinta ya ya soma mutuwa, da ƙyar ta na jan jiki ta ƙarasa in da wayarta take, ta na fitar da numfashi da ƙyar, hannunta na rawa ta buɗe wayar, wayar ma kamar zata faɗi daga hannunata, da ƙyar ta lalabo number Taj ta buga masa kira hawaye ba sauka kan kuncinta saboda azaba da take ji ajikinta.

Sai addu'a take yi ya ɗauka don bata jin zata iya riƙe kanta don gab take da rasa ji da ma ganin ta gabaɗaya, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka, cikin sarƙewar numfashi da rarrabewar murya ta ce "T....Ta....Taj.....k....k.....ka zo ...ka taimake ni....zan.....zan....mutu.....zan ......mutu." Daga haka wayar ta faɗi daga hanunta jikinta ya saki gabaɗaya idanunta suka rufe.

Duk in da hankalin Taj yake ya tashi, Sai cewa yake yi sa ƙarfi "Hello! Hello! Ameenatu ki na jina?" Sai kuma ya yarda wayar ya nufi part ɗinsu da sauri, so Mom suka bishi baya, daƙin shi ya fara shiga bata ciki sannan ya fito da sauri ya shiga ɗakinta ya na kiran sunanta, wani irin faɗuwa gaban shi ya yi ganinta kwance a ƙasa jikinta duk ya yi wani iri, da sauri ya ƙarasa in da take ya ɗagota jikin shi, "Ameenatu! Ameenatu!" Ya faɗa cikin tashin hankali sai kuma ya miƙe da sauri riƙe da ita ajikinshi ya fito ɗakin da ita, ko da ya fita haraban gidan an rigada an shirya mota sakata ya yi ciki shi ma ya shiga driver ya ja da sauri suka fita daga gidan.

Asibiti suka nufa direct in da aka amsheta emergency, gabaɗaya hankalin Taj a tashe yake, idan wani abu ya samu Naila bai san me zai yi ba, ba zai taɓa yafe ma kansa idan wani abu ya sameta ba, sai yanzu ya fara dana sanin contract marriage da suka yi, kamata ya yi ya yi solving problem ɗinsa da kansa, amma ya je ya jawo ta yanzu ga shi nan su na neman halaka ta, baya ma so ya yi tunanin wani abu ya sameta ɗin, so ya na addu'a allah ya sa da sauƙi Allah ya sa abun bai yi worst ba.

Abu kamar wasa da ƙyar likitoci suka samu kanta, sai ga shi Naila ɗin hadda su oxygen da wasu na'urori, sai abun ya baka tsoro, ko da aka faɗa ma Taj poison ne ta ce haka ya ji kamar ya yi hauka, and ko da aka yi testing abincin da ta ci a lab, ba ƙaramin poison aka saka mata a abinci ba, don poison ɗin ya na da haɗari sosai, don lokacin ɗaya yake kashe mutun, ita kawai za'a ce ne kawai Allah ne ya ceceta.

Hankalin su Mami ya ta shi ƙwarai da jin haka, sai addu'a kawai suke yi allah ya sa ta farfaɗo ba tare da poison ɗin ya taɓi wani sashe na jikinta ba, don yanzu she is unconscious bata san in da kanta yake ba.

Kwanan Naila biyu cikin na uku ta farfarɗo nan aka yi mata wasu gwaje gawaje and Alhamdulillah babu abun da ya sameta sai dai zata cigaba da karɓan treatment da medications, Taj ne ke kula da ita sosai don ajiye aikin shi ya yi gefe ya na kula da ita, ƴan gidan su su kawo sun zo haka ma Ilham, so abokan aikinta dai dama anan asibitin take aiki so duk sun zo sun dubata.

Satin ta biyu a asibiti aka sallamo ta bayan an haÉ—a ta da magunguna.

Da dare,
Zaune take saman gado ta jingine da kan gandon, ta na sanye da kayan bacci, while Taj na tsaye gaban mirror ya na fesa turare shi ma shirye cikin kayan baccin, ajiye turaren ya yi ya juyo ya kalleta, "Babu abun da kike buƙata?" ya tambayeta, shuru ta yi ta na kallonshi kafin ta ce "Ruwa." "Ok." Ya ce ya na ficewa daga ɗakin don ya ɗauko mata ruwan da kallo ta bi shi ta na murmushi , Actually bata taɓa tunanin Taj is so caring ba, like da gaskiyar Taufeeq sa ya ce Taj ɗin ya na da sauƙin hali if u understand him, yanzu ta fara gane Taj ɗin.

Yanna da sauƙin kai sosai fiye da yanda ake tsammani, kawai abubuwan da suka faru da shi ne suka yi shaping ɗinsa into something else, but Taj ya na da halin ƙwarai he is so caring and guntule, da ace auren soyayya suka yi zata ce he is very romantic, but regardless he is still romantic.

Ta na zauna ya shigo cikin ɗakin riƙe da bottle water ya kawo mata, ya buɗe sannan ya bata bottle ɗin, ahankali ta saka hannu ta amsa, "Nagode. " Daga haka ta kai ruwan bakinta ta sha kaɗan, amsan ruwan ya yi ya rufe bayan ta gama sha ya ajiye bottle ɗin a side drawer ɗinta, sannan ya wuce ya hau gado the other side ya kwanta, shuru suka yi tsakanin su kafin ya ce "Pls Ameenatu ki na lura da abin da zaki ci ok?" "Ok." Ta ce daga haka babu wanda ya sake cewa komai tsakanin su.

Bayan kwana biyu.

A hankali ta buɗe drawer in da maganinta suke, ta kwaso su ta ajiye kan drawer ɗin sannan ta shiga shan su yanda aka rubuta instruction ɗaya bayan ɗaya, bayan ta gama sha ta mai da, wucewa ta yi toilet ta yi wanka don ta na so ta yi shirin bacci, wanka ta yi wanda da ƙyar ta ƙare wanka saboda jiri da take gani, haka take jin kanta high kamar irin ka yi shaye shayen nan closet ta wuce, da ƙyar ta share ruwan jikinta ta saka underwears, sannan ta wuce in da jirin kayan su suka da yake yau ɗakin Taj ɗin ta yi wanka, biyu biyu take ganin kayan so kawai ta janyo t shirt ɗaya ta saka ta na fitowa daga closet ɗin a daddafe, wanda da ƙyar take buɗe idanunta don sun yi mata nauyi.

Ta na fitowa suka haɗa ido da Taj da ya shigo ɗakin, wani irin murmushi ta sakar mishi wanda tun da yake bai taɓa ganin ta yi murmushin ba, and at the same time mamaki yake yi don t shirt ɗinsa ne sanye jikinta wacce ta yi mata faɗa da ma tsawo gabaɗaya, don ta kai mata gwiwa kamar half gown.

"Tajudden. " Ta ce ta na nufo in da yake at the same time ta na daria, "Tajuddeen ." Ta sake kiran sunan shi ta na ƙarasowa in da yake ƙafafunta suka harɗe ta tafi zata faɗi ya yi sauri taro ta, ta faɗa jikinshi, ɗagowa ta yi ta na kallon hannayenta da ta dafa ƙirjinsa sai kuma ta ɗago ta kalli fuskarsa ta na murmushi cikin muryan ta na kamar mai jin bacci ta ce "Mr Tajudden ka na da faffaɗan ƙirji." Ta ce ta na shafa ƙirjinshi, wani irin ya ji kan maganar da ta faɗa, bai an kara ba ya ji ta ce "Laa ka na da Abs, bari in gani packs nawa ke gare ka."
Chapter 32 · 0% Book details