← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 71

Sashe 39

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta saka masa ta ajiye gaban sa sannan ta saka nata ta zauna kusa da Taj dama kusa dashi take zama kullum, shuru wajen ya ɗauka kowa ya soma cin abincin shi, a hankali Taj da yake lure da Naila ɗin wacce bama cin abinci take yi ba wasa da shi take yi, matsar da face ɗinsa ya yi ɗan kusa da ita ƙasa ƙasa ya ce "Me ke damun ki? Koh cramps ɗin ne har yanzu." Juyowa ta yi ta kalleshi ta na mamakin ya aka yi ya san meke damunta, slowly kamar wacce ake controlling ta gyaɗa kai "Sorry." Ya ce ƙasa ƙasa.

Cigaba da cin abincin suka yi in da Mike sai santi yake yi don plate biyu ya canye duk ya ishe su da surutu, su na gama cin abincin ta koma part ɗin su ɗakinta ta wuce duk da bata jin daɗi but akwai aikin da ya kamata ta yi, sai around 10 bayan ta saka kayan bacci ta nufi ɗakin Taj,  ko da ta shiga baya ciki but ta ji karan ruwa a toilet,  a hankali ta ƙarasa bakin gadon ta na ɗaukar duvet da pillow ta kai kan sofa din da take kwana ta ɗora don a kwanakin Ayan ya bar kwana ɗakin.

Ta na tsaye bakin sofa a hankali ta ji an rungumeta ta baya tare da zagoyo hannunsa kan cikinta, ya yin da face É—insa na kan shoulder É—inta jar ta na jin É—umin numfashinsa a fuskarta, kasa motsi ta yi, a hankali Taj ya saka hannunsa É—aya cikin rigar ta ya na É—ora shi kan cikinta, kafin slowly ya yi sliding hannunsa cikin wandonta ya na É—ora shi kan mararta, wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta na jin wani iri ajikinta, and she is feeling so uncomfortable, especially da hannunsa yake kan bare mararta.

"How are u feeling. " Ya ce cikin soft voice wanda ya sakata lumshe ido don kuwa a kunnenta ya yi magana, and ta na jin saukar numfashin sa, gyaÉ—a kai kawai ta yi batare da ta ce komai ba ta na jin yanda yake massaging mararta a hankali.

A hankali ya kama kunnenta kaɗan ya na sakar mata numfashi me ɗumi kafin ya ciza sai dai ba sosai ba ɗan slight cizo haka da yasaka tsigar jikinta ta shi gabaɗaya ta na ɗora hannunta kan hannunshi dake kan marar ta tare da kiran sunan shi a kasalance "Umm." Ya amsa ya na sakar mata kiss gefen wuyanta da ya sa ta sake ƙanƙame hannunsa tare da cewa "Taj." Cikin wani irin naked voice, jikinta na sakewa gabaɗaya ya zamana shi ne yake tallafe da ita.

Sake kissing wuyanta ya yi da ya sa muryanta na rawa tace "Taj pls dan Allah ka daina." "In dai na me." Ya ce ya na juyo da ita ahankali ta fuskance shi, ɗago kanta ta yi ta na buɗe idanunta da suka soma canza launi ta kalleshi, wani irin faɗuwa gabanta yayi, yayin da take kallon idanunsa,  saboda wani irin kallo da yake yi mata like naked look, ta sha ganin ya na yi mata  irin wannan kallon but na yau ya bambanta da na kullum,  kallonshi take yi ta ma kasa motsawa ya yin da yake matso da face ɗin sa dab da tata.

Sai dai kafin ya kai ga abun da yake son yi aka yi knocking ƙofar ɗakinsu, ɗan kauda kai ya yi ya na kallon ƙofa don ya san Ayan ne, ɗan numfashi ya sauke ya na shafa gashin kanta don kuwa ta kwantar da kanta ne akan ƙirjinshi, jikinta duk ya mutu ya yi weak sosai.

A hankali ya saka hannun ya ɗauketa ya nufi gado da ita ya kwantar, kafin ya koma ya ɗauko bargo da kuma pillow ɗin da ta ɗora kan kujera ya ɗora akan gadon, sannan ya je ya buɗe ma Ayan ƙofa, aikuwa ya na shigowa ya yi tsalle ya faɗa kan gadon, sai sa Taj ya tsawatar masa akan ka da ya dami Naila ɗin.

Washegari da safe ta na fitowa zata je wajen aiki da Mike ta fara haÉ—uwa, ba ma ita ta fara ganinshi ba shi ya fara ganinta sai ganin shi ta yi gaban ta ya na cewa "Goodmorning favourite cousin in-law. " Wani irin kallo ta yi masa ta na cewa "Am not ur favorite anything. " Jinjina kai ya yi "So u r a Dr?" Ya ce ya na kallon labcoat É—in dake hannunta "Well as u can see." Ta ce ta na yin gaba abunta, É—age kafaÉ—a ya yi shi ma ya nufi part É—in shi.

Around 6 ta dawo gidan, a haraban gidan ta gansa shi da Ayan su na wasa da sauri Ayan ya zo wajenta ya na rumgumeta "Welcome Ummi. " Murmushi ta yi "Thank u my boy." Ta ce ta na shafa kanshi, sannan ta riƙe hannunshi suka nufi entrance ɗin palor "Welcome Fav......" Wani kallo da ta yi masa ne ya sakashi sakin daria ya na cewa "Chill mana, Cousin in-law. " ƙyaleshi ta yi ta na wucewarta cikin gida, don wallahi wani kalan haushi Mike ɗin yake bata.

Tare da Ayan suka wuce part ɗinta sai surutun abun da aka yi musu a islamiya yake yi, watsa ruwa ta yi suka yi sallan magrib sannan ta shiga kitchen ta dafa musu fast food duka zauna ita da ayan suka ci don yau kam bata iyawa da surutun Mike shi ya sa bata fita,  bayan sun ƙare suka yi sallar isha'i suka zauna anan palor Ayan ya na kallon cartoon ita kuma ta na aiki da laptop.

Washegari bata je asibiti ba bata da duty, ta na zaune a palor ta na aiki da system dinta Ayan kuma ya na gefe ya na wasa da kayan wasan shi, da yake an tashi daga makaranta, shigowa palorn Mike ya yi "Hey." Ya ce ya na É—aga mata hannu, ko kallon shi bata yi ba haka ya saka shi wucewa direct cikin kitchen ya buÉ—e fridge ya É—auko fresh fruits drink da ta yi ta yi packaging É—insu cikin wasu fine bottles guda ya dauko ya na dawowa palor, ya zauna kan kujerar dake facing tata, ya saka hannu ya janyo plate na snacks dake gabanta ya shiga ci.

Ɗagowa ta yi ta kalleshi ta na yamutsa fuska ba tare da ta ce komai ba ta koma ta cigaba da abun da take yi, ganin bata tankashi ba ya saka shi fara surutu shi da Ayan don kawai ya dameta, su na haka Taj ya shigo palorn, idanunshi na kan Mike har ya ƙaraso cikin palor ɗin, 'What are u doing here?" Ɗage kafaɗa Mike ya yi "Na zo wajen cousin in-law ne."

Kallon Naila Taj ya yi wacce koh É—agowa bata yi ba sai aikinta kawai take yi, sai kuma ya girgiza kansa ya na wucewa ya shige cikin É—aki, Ayan na binshi baya ta na fada masa abun da malamar su ta makaranta ta ce.

Bayan Taj ya wuce Mike ya juyo ya kalleta "Cousin in-law. " Ɗagowa ta yi cikin gajiya ta ce "Am not in the mood of talking,  can't u read the room for god sake." "Sorry." Ya ce da ita bai sake magana ba.

Meemziey's pen

Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

page___________2️⃣3️⃣

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda Mike ya addabi rayuwar Naila sai laƙe mata yake yi ko bata yi masa magana ba sai ya yi mata, tun ta na ƙyaleshi har ta fara biye mishi, koh don ta saka Haulat jin haushi don ta gane Haulat bata son shirin da suke yi da Mike ɗin, shi kuma Mike bai da irin halin su so shi babu ruwan shi, kawai dai iskanci ne ya yi masa yawa irin na wanda ya tashi ƙasar waje, tun da almost rayuwanshi acan yayi.

Kuma Mike din cikin gidan babu wanda ya laƙe ma irin Taufeeq wato Tee da Naila,  in baka ji ya na kiran Tee ba toh bakinsa zai furta cousin in-law, sannan bai da part ɗin zama sai na su Taj abun da yake ba Taj haushi kenan, kuma shi Mike ɗin sometimes da gangan yake yi saboda ya ba Taj ɗin haushi.

Tsaye take cikin babban kitchen ta na girki, ba wai girkin gida take yi ba Mami take yi ma girki, don yau she just feel like doing it, ta na tsaye sanye da Apron Taj ya shigo, "What are u cooking?" Ya ce ya na ƙarasowa cikin kitchen ɗin "Abincin Mami ne." Ta ce ta na juyowa ta kalleshi face ɗinta da murmushi,  hannunta ya kama a hankali ya na murzawa, shi ma ɗin murmushi yake yi "Sannu da dawo." "Yawwa sannu da aiki." Ya ce ya na kai bayan hannunta bakinshi ya yi kissing.

Sai kuma ya janyo hannunta É—aya ya na sakata jikinsa, "Yah jikinka fever É—in ya sauka?" Ta ce ta na zare hannunta daga nashi ta É—ora shi kan goshinsa, "Umm thanks to u."

Haulat dake bakin ƙofar kitchen ta na kallonsu idanunta sun yi ja ranta na ɓaci zuciyarta ta yi mata baƙi ƙirin, jawo ta ta ji anyi da ƙarfi ta na juyawa suka haɗa ido da Mike, janta ya shiga yi zuwa ɗakinta su na shiga ya saki hannunta ya na kallonta cikin takaici ya ce "Wai ke har yanzu son Yah Taj kike yi? Har yanzu baki haƙura da shi ba? Don't forget this man is married and u r still following him, where is ur pride na ƴa mace? Where is it." "Ban da shi." Ta faɗa a tsawace "Na yadda shi tuni, bayan na yada na bi takansa na tattaka sa." Ta ce hawaye na sauka kan kuncinta.
Chapter 39 · 0% Book details