← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 71

Sashe 3

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da ta karasa gidan su Ilham ko gani bata yi gashi hijab da ta saka ya na damun ciwon ta, ta na shiga palor ta fisge hijab din jikinta tare da sulalewa nan bakin kofa ta kwanta ta na fitar da numfashin wahala.

Dai dai Mom mahaifyar Ilham ta fito daga kitchen, idanunta suka sauka kan Naila dake kwance bakin kofar palor, sa sauri ta karasa in da take "Ah ah Naila me kike yi anan? Subhanallah me ya same ki?" Ta ce ta na kallon bayan Naila É—in da fatar wajen ta tashi don kwanciyar rub da ciki ta yi.

Shuru Naila ta yi ba tare da ta amsa ba don ko bakin magana ba ta da, cikin tashin hankali Mom ta shiga ƙwala kiran Ilham, "Ilham! Ilham! Yi maza dauko min car key ɗina da hijab ɗina yi sauri." "Tau Mom. " Ilham ta ce daga cikin ɗaki bayan Wani lokaci ta fito, da sauri ta karasa in da mom ɗin take zaro ido ta yi ganin yanayin Naila ɗin ai kuwa ta fashe da kuka ta na yarfa hannu "Mom me ya samu Naila ɗin."

"Ni dai kama min ita mu kai ta mota, ta na bukatar ta ga likita." Cikin sauri suka kama tafiya suka fice a back seat suka sakata, kallon Ilham Mom ta yi "Na manta dauko min purse É—ina sannan ki sawo hijab mu tafi." Da sauri Ilham ta nufi cikin gida, bata dade ba ta fito da abun da muka din ta ce, mota suka shiga mai gadi ya buÉ—e musu gate suka yi asibiti, ko da suka isa bata ma cikin hayyacinta a emergency aka amsheta aka shiga bata taimakon gaggawa.

Cikin kankanin lokaci aka yi dressing ciwon nata aka saka mata magani, dole a nan suka kwana a asibitin da yake ma mahaifin Ilham din baya na, da safe around 12 aka sallamo su.

Anan gidan su ilham ta yi zamanta sai bayan isha ta koma gida ta na shiga babu wanda ya tambayeta daga ina take, a ina ta kwana, ko kuma wacce ta yi mata aika aikar ta ce sa ita ya jiki, babu wanda ya yi hakan dakinsu ta wuce ta kwanta, ta yi shuru abubuwa na yawo a kanta.

Washegari.
6:32am
Ta an zaune saman sallaya Inna ta shigo É—akin tsaye ta yi ta na kallon Naila É—in sannan ta ce "Ke baki san ki fito ki yi aiki ba, ko baki san rana ta fito ba." Shuru Naila ta yi ba tare da ta ce komai ba ta na cigaba da jan carbin hannunta.

Cikin hasala Inna ta ce "Wai ba dake nake ba?" Idanunta ta ɗago ta zuba ma Inna ɗin wanda tun da take bata taba kallon mutun hakanan ba, kai bata taba kallon mutun ido cikin ido ba tun da ta taso, kullum kanta a ƙasa yake, yau kuwa da ta zuba ma Inna idanunta masu launin blue wanda nan take Inna ta ji wani irin kaifin su ya na shiga jikinta.

Cikin wani irin cold voice ba tare da emotion ɗin komai ba ta ce "Ba ni da lafiya, koh ba ke bace kika ƙona ni da iron?" Sai kuma ta saki murmushi "Ba zan iya ba Inna. " ta ce ta na sauke idanunta ta cigaba da abun da take yi, haka kawai yau Inna ta ga Naila din ta yi mata wani ƙwarjini sai ma ta kasa yin magana ta fice daga dakin.

Bayan fitar Inna miƙewa ta yi ta koma kan katifarta ta kwanta, nan da nan bacci ya ɗauke ta bata farka ba sai sha biyu, shiryawa ta yi ta wuce gidan su ilham wacce ta raketa wani chemist dake anguwar aka gyara mata ciwonta, bayan sun dawo ta ci abinci sannan ta sha maganinta.

Yau ma sai bayan Isha ta koma gida.

Bayan sati biyu wasa wasa Inna sai ta kasa yi ma Naila din magana akan duk wani aikin gida, Naila kuwa hade fuska take yi bata ma ba da wajen da Inna din zata yi mata wata maganar, ta ji sauƙi sosai ƙonuwar ta tsane kaɗan ya rage wajen ya warke gabaɗaya, har ma ta fara zuwa makaranta saboda shirye shiryen candy da suke yi.

Tafiya take yi a tsakiyar gidan riƙe da bucket da ta jawo ruwa daga rijiya, rana ta yi zafi sosai, zufa na tsiyaya daga jikinta, ta na jin radadi akan ciwonta da ya kusa warkewa, da yake ta dawo da yin ayyukan ta don yau da safe ita ta yi wanke wanke, cikin katuwar robar da suke ajiye ruwa ta zuba, ɗan durkusawa ta yi wajen da yake cikin inuwa ne ta na sauke ajiyar zuciya.

Out of no where ta ji an tsaya mata aka, É—ago kanta ta yi suka haÉ—a ido da Inna, mikewa ta yi tsaye, cikin faÉ—a Inna ta ce "kin kuwa share gidan nan yau?" "Na share. " Ta ce ba da karfi ba da wata kalan soft calm voice, É—an yamutsa fuska Inna ta yi "Ni kike mayar ma magana."

Shuru Naila ta yi sai ta kalli ƙasan wajen, Sai kuma ta ɗago ta kalli Inna "Na share." Ta sake maimaitawa, bata ida rufe baki ba ta ji saukan wani lafiyayyen mari akan kuncin ta, koh gizau bata yi ba duka da ta ji zafin marin, face dinta ne kawai ya kalli gafe, bata fashe da kuka ba, bata ba da hak'uri ba sannan babu hawaye a idanunta.

Kallonta Inna ta yi kamar wacce take tunani koh mamaki, sai kuma ta sake É—aga hannunta, sai dai Naila na nan tsaye a in da take babu alamar tsoro a tattare da ita, "Mene ne? Taurin kai zaki gwada mini?" Juyo da kanta ta yi ta na saka idanunta masu kala cikin na Inna, ba ma zaka gane yanayin ta ba.

"Kina iya duka na." Ta ce a hankali "Amma ƙasan ba zai share kan shi ba, babu abun da zai canza." Wani irin shuru ya ratsa tsakanin su, Inna ta zuba mata ido, for the first time wani abu kamar tsoron yarinyar ya shige ta, tsaki ta yi ta juya ta bar wajen.

Da kallo Naila ta bita, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta na shafa in da Inna din ta mareta, fasa É—iban ruwan ta yi, ta yi wucewarta É—aki ta kwanta, dama ta gaji da zama ne bata yi aiki ba shi ne ta fito ta É—an kama.

5:22pm

Ta na zaune cikin daki Inna ta sake shigowa wannan karon hadda kawunta ya na gida, "Ke fito ki yi wanke wanke." Cewar Inna, ba tare da ta dago ba ta ce "Ita Fa'iza aikin me take yi da ba za ta yi wanke wanken ba?" Riƙe haɓa Inna ta yi "Eyyeh lalle wuyanki ya isa yanka." Sai kuma ta daga murya ta shiga kiran kawu Usman "Baban Fa'iza! Baban Fa'iza. "

"Ke mene ne kike ƙwalamin kira haka?" Ya ce daga can palor in da yake zaune "Yoh zo ka gani, Ameenatu ta girma wai ba za ta yi wanke wanke ba hadda gaya min maganganu." "Kambu ita Ameenatu ɗin ta ce miki haka?" Ya ce ya na tasowa ya shigo ɗakin, idanunshi suka sauka kan Naila dake zaune koh ajikinta, baki cike cikin kumfar baki ya ce "Ke Ameenatu a saka ki wanke wanke ki ce ba zaki yi ba? Hala wa kike?"

Girgiza kai ta yi "Ba kowa nake ba face ƴar ƙanwar ka da ka maida tamkar baiwa, shegiya marar uba, koh ba haka bane?" Ta ce ta na dagowa, ta zuba masa idanunta da suke da wani irin kaifi, kamewa kawu ta yi ya na kallonta ya ma kasa furta komai, "Baiwa nake mana, shegiya marar uba." Sai kuma ta saki wani murmushi mai ciwo "Toh yanzu baiwar ta ce ta gaji da yin wanke wanke da ɗiban ruwa idan Fa'iza ba za ta yi ba, kwanoni su ruɓe amma ba zan taɓa su ba."

Ta ce da wani kalan manipulative murmushi.

Kawu ya ɗauki lokaci mai tsayi ya na kallonta ya na cikin wani irin shock saboda abun da yake hangowa acikin idanun Naila ɗin ya kuskura ya taɓa ta, don wani irin abun ne na komai ta na iya destroying a halin da take ciki.

For the first time wani abu mai kamar tsoro ya shige sa akanta, sai kawai ya juya ya fice, haka ma Inna din, sai baya sun fita take jin muryoyin su su na zage zage murmushi kawai ta yi, ta riga da ta yi alkawari ko da wasa babu wanda ya isa ya sake kai hannunsa jikinta da sunan duka.

Meemziey's pen ✍️
[23/09, 11:19] Amina Khaleel: https://www.arewapen.com/chapter?id=6ab23caacb0cfb2373709948

Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

Page_________3️⃣

Kwantawa ta yi ta na tunani sai kuma ta saki murmushi,  yanzu ta gane, ta gano komai yanzu, idan ka nuna ka na jin tsoron abu lokacin ne yake da damar cutar da kai, TSORO, FEAR, yanzu bata da shi, ko kaɗan yanzu wannan baya existing cikin dictionary ɗinta, aduk lokacin da aka daketa ba wai ciwon dukan ne ka saka ta kuka ba, tsoro ne, don wani lokacin tun kafin a fara dukanta take kuka.

Amma yanzu fah da ta cire tsoron bata jin komai, ba wai bata jin ciwon dukan ta da ake yi ba ne, Aa kawai yanzu ta na iya daurewa, ta na iya shanye duk wani raɗaɗi da ciwo da take ji, ba zata sake ba, ba zata sake barin wani ko da wasa ya taɓa lafiyar jikinta ba.

And tun daga ranar, ta samu lafiya a gidan ta samu ƴancin kanta, babu mai takura mata sannan bata takura kowa, bata da yawan magana komai da ido take yinsa, idan ma ka yi daidai ko ba daidai ba da ido zata gyara maka, slowly da silent treatment ta dasa wani irin shakkarta a zuciyarsu, ta na aikin gida kam idan ta yi niya, kuma yanzu ko da wasa ba'a isa a bata abincin wani da ya raga ba, da an ƙare abinci zata dauki kwano ta je ta ɗiba kuma ba'a isa a yi mata magana ba.
Chapter 3 · 0% Book details