← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 71

Sashe 45

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallon shi daga mom har Haulat suke yi sun ma kasa magana, Haulat da abun ya ishe ta ta ce "Mom she took over everything har a office, she is the one controlling everything i heard people saying that." Kallon shi mom take yi ta na tunanin something 8s definitely wrong with Taj coz ta yaya zai bar mata komai ta na kula da shi Taj da baya wasa da aikin shi ya aka yi haka ta faru, "Taj are u sick or something,  akwai abun da ke damun ka ne how could u live everything a hannun bazawarar matar ka?"

Ɗan frowning face Taj ya yi "Stop disrespecting my wife,  ki san abun da zaki ce." Ya fada fuskar sa haɗe, kama hannunshi naila ta yi ta kalleshi "Honey wallahi duk surutun nan ya saka na yi loosing appetite ɗina, lets go out and eat." "Oh sorry baby, lets go." Ya ce ya na kama hannunta suka fice, su na ficewa dai dai Taufeeq da Mike su na shigowa suka zo suka iske su mom cirko cirko tambayar su suka yi me yasa suke tsaye a wajen nan ne Haulat ke faɗa musu komai, shi Taufeeq bai damu ba don damuwar da yake ciki ta ishe shi damuwar ummu, don har yanzu bata kira shi ba kuma ya aika aje a duba gidan su can Germany aka ce ai basu nan sun koma ƙasar su suma.

Sannan ya san yah Taj baya yanke hukunci sai da dalili don Taj ɗin ya san abun da yake yi, kai koma dai menene in ta ruɓa zasu ji wari.

Wani fancy restaurant suka je suka ci abinci su uku ita Taj da kuma Ayan suka yi hotuna sannan suka dawo sai ma around 10 suka dawo.

Bayan kwana biyu Naila na zaune a palorn ta ta na aiki da laptop Haulat ta shigo wajan rai ɓace, ta tsaya gaban Naila ɗin ta ce "Don me zaki yi haka na je cire kuɗi a family acc an ce limit is 50k." Ɗagowa Naila  ta yi "Uhum to ya akayi 50k ɗin ba kuɗi bane?" Wani kallo Haulat ta yi mata "Koh man da nake shafawa 50k ba zai siya ba." "Oh ai ban sani ba, toh yanzu ya kike so ayi?"

Naila din ta tambaya a ɗage "500k nake buƙata." Jinjina kai Naila ta yi "Ok, so sai kin rubuta application da kuma reasons da ya saka kike son 500k ɗin sai na baki idan har kina da valid reasons." Wani kallo haulat ta yi mata "Is this a bank or something da sai na rubuta application,  neman aiki nake yi hala?" "Uhum idan kin ji baki iya wa just go and use ur money wannan kuɗin mijina ne nake tattali, ba na so ana ɓarnar dukiyar mijina."

Naila ta faÉ—a ta na maida kanta kan laptop É—inta, tsaye haulat ta yi wallahi she urgently need that money, gashi bata da kuÉ—i a acc É—inta shekaran jiya ta yi using dinsu gabaÉ—aya ta canza waya da niyar daga baya sai ta É—eba cikin family acct É—in gashi yanzu Naila ta rufe komai.

Juyawa ta yi zata wuce cikin mugunta Naila ta ce "Bana son application ɗin, kawai ki zo ji bani dalilinki a baki and sai in baki kuɗin." Kamar bazata yi ba sai kuma ta dawo, haulat tafi ƙarfin minti 30 ta na yi ma Naila bayanin abun da zata yi da ƙudi, daga ƙarshe Naila ta bata 250k kamar zata mutu haka haulat take ji.

Monday
Zaune suka cikin office ita da Taj wanda yake zaune kan sofa can nesa ita kuma ta na zaune kan kujerar shi ta na duba wasu files, Sadeek ne ya shigo office ɗin riƙe da file na wani project da suke yi shi da Taj, bayan sun gaisa zai miƙa ma Taj  file ɗin naila ta ce "Hand it over here." Kallon Taj sadeek ya yi Taj ya gyaɗa masa kai, confusely ya miƙa ma naila file ɗin ta shiga duba file ɗin, sannan ta miƙa ma sadeek tare da furta approved "Ka bashi ya yi signing. "  bama Taj pen file ɗin ya yi ya yi signing.

Mamaki ya kashe sadeek da ya ma kasa magana, kawai ya fice ya na fita ya É—an juyo, ta glass ya ga naila ta taso ta zauna kusa da Taj É—in ta na yi masa magana shi kuma Taj ya na murmushi ta na saka hannunsa cikin nasa, wani irin kallon su yake yi kafin ya juya ya wuce.

Wasu tunanuka na yawo aranshi, ya na tunanin how on earth Taj ya bari Naila take controlling É—insa, tun ba yau ba ya gani don akwai ranar da yazo office É—in ya iske an kawo ma Taj coffee naila ta ce a maida coffee É—in, shin, ba ta ce Taj ya rage sha coffee ba? ranar ya sha mamaki but na yau yafi bashi mamaki, ta yaya in aka kawo maka abu sai matar ka ta duba ta yi approving kafin ya yi signing so idan bata yi approving ba shikenan project É—in ya tafi a banza kenan, haka dai ya yi ta tunanukan shi har ya koma nashi company É—in.

Bayan kwana biyu, yau urgently ya shigo company É—in ya zo office din kai tsaye ta buÉ—e ya shigo coz he never expect zai ga abun da ya gani, naila na zaune kan table shi kuma Taj ya na tsaye in between her legs they were kissing each other basu ma san Sadeek É—in ya shigo ba, da sauri ya koma baya ya na ficewa daga office É—in, yanayin shi na canzawa gabaÉ—aya fasa shiga ya yi kawai ya koma ya fice daga office É—in.

And daga ranar sai ya kama zuwa office É—insu, sometimes unannounced ya zo su zauna da Taj su yi magana akan business da sauran su, sai ya zamana ya fi zama a company É—in Taj more than his, and tsakanin Taj da naila É—in babu wanda ya yi masa magana saboda me shi ya ji ya na iyawa ya baro na shi aiki ya zo nan.

Yau da sauri ta tashi anan zata bar Taj ɗin saboda ta yi ma Ayan alkawari za su yi wa kuma zata yi masa pancakes,  sai Taj ya ce driver ya kaita ya dawo, sai sadeek ya ce ba sai driver ya kaita ba shi ma ya tashi zuwa gida bari ya yi dropping nata, no problem Taj ya ce, naila ta mike ta hada kayanta ta ƙarasa in da Taj yake ta sakar masa peck a kumatu tare da cewa "Take care and don't come late Ok." Ok." Ya gyaɗa kansa ya na sakar mata murmushi sadeek na daga gefe kanshi a ɗuke, ficewa ta yi sadeek ya yi bayanta, zuwa wajen motar shi ta buɗe passenger's seat ta shiga, shi kuma ya shiga driver seat, shuru motar ta yi can sadeek din ya ce "Why are u intimate with Taj?"

Naila bata amsa ba saboda bata zaci da ita yake ba, probably maybe waya yake yi coz she see no reason da sadeek zai yi mata wannan tambayar akan mijinta ba ma wani ba, so bata amsa shi ba, shi ma bai sake cewa komai ba har ya sauketa.

Shiga cikin gida ta yi ta wuce part ɗin su ta yi wanka ta canza kaya sannan ta shiga kitchen ta fara soya pancakes din kafin Ayan ta dawo daga islamiya, ta na tsakar soyawa ne ya dawo sai murna yake yi, sai da ya ci pancakes ɗin sannan aka cire uniform ta yi masa wanka, ta canza masa kaya, da ita da shi babu wanda ya ci dinner aranar sun ci pancakes sun ƙoshi.

***********
Tsaye yake gaban wasu na'urori (computers) da suke ɗauke da live footage na office ɗin Taj palorn Taj kitchen, office ɗin naila da dai sauran su, footage na palorn Taj yake kallo wanda naila ke zaune a ƙasa ita da Ayan ta na yi masa assignment taj kuma ya na zaune kan sofa ya na kallon news, wani irin kallon footage ɗin yake yi idanunsa ba yi jaa ya ce, "U are not suppose to be happy Tajudden, especially with her coz she is mine." Ya ce ya na dafe table ɗin gaban sa.

"U are not suppose to be intimate with her, saboda ita tawace, naila ta wace, ni ya kamata in mallaketa ni ya kamata na aureta, wai me ya sa kake samun komai a sauƙaƙe, u have manage to win her over." Ya ce ya na datse haƙorinsa idanunsa na sake yi jaa, ka na jin ƙamshin hassada ƙarara na fitowa daga gareshi.

Meemziey's pen

Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

page __________2️⃣6️⃣

Haka rayuwa ta cigaba da kasan cewa, sai dai yanzu wani sabon Almari da ya bullo ma naila na wata unknown number da take kiranta, ba za'a yi magana ba sai dai ayi shuru, ta na hello hello, da kira aka fara daga baya kuma sai aka soma turo mata massege kamar haka "Be careful who u trust." Da ta nuna ma Taj ya ce ta yi ignoring dinsa, daga baya aka sake turo mata "Ki na tunanin ya na son ki ne?"

Ita ta san ba su Ammi koh Mr Sidi bane, "You're smarter than they think. Don't let anyone control you." Bata mai da hankali kan abin ba sai da aka fara turo mata masseges akan abun da ke faruwa cikin gida, ta san akwai camera a palor din but ta zaci su Ammi suka saka, so shi wannan da yake turo mata waÆ´an nan masseges waye shi daga ina ya fito ta zaci su Ammi ne kawai shin dama akwai wasu, tunani dai kala kala.
Chapter 45 · 0% Book details