← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 71

Sashe 13

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rike ƙugu ta yi "Eh mana." Matsowa ya yi kusa " ki na tunanin kawai...." Katse shi ta yi "Kai fah ka daki mota ta, so ka dena ɗaga murya." Tsayawa ya yi kawai ya na kallonta, babu tsoro a idonta, ita fah ta yi laifi amma ta maida abun kanshi, "Baki san waye kika ɓatawa lokaci ba, some of us don't have time for ur nonsense. "

'And u don't know what am dealing with either, so don't project ur anger on me." "After all ba na da lokacin ka." Ta ce ta na juyawa zuwa in da motar ta take, shi ma komawa ya yi cikin motar shi ya ta da ya bar wajen, Sai dai basu sani ba waje É—aya suka nufa.

Ta na isa asibiti ta janyo labcoat ɗinta ta fito daga mota ta nufi ICU ta na zuwa koh ta iske ya farka, ya na magana amma bata fita nan ta shiga duba shi, sai kallonta yaron yake yi duk in da tabi, bayan ta ƙare duba shi ta fito, dai dai ya na ƙarasowa wajen, dakatawa suka yi suka na yi ma juna kallon kallo "You!" Ya ce ya na nunata da mamaki "Me kika zo yi nan?"

Taɓe baki ta yi ta na gyara labcoat ɗinta da kyau, don ya ga sunan da aka rubuta gaban labcoat ɗin "Dr Ameenatu.... Consultant Neurologist. " Ya karanta sunan dake kan labcoat ɗin zai yi magana daidai MD na asibitin na shigowa wajen, da sauri cikin respect ta ce "Barka da zuwa sir." Jinjina kai ya yi "Yawwa Dr Ameenatu. " "Na'am sir." Sai kuma ya juya suka gaisa da mutumin "Ah ah Mr TAJUDDEEN Barka da zuwa an iso lagiya?" Cewar MD "Alhamdulillah. " Ya ce a taƙaice.

Kallon Naila MD ya yi "Mr Tajudden ga likitar yaron ka nan Dr Ameenatu ita ce in charge na case ɗinsa, Surgeon." "Barka dai sir." Ta ce da Tajuddeen ɗin cikin murmushin yaƙe ta na hararanshi ba tare da ta bari MD ya gani ba, sannan ta ce da MD "Sir zan tafi in duba wasu patients. " "Ok Dr Ameenatu. " Daga haka ta wuce su kuma su Taj ɗin suka nufi cikin ICU ɗin.

Wucewa suka yi ciki Ayan na ganin babanshi ya washe baki, gaida su Mom ya yi sannan ya karasa in da Ayan yake, ya ja kujera ya zauna, ya na kama hannun Ayan ya shiga yi mishi magana, Ayan sai daÉ—i yake ji ya na yi ta murmurshi.

Shi kuma Tajudden sai wasa yake yi ma Ayan ɗin, he thought ya rasa Ayan ɗin don tun da labarin abun da ya faru ya kai masa bai sake samun bacci ba, ya na so ya bi private jet sai dai baya so labarin dawowar shi ƙasar ya watsu so dole normal flight ya biyo ko da ya iso dare ya yi, key ɗin mota kawai ya amsa daga security ya nufi hanyar asibitin sai dai kafin ya isa ya yi karo da motar wani, cikin wani irin fushi ya fito gashi ya na sauri ga shi an ɓata masa lokaci.

He expected someone maybe namiji but he saw her, too small, too tiny and at first she was talking calmly for someone who had just endangered lives on a public road, and the worse of it is she talked back at him, the audacity annoy him more than anything.

Idan mutane suka haÉ—u da fushin sa komai taurin kan mutun sai ya sara masa, but ita bata ma damu ba, like she had nothing to lose, and that is why, that is why ya tsani Nigeria, and daga karshe ma tafiya ta yi ta bar shi a tsaye, ya zaci ba zai sake ganin ta ba shi kenan ba zai sake haÉ—uwa da ita ba, amma me?

Ya na shiga ICU da ita ya fara cin karo, and maganar da MD ya faɗa masa "Ita ce in charge na case ɗin yaron ka.." abun da ya ƙona masa rai more than anything, ita wacce ya gani a hanya, yanzu ga ta tsaye a gabansa sanye cikin farar labcoat wacce ta yi fitting ɗinta kamar don ita kaɗai aka yi coat ɗin, da sunanta rubuce a coat ɗin.

Consultant Neurologist.

Ƴar ƙanƙanuwa da ita too young, wannan ita ce wacce ta buɗe kan yaron sa, ta buɗe ƙwaƙwalwar yaronsa, Nah he reject it, absolute rejection.

Bai yarda da Doctors É—in Nigeria ba.
He trusted systems, protocols, peer reviewed data.
Not instincts, not conference without pedigree .

And she looked unserious, ba daga É—abi'un ta ba daga shekarunta.

Ya ɗauke idonsa daga kallonta coz she irritates him, sai ya ji MD ya kuma cewa "Ita ta ta jagoranci case ɗin lokacin da sauran suka ƙi." Sauran ya maimaita, sai kuma ya sake kallonta, bata yi ƙoƙarin burgeshi ba lokacin da MD ya ce hakan, ko kuma ta yi bayanin kanta, ko ta yi defending decision ɗinta, sai ma excusing kanta da ta yi ta kama harakan gabanta, ya na kallonta lokacin da MD ya yi introducing ɗinta hadda harararshi.

Bayan ya shigo ICU É—in kuma Taslim Kanwar shi ta shiga yi masa bayanin abun da ya faru lokacin da aka kawo Ayan É—in asibiti, sai da aka kirata ta na gida, ta zo ta yi masa surgery bayan cecekucen da aka yi.

Shi dai bai sani ba, but bata yi masa ba koh kaÉ—an.

Ita kuma Naila ta ma mance da rayuwarshi ta na can ta na duba sauran patient É—inta, daga nan kuma ta koma gida, washegari da ta zo sai da ta gama duba duka patient É—inta sannan ta zo wajen Ayan, lokacin an maida su normal Amenity, ta na shiga Ayan ya yi ta kallonta, sai murmushi yake yi da alama ya ji daÉ—in zuwan ta, duk ta É—ago sai ta ga ya na kallonta ya na murmushi, ga ta ita bata ma iya irin murmushin nan na Munafunci ba, ashe wai tun da safe yake tambayar nurses dake wajen ina take ina take, ya na ta damunsu.

Meemziey's pen
[04/10, 14:29] Amina Khaleel: Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

page______1️⃣0️⃣

Wasa wasa sai yaron ya zama attached to her, wani lokacin ma baya cin abinci koh shan magani dai in ta na nan idan kuma aka matsa mishi ya saka kuka, Tajudden da su Mami su na ganin kamar wasa sai, sai fah abun ya zama da gaske don idan bata kusa sai an kirata, ta yi mishi magana yake cin abinci koh shan magani, ga shi da naci da yake ya fara jin sauƙi in ta zo duba shi ya yi ta yi mata surutu.

Akwai ranar da ya ce mata me yasa bata murmushi kuma gata very pretty ta na da kyau amma bata murmushi, Hadda ce mata Daga yau Dr Pretty zai kama kiranta, abun da ya sakata murmushi kenan har dimple É—inta ya lotsa, ya tsaya ya na kallonta kamar wata sabuwar halitta, duk abun da suke yi Taj na kallonsu, haushi kamar ta kashe shi ganin yanda gabaÉ—aya yaron ya zama attached to her.

And tun daga ranar da an yi abu É—aya biyu Dr Pretty, har wani nishaÉ—i yake ji in ta na nan, ga shi bata so ta zama attached to him saboda su na da kuÉ—i ka da aga kamar don kuÉ—in take yi.

A kwai ranar da ta zo ta iske shi ya na ta kuka wai an aske masa gashin kansa duk ya yi muni, ranar sai da ya bata daria, da ƙyar ta iya lallaɓashi akan ya yi shuru, washegari ko da ta zo, ta ɗora wig akan ta saman rolling ɗin da ta yi, ba normal wig ba ne irin wig ɗin nan ne na joker mai kala kala ɗin nan, ta cire wig din ta saka mishi akai ta ce duk lokacin da ya ji he feels ugly ya saka wig ɗin duk da shi ɗin ba marar kyau ba ne, sai jin daɗi kuwa yake yi ta yi.

Tajudden ya na ganin su ya na kallon duk abun da yake faruwa wanda ya san nan gaba matsala za'a samu.

Yau wata Ayan ɗaya da kwana biyu a asibiti, tsaye take cikin ɗakin bayan ta cire masa cannula da sauran su don kuwa sallamar su za ta yi yau tun da ha ni sauki, about 8 days kenen bai sami post op Seizure ba, kuma vital ɗinsa are stable, sai dai za'a na kama dawowa da shi for check up don shi kam yanzu ya na buƙatar long life monitoring.

Bayan ta gama komai ta durƙusa gefen gadon da Ayan yake wanda ya yi zaune ya yi shuru jikinshi duk ya yi sanyi "Cry Cry Baby, Yau za'a je gida koh?" Ta ce ta na murmushi, bai yi murmushi ba kamar yanda ya saba, sai rawa da bakinsa ya soma yi ya ce "Aa." Tare da maƙe kafaɗah, kallonshi ta yi "Me yasa, don't u want to go home and play, and sleep on ur big bed, the one da kake bani labari."

Kama hannunta ya yi ya riƙe "Ni ba zan je ba, anan bake so in tsaya tare da ke." "Tau wata sabuwa in ji ƴan caca." Ta faɗa acikin zuciyarta, shuru ɗakin ya ɗauka su Mami su na gefe suna kallonsu, Nurse ɗin da suke tare da ita kuwa dama fita take shirin yi amma sai ta dawo ta ji kwakwaf.

Ganin É—akin ya yi shuru awkwardly ya sa ta ce "No ka da ka damu, i will still be ur doctor, za'a kawo ka check up zaka ganni ok." Girgiza kanshi ya yi hawaye suka zubo a kumatun shi ya ce "A'a ai ba kullum zan kama ganinki ba." Sai kuma ya rufe kunnesa "Ni ba zan ji duk wani abun da zaki ce ba, ni anan zan zauna tare dake."
Chapter 13 · 0% Book details