← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 71

Sashe 35

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da asuba
Da addu'a tashi daga bacci ya farka a bakinshi, zaune ya miƙe, ya na jan siririn tsaki, haushi da takaicin kanshi na kama shi lokaci ɗaya saboda mafarkin da ya yi, sauka daga kan gadon ya yi ya nufi toilet wanka ya yi tare da alwala ya fito ya shirya ya nufi masallaci, bai ta da ita ba saboda yasan bata sallah wanda ita karan kanta bata san ya sani ba.

**************

Berlin Germany
Charitè Universitätsmedizin Hospital
Taufeeq

A hankali yake takawa acikin corridor É—in ya na amsa waya a hankali while hannunsa É—aya zube cikin aljuhun expensive suit É—insa na chanel, calmly yake amsa wayan kafin a hankali ya ce "Yes, i already reviewed the documents." Ya faÉ—a da yaren turanci, kafin cikin wani low but steady voice ya ce "I'll send the final respond tomorrow. " Daga haka ya katse kiran ya maida wayar cikin aljuhun shi.

Alokacin ne idanunshi suka sauka akanta, a can ƙarshen corridor ɗin, zaune a ƙasa babu takalmi a ƙafafunta, ta na sanye cikin kayan asibiti na patient riga da wando sai wata over size cardigan da ta ɗora asama, ta na zaune ta ɗunƙule waje ɗaya yayin da gashinta da yake baƙi da kuma sosai ya zubo ta gefen shoulders ɗinta.

Kusa da ita wata nurse ce a durƙushe ta na lallashinta akan ta tashi su koma ɗakinta, amma yarinyar koh motsi bata yi ba, "Please." Nurse ɗin ta faɗa cikin German accent "You cannot stay here."

Amma yarinyar bata koh kula ta ba idanunta na kan wani glass window ta kafe window ɗin da kallo koh ƙyeptawa bata yi bare motsi, ta yi shuru.

ÆŠan kallonta Taufeeq ya yi na wani lokaci kafin ya É—auke idonshi daga gareta ya cigaba da tafiya.

Ita kuma nurse ɗin cikin gajiya ta miƙe "I'll come back with the Dr." Daga haka ta juya ta wuce, nurse ɗin na wuce wa a hankali yarinyar ta juyo ta kalli Taufeeq, ɗan dakatawa Taufeeq ya yi tunanuka na yawo a ranshi, tsawon wani lokaci suna kallon juna babu wanda ya motsa, kafin a hankali ta miƙe ta shiga ta kowa zuwa in da yake, kallonta yake yi yayin da take taka tile na hospital ɗin babu takalmi a ƙafanta, sannan ta na tafiya me kamar wacce take koyo.

A hankali a hankali har ta tsaya a gabanshi, kusa sosai har ya na iya lura da ciwukan da suke a tsintsiyar hannunta, da wanda yake a gefen wuyanta, da kuma yanda jikinta ke rawa sosai.

Fuskanta expressionless like babu wani emotion akai. So silent.

ÆŠan kalle kalle Taufeeq ya shiga yi koh zai ga wata nurse ko wani Dr haka but babu kowa akan corridor É—in da yake gefen VIP ne babu wani hayaniya.

Ɗan kallonta ya yi ya ce "You shouldn’t be walking around alone." Babu wani reaction daga gareta sai ma kallonshi da take yi kafin a hankali without warning ta ɗaga hannunta ta riƙe hannun suite ɗinsa, ba hannunsa ta riƙe ba suite ɗin nasa ta riƙe, ɗan frowning face Taufeeq ya yi ya na ɗan ja baya don ta sake shi, duk da ba wani riƙo ta yi ma hannun suite ɗin nasa ba, but it was desperate shi yasa bata saki ba, and kamar she is trying to confirm if he was real.

Slowly ta ɗago ɗayan hannunta, acikin hanunta bata black marker ce, kafin ma ya yi reacting ta riƙe ɗayan hannunsa ta shiga rubutu akanshi, handwriting ɗinta ma is a little bit messy and shaky don jikinta rawa yake yi, "DON'T TRUST THE PEOPLE WHO SMILE TOO MUCH." "Ka da ka yar da da mutanen da suke yi maka murmushi sosai." Shi ne abun da ta rubuta a tafin hannunshi.

Kallon hannunshi Taufeeq yake yi ya na kallon abun da ta rubuta sannan ya ɗago ya kalleta "She told u to write that?" Ya tambaya, bata amsa shi ba sai shuru da ta yi, zai sake magana suka jiyo takun tafiya ta na jin haka jikinta ya shiga rawa sosai, kamar mai jin tsoro da sauri ta koma bayanshi ta ɓoye, kamar wata ƙaramar yarinyar da take jin tsoro.

Wani likita tare da wasu nurses biyu suka ƙaraso wajen "There u are." Likitan ya ce ya na kallonta kafin ya kalli Taufeeq "I apologise sir, she sometimes wanders." Ɗan juyawa Taufeeq ya yi ya kalleta, ta na bayanshi ta wani rirriƙeshi, ɗan kallonta Dr ya yi cikin tausayi ya ce "She suffered severe neurological trauma after an accident."

Ɗan kallonta Taufeeq ya yi bayan likitan ya ƙare magana, "Accident. " ya maimaita cikin zuciyarshi wani tunani na yawo aranshi, sai kuma ya jinjina kai ya na saka hannunshi ta baya ya jawota ya miƙa ma nurses ɗin, sai kawai ta juyo ta kalleshi idanunta na tara ruwa wanda for the first time tun da ya haɗu da ita ya ga emotion akan face ɗinta, sai ya ji wani irin jikinshi ya yi sanyi.

Tafiya suka shiga yi da ita ganin haka likitan ya ce "Thank you. " Sannan ya juya ya soma tafiya, har aka yi nisa da ita idanunta na kanshi ta na kallonshi, shi ma Taufeeq ɗin kallonta yake yi wanda har ga Allah bai san dalilin kallon nata ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan sun ɓace mishi sai kuma ya kalli tafin hannunsa in da ta yi rubuta ya na sakin murmushi, sannan shima ya cigaba da tafiya.

Meemziey's pen
[04/10, 14:43] Amina Khaleel: Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

page ____21

Ko da ya koma masaukin shi ko kuma ace gida don kuwa a gida yake zaune, and area din da yake like ya na É—aya daga cikin area na masu kuÉ—i haka, and abun da ya kaishi asibiti shi ne wani abokin aikinsa ne baya da lafiya so ya je ya duba shi ne.

Tsaye yake a gaban mirror ya na É—aure da towel a watse É—inshi da yake wanka zai shiga, face É—insa yake kallo a mirror, kawai sai ta faÉ—o masa a rai a hankali ya furta "Why did she look at me like that?" Sai kuma ya kalli tafin hannunsa in da ta yi masa rubutu duk da Rubutun ya goge but ana ganinshi, a hankali ya cigaba da kallon hannun na shi ya daÉ—e tsaye awajen kafin ya wuce ya yi wanka ya yi shirin bacci.

After 2 days .

Yau ma ya koma asibiti ya je ya duba abokin aikinsa, a hankali yake tafiya cikin corridor É—in a hankali ya kai duban shi zuwa ga in da take zama sai dai babu ta awajen, nurse É—in dake bayan shi ne da ta lura ta ce " looking for someone?" "No." Murmushi nurse É—in ta yi kamar ta san me yake tunani ta ce "The silent girl." Sai kuna ta yi shuru kafin ta sake cewa "She was discharged this morning ."

ÆŠan Jinina kai ya yi feeling somehow disappointed sai kuma ya cigaba da tafiya, ya je ya duba friend din nasa sannan ya wuce wajen aiki.

Da yammacin ranar ya na zaune bayan mota yayin da driver ɗinsa ke tuƙa sa tun da suka shigo layin da gidan su yake ya kafe gidan dake kusa da nashi da kallo, wata ƴar budurwar dake tsaye bakin ƙofar gidan, ta na sanye da farar dagowar riga ƴar kanti sai ƙautuwar rigar sanyi dake sanye ajikonta da yake garin akwai sanyi, kanta sanye da hular sanyi ita ma sai ƙafafunta masu sanye da sneakers, ta na tsaye bakin ƙofa ta zuba ma titin ido hannunta harde a ƙirjinta.

Kallonta kawai yake yi har aka isa ƙofar gidan sa bai sani ba sai da driver ɗin ya yi masa magana buɗe ƙofa ya yi ya na sako ƙafarsa dai dai wata mata ta buɗe ƙofar gidan ta jawo yariyar ciki so basu ga juna ba, numfashi ya fitar ya fito nufi cikin Gidan sa driver na biye da kayan sa.

Washegari da safe ya fito daga morning jogging kenan zai shiga gidan shi ya ji mage na kuka har zai wuce sai kuma ya dakata ya juyo zuwa gidan dake kusa da nashi can ya hangeta ta na durƙushe a wajen wanda ta na sanye da kayan bacci riga da wando har yanzu sai rigan sanyin da take sanye da ita, da kuma hula akanta, gabanta kuwa wata ƴar ƙaramar farar mage ce wacce ta malale awajen, ita budurwar bata lura da zuwanshi ba hankalinta na kan magen, sai ƙoƙarin ciro magen take yi ba tare da ta yi magana ba sai miƙa hannu da take yi.

For almost five minutes ta na haka sannan ta samu ta ciro magen, shi kuwa Taufeeq ya na gefe ya na kallonta, rungume magen ta yi face É—inta na É—an sakewa duk da ba murmushi ta yi ba, sai kawai Taufeeq ya tsaya ya na kallonta, ta na É—agowa suka haÉ—a ido dashi, kallonshi take yi kamar ta na so ta tuna in da ta sanshi, ya mutsa fuska ta yi bayan ta gane shi.

Kallonta Taufeeq yy sai kuma ya maida kallonshi kan magen tare da furta "Ur cat?" A hankali kamar mai tsoro ta ɗan girgiza kanta alaman Aa, kenan ba nata bane, ita kuma magen sai sake shage mata take yi, haka kawai Taufeeq ya samu kanshi da sakin murmushi "So it's like u?" Nan bata amsa shi ba kallonta ya cigaba da yi kafin idanunshi su sauka kan fararen ƙafafunta da babu takalmi balle socks, ɗan haɗe gira ya yi ba kamar faɗa ba ya ce "Ki kama saka takalmi."

Kallon kafafunta ta yi sai kuma ta kalleshi, wani iri Taufeeq ɗin ya ji coz ina ruwanshi, sai kuma ya ce "Take care." Ya juya zai wuce bai yi ta ku biyu ba ya ji an riƙe masa hannu riga kamar dai yanda ta yi ranan a asibiti, kallon hannun ta da ta riƙe masa riga ta yi ita ma sai ta kalli hannu sai kuma ta saki hannun rigar shi ta na kama tafin hannunsa ta saka masa wani abu, kallon abun da ta saka masa ya yi sweet ne, ko da ya ɗago har ta kai cikin gida ta na riƙe da magen.
Chapter 35 · 0% Book details