← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 71

Sashe 68

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

El Bashir sai faman dannar ƙirjinta yake yi, wani dr ne cikin sanyin jiki ya janye shi ya na cewa ya bari, wani irin rawa jikinshi ya ɗauka ya na fashewa da kuka ya koma gefe ya ma kasa yin komai, wani Dr din ya ce "Time of death 2:24......" Da wani irin karfi Saif da ya shigo wajen ya ture dr din ya na karasawa in da take kwance ya shiga tattaɓata "Malak Malak malak." Ya kira sunanta har sau uku hankali tashe..

Amma koh motsi bata yi ba jikinta ya yi wani irin fari fayau, lips dinta sun bushe sosai ya yi brown color, fuskarta ta faɗa sosai, da kanta da babu gashi saboda surgery ðin da aka yi mata akai an aske gashin, ga kan nan naðe da bandage, har jiniyoyinta da suka canza kala ka na gani a jikinta, wani irin kuka Saif ya fashe da shi ya na sake jijjigata "Malak Malak, no no no no Malak don allah ki tashi." Amma koh motsi bata yi ba.

Wani irin kuka Saif ya sake saki "Plss malak pls malak ka da ki yi min haka, don allah ki ta shi, wannan karon ka da ki mutu ki tashi,  ki nuna musu duk abun da zasu yi ba su isa su ɗauki ranki ba, plsss show them u can survive anything da suka yi miki plssssss ka da ki mutu wannan karonnnnn. " ya faɗa ya na wani irin kuka kamar zai mutu wani irin ciwo da raɗaɗi yake ji, sai addu'a yake yi allah ya sa wannan mafarki ne coz he can't even imagine his life with out malak.

Durƙusawa ya yi bakin gadon ya na riƙe da hannunta "Kin ce....kin ce ki na son mu yi abubuwa da yawa,  u said u wanted lot of children, u said we'd go to different countries,  we will travel around the world, and......and u said u want a closet full of all those flashy colors, u said you'd make shopping a part of ur every day routine, and now zaki tafi ki bar ni we didn't even do all that babu wanda muka yi, babu and u even said idan na yi miki kishiya zaki karya kafafuna ta yanda ke kaɗai zaki iya zama da ni, plsss ki tashi na yarda ki karya kafafun nawa in dai zaki dawo don allah Malak ka da ki yi min haka don Allah."

Ya ce ya na sake riƙe hannunta da kyau, kawai ji kake Beeb cardiac monitor dinta ta yi ƙara and da sauri Saif ya ɗago ya na kallon face ɗinta, wasu hawayen suka zubo gefen fuskarta and take monitor ɗin ta cigaba da ƙara Beeb Beeb Beeb layukan da suka yi flat suka koma wavy, da sauri El bashir ya ce "She is alive." Kawai sauran likitocin suka karaso aka mai da mata da oxygen ɗinta suka shiga dubata, wani irin murmushi saif ya saki cikin kuka ya ce "I know ba zaki tafi ki barni ba." Kawai ya sulale wajen ya faɗi, ya suma.

Sai da aka ga ta dawo dai dai sannan suka yi kanshi, wanda shi shock ne na abun da ya faru da kuma stress da ma rashin baccin da baya samu kwanan shi ya saka ya suma, sannan blood pressure É—insa ya hau sosai don haka allurorin bacci aka yi masa wanda ya yini ya na bacci aranar.

Ita ma naila ta farka tun ma lokacin da malak ɗin ta dawo ita ma ta farka, sai dai yanzu kam an sakata a bed rest dama she yakamata ta yi amma taƙi ji saboda yar uwarta, sai da ma aka ɗaura mata ruwa.

Bayan sati ɗaya Malak ta yi improving sosai don yanzu ancire mata oxygen da ma wasu mechines ɗin yanzu da kanta take numfashi, ana bata best kulawa da ya kamata, zuwa yanzu Haddad's da ma kowa ya san cewa ita ɗin ita ce Captain Malak Abdullah, sannan ana nan ana bincike akan waƴan da suka yi mata haka da kuma waƴanda ke neman  rayuwar ta.

Gefen Haddad's kuwa koh don kulawar da aka ga El Bashir na bama Naila da ma Æ´ar uwarta Malak sun yarda cewar lallai Æ´aÆ´ansa ne sai dai babu wanda ya san a ina ya samo yaÆ´an wannan shi da kanshi shi zai yi bayani.

In da su Naila ɗin ma sun dawo Haddad's da zama a gidan su saif suke in da aka gyara musu part ɗin baƙi anan suke zama, wanda El Bashir ne ya yi ma saif magana saboda bai so ya kawo su Taj ɗin gidan sa, saboda wannan cin fuska ne ga Ummu Rumana wato matarsa, shi Taj ɗin ma ya so ya ƙi har sai da su kareem da su Ummi suka saka baki tunda dai yanzu shi ma ya zama Haddad ɗin tun da matar shi Haddad ce, daga Mrs Tajuddeen Abad ta koma Ameenatu El Bashir Haddad,  a yanzu sunanta ya cika complete.

Ummu Rumana kuwa duk abun da ake yi ta zuba ido ta ga in da zai tsaya, dama bata da wani problem don kuwa duk cikin matan Haddad ta fisu kirki da son mutane da ma halin ƙwarai wanda daga ita sai Ummi, ta na jin ciwon abun da ake yi but ta yi shuru ta yi haƙuri ta san mijinta sosai kuma she trust him.

Har yanzu asibitin na nan cike da sojoji don kuwa har yanzu akwai masoyan malak ɗin duk da ta ɗauko shekaru da dama babu wanda ya ji labarinta don kuwa cewa aka yi ta mutu kusan shekaru masu yawa kenan yanzu,  so har yanzu akwai masu jira ta farka, abokanan aikinta, senior colleagues dinta juniors ɗinta, da students ɗinda ta koyar kafin ta shiga cikin shadow five, da ma mutanen da ta taimaka, they are all waiting for her to wake up ana nan ana yi mata addu'a.

Hmm my people labarin Malak Abdullah is a legendary labari, wallahi ka da ku bari a wuce ku.

Meemziey's pen

Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

Page _______3️⃣6️⃣

Su naila yanzu sun ɗan fara sabawa da mutanen haddad ɗin duk da ba sosai ba saboda duk yawanci zaman su a asibiti ne sai dai kam ta na shiri sosai da ƙanwar saif ɗin wato Khairi mugun shiri suke yi sosai da sosai, gefe daya kuma suna nan suna jinya ƴar uwarta wanda an cire mata life support da duk wani na'ura da kanta take numfashi,  anan haka wata rana kwatsam sai gashi ta farka sun yi murna sosai dai dai murnar ta koma ciki saboda ita malak ɗin bata tuna komai ko da sunan ta ne ta samu memory loss, ta manta da mijinta saif da ma komai ta dawo kamar sabon mutun.

Naila ta yi kuka sosai na jin malak ɗin ta manta memories ɗinta wanda gefe daya kuma ta ji dadi saboda malak ɗin ba zata tuna abubuwa marasa kyau da suka faru da ita a baya ba, saboda ta na da wasu irin painful memories masu ciwo wanda har yau bata yi ma mutuwar iyayen riƙonta kuka ba, don duk lokacin da ta tuna da mutuwar kafin ta kaiga yin kukan ta sake samun memory loss saboda ba yau bane karo na farko da take manta komai akanta.

Brain ɗinta ya riga da ya yi weak da abu kaɗan ke saka ta manta komai, the brain is exhausted, so Haddad's din basu yi kokarin tuna mata da wayan nan memories ba sai suka shiga kokarin gina mata sabbin happy memories wanda suke bata wata irin kulawa me kyau sosai da sosai, kullum cikin kawo mata gifts ake yi da sauran su,  ana nuna mata kulawa har ta Innalillahi don kuwa dakin nata na asibiti da yake an maida ita normal room, an yi masa paint pink aka jera mata wasu pink teddies, hatta da hospital gown ɗinta pink aka mai da su da ma slippers ɗinta kowa na nuna mata so saboda malak ɗin ta wahala iya wahala.

sannan wani irin mugun shiri suke yi da Naila wacce ita ma take bama yar uwar tata kulawa fiyeda tsammani ta karanci brain ta san abun da brain yake buƙata especially irin na malak, happiness farin ciki shi ne abun da malak din take bukata and she is willing to give her it.

Gefen El Bashir wato mahaifin su naila din shi ma ya na bama yayan shi kulawa sosai especially É—ayar can wanda yana da hannu wajen lalata rayuwarta da ma duka farincikin da ta rasa.

Gefen manyan Haddad kuwa ganin malak ta ji sauƙi lokacin ne aka turke El Bashir,  duka manyan suna nan, hadda matan su su ammi ummi da ummu rumana, da kuma saif Taj sai naila, sai Khair ba da Malak ba saboda case ne za'a yi ana so ta sama happy memories kawai ba'a son abun da ya taɓa ta, tun da brain din dai haka haka take.

So shi dai El Bashir tun lokacin ana samari dai ba'a jin magana, saboda lokacin anan ji da ƙuruciya da kuma kuɗi an taso cikin ahalin da akwai arziƙi, har ya zo ya Ummu rumana suka haifi ɗa wato Jamal duk kanshi na ɗan rawa haka bai natsu ba.

Wani abokinsa kamar family friend haka ya haɗa musu party a gidan su saboda shi ma abokin gidan su suna da kuɗi, so iyayen abokin basu nan aka hada party maza da mata suka yi shaye shaye ya bugu ya kwana da mai aikin gidan, mahaifiyar su Malak kenan ana ce mata umaima,  shi bai ma santa ba bai taɓa ganin face ɗinta ba, kuma ba zai iya tuna ta ba saboda abuge ya yi abun, ba ma zai ce kwana da ita ya yi ba coz bata bashi kanta ba its a rape.

Kuma koda safiya ta waye bai ganta ba, da haka ya dawo gida sai abun ya yi ta damunshi a rai, hadda tambayar abokin shi ya yi ina mai aikinsu ya ce ta bar aiki a gidan nan kuma shi daga lokacin bai sake bi ta kanta ba duka da abun na yawan faÉ—o masa akai akai.

Kuma tun da ga ranar ya ajiye duk wata É—abi'ar banza da yake yi bai sake yi ba.
Chapter 68 · 0% Book details