← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 71

Sashe 63

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta na tsakar kallo ne taj ya shigo kashe wayar ta yi ta na ɗagowa a hankali ta kalleshi, shi ma kallonta yake yi ganin idanunta sun yi ja, da alama har yanzu abun na aranta, ajiye wayar ta yi gefenta a ƙoƙarinta na son kauda abin ta karasa jn da yake ta na shiga jikinshi ta rungume shi, "Sannu da zuwa." "Yawwa." Ya faɗa ya na rungumeta back ya shiga shafa bayanta ba tare da ya ce mata komai ba but rarrashin ta yake yi, baya so ya yi mata maganar har sai lokacin da shirya ta sauko sannan su yi maganar, ba ya so ya fara saka bakinsa a family problem ɗinta, sai ranar da ta yi niya su zauna su yi sorting things out

Sun daɗe a haka sannan ya raba hug ɗin ya na kallon face ɗinta, ita ma kallonshi take yi, kissing goshinta ya yi sannan hancinta sannan ya yi kissing lips ɗinta, a hankali ya ɗauketa ya na nufar gado da ita ya kwantar da ita gefen ayan ya na jan blanket ha rufeta, "Sleep ok? Ka da ki saka damuwa a ranki, it will only cause u pain." Jinjina kai ta yi, ya yi kissing goshinta sannan ya miƙe ya shiga rage kayanshi toilet ya nufa ya watso ruwa ya fito ya shirya cikin kayan bacci ya kwanta bayan ya kashe wuta.

Kusan kwana biyu suka cigaba da sha'anin su, babu wanda ya sake ta da maganar, shi dai Taj akwanakin he is very busy bai cika zama ba sai dare yake dawowa so basu samu damar yin magana ba.

Yau da latti sosai ya dawo ya isketa palor ita da Ayan sai dai Ayan ya yi bacci, ita kaɗai ta rage ta na kallon cartoon, ƙarasowa ya yi ya zauna kusa da ita "Barka da dawowa. " ta ce ta na kallonshi, rungumeta ya yi ta gefe ya na kissing goshinta, "Yawwa ya kike?" "Lfy qlu." Ta ce sannan ta miƙe a hankali ta na sauke kan ayan daga jikinta ta nufi kitchen ta ɗauko masa drink na fresh fruits da ta haɗa ta kawo masa, amsa ya yi "Tnx." Sannan ya kai bakinsa, lumshe ido ya yi saboda sanyin drink ɗin da ya ratsa shi, ga kuma wani daɗi da galmi galmi.

Bai ajiye cup ɗin ba sai da ya shanye,  amsan cup ɗin ta yi ta ajiye kan table sannan ta kalleshi, duk da ya ga kamar magana take so ta yi sai dai bai ce komai ba, "I want us to talk." Ta ce a hankali jinjina kai ya yi "Ina jin ki." Wani abu ta haɗe, "It about my father's side of the family,  i will like to meet them. " ta ɗan dakata, kallonta ya yi "Continue ina jinki." Ta cika gaba da cewa "I'd like to go to Jubala, i want to meet them, and i have so many things to ask them."

Ta sake yi shuru, a hankali ya ce "Ke kaɗai kike so ki je or do u want me to escort u." Ɗago idanunta ta yi "I want us to go together, u are my husband after all." "Jinjina kai ya yi, our visa na zuwa Jubala is already out har an yi approving,  ka wai ki faɗi ranar da kike so mu je koh yanzu kike so we can go there,  in da PJ private jet kike so in kuma da public plane, ki zaɓi ko wanne kike so." Numfashi ta ja ta na mamakin yaushe duk ya yi waƴan nan, ko da busy ɗin da ya yi don harakar visa ɗinsu ne.

Shi ya sa bai zama gida, shi kuma abun da ya saka ya yi preparing shi ne ya san ko ba daÉ—e koh ba jima dole wata rana sai ta ce masa ta na so ta je Jubala and she he is ready to do duk abun da take so, "Aa i want us to go on public plane, bana so muja attention. " ta É—an yi shuru kamar mai tunani sannan ta ce "Nan da two days fah, ya yi?" Murmushi ya yi ya na jinjina mata kai "Eh duk abun da kike ce." Rumgume shi ta yi "Nagode sosai, Allah y......" "shhhhh." Ya dora yatsan sa a lips É—inta babu godiya a tsakanin mu.

Jinjina kai ta yi, sun dade a haka kafin su koma É—aki hadda ayan.

And daga nan suka fara shirya shiryen barin ƙasa, a kwanakin her heart felt so heavy Kamar an ɗora mata dutse akai, amma haka take yi ta gurgurawa,  sai tunani take tambayoyi na yawo akanta, Shin idan ta je me zata ce musu?
Shin ya ya zasu tarbeta?
Shin zasu yarda da ita?
Mahaifin nata zai amshe ta hannu biyu biyu?
Idan dama sun san da ita fah kawai sun zaɓi su rufe abun ne fah?
Shin Shin Shin?
Sun yi mata yawa akanta, don har wani ciwo kanta ke yi ga yanda take yawan faÉ—uwar gaba.

Haka dai take yi ta anticipating, sun sanar da ƴan gidan zasu yi tafiya sai dai basu sanar da su ainihin in da zasu tafi ba, suka ce Italy zasu tafi, ayan sai tambayar ta yake yi me ta sa take haɗa kayanta a akwati, sai ta ce masa tafiya zata yi, ya ce ya na zuwa ta ce ya yi haƙuri wani aiki zai kai su.

Shi kuma gefen taj ya na nan ya na shirya musu komai da komai tun daga transport accommodation É—insu in suka isa can da transport É—insu da komai ma, duk ya na nan ya na shiri.

Ana nan aka kai ranar tafiya, Wanda da ƙyar aka rabata da ayan, gashi ranar sai zuciyarta ta sake yi nauyi,  nauyi sosai, sannan ta na ta bugawa da ƙarfi, she is nervous anxious da komai ma, ita ta manta yaushe rabon ta ji irin wannan feeling, becoz she always held her head high she is confident,  but now, her confident as shattered into smaller tiny pieces that cant be fixed.

Har suka isa airport da yake public plane zasu shiga, aka yi checking ɗinsu sannan suka ɗaga in da first class suka shiga, shi taj bai taɓa ganinta cikin wannan halin ba koh sau ɗaya,  bai san wannan side nata ba, he only knows the brave and confident side but this side, it doesn't suit her koh kaɗan.

Dole cikin jirgin ya yi ta rarrashinta da ƙyar ya samu ta kwantar da hankalin ta, tafiyar awanni suka sauka a Al Najm International Airport, Hali, Jubala.

Bayan sun gama duk abun da zasu yi a airport É—in Wata dalleliyar mota ta zo ta É—auke su zuwa hotel É—in da ya yi booking, hotel É—in babban hotel ne da kuÉ—in kwana É—aya sai ya kusa zaunar da kai, but bai damu ba coz money is not the problem.

Bayan sun isa masaukin su wanka suka yi tare da sallah sannan suka huta, ba zasu fita ba sai gobe.

Wanda a daren ranar sai da ta samu attack ɗin da ta kan samu duk da ta daɗe bata sameshi ba sai yau, ta na yi ta kuka hankalin Taj duk ya tashi sai aikon rarrashinta yake yi, haka suka kwana, wanda washe gari ya ce idan bata jin ƙarfin jikinta ba sai ta yi ba ta ce ta na iya wa, ko da safen sai da ta samu wani attack, duk da haka ta dage da cewa sai sun fita.

Haka suka shirya taj ya kira driver É—in da zai É—auke su zuwa Haddad Estate.

A hankali motar su ta yi parking a bakin babban gate na haddad estate wanda aka rubuta Haddad Estate da babban baƙi black and gold rubutu, Tajuddeen sai kallon logon gidan yake yi ba wai don ya san gidan ba, sannan ba don ya taɓa shiga gidan ba, sai dai don ya san wannan sunan kuma ya taɓa aiki da mai wannan sunan, wato Haddad, sake riƙe hannun Naila ya yi wacce duk jikinta ya yi sanyi, dukan su basu sani ba, amma fuskarta, wato fuskar naila, fuska ce ta sani fuskace da duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta saboda wata irin fuska ce da ta taɓa gina babban tarihi a ƙasar jubala, sannan ta zama wata irin bala'i a wannan ƙasar, su ba su sani ba, sai dai waƴanda suka san da haka da sun kalli fuskar sun sani.

Sai tambayoyi securities din bakin gate suke yi musu daga ƙarshe hana su shiga aka yi saboda basu da pass sannan babu wanda ya san da zuwa su a gidan, har ya dauko wayar shi zai yi dialing wata number sai kuma ya ɗago ya na kallon wata mota da ta yi parking a wajen, Saifuddeen, babban ɗa na gidan ya fito daga motar, ya nufi securities ɗin bakin gate din suna magana.

Numfashi Taj ya sauke don ya gane wannan fuskar saboda har ya mutu ba zai taɓa manta ta ba, Saif ɗin abokin business din sa ne a da, lokacin da suka yi aiki tare akan wani project su na shiri sosai duk da ya bama saif ɗin shekaru, sannan bayan sun gama project ɗin suka rabu lafiya wanda basu sake jin motsin juna ba sai yau da shi Taj ɗin ya ganshi.

A hankali ya saki hannun naila, ya na buɗe marfin kofar ya fita, ɗan juyowa saif ya yi suka haɗa ido da shi, Cak ya dakata da maganar ya na kallon Taj ya na tunanin in da yasan face ɗinnan, duk da halin da yake ciki sai da ya saki murmushi saboda ya gane waye a wajen, A tsaye a gaban shi Tajuddeen Ibrahim Abad yake gani, mutumin da suka shafe tsayin shekaru basu haðu ba.

A hankali Saif ya shiga takawa zuwa inda yake haka ma taj suna karasawa, Saif ya bashi hannu suka gaisa har yanzu mamakin ganin Taj Abad yake yi a wajen, don ha sake tabbatarwa sai ya ce "Tajuddeen Abad?" Murmushi Taj ya yi shima ya ce "Saifuddeen Haddad." Ganin da gaske shi ðin ne Saif ya girgiza kanshi "Wallahi ban taɓatunanin zan sake ganin ka ba." Taj ya yi ,yar dariya
"Ni ma ban yi tunanin zan gan ka ba."
Chapter 63 · 0% Book details