← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 71

Sashe 66

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu sirarun hawaye ne suka fara zubowa ta gefen idonta sannan a hankali ta soma buɗe idonta ɗan rufewa ta yi saboda hasken da ya yi mata yawa, sai kuma ta sake buɗewa har ta yi adjusting, ta sake buɗe su gabaɗaya kallon ɗakin take yi kafin a hankali ta juyarda kanta in da ta ji kamar an riƙe mata hannu idanunta ne suka sauka kan Taj ya ɗora kanshi a gefen gadon ya na bacci hankali kwance.

Sosai ta zuba mishi ido ta na jin wani son shi na ratsata, a hankali ta buÉ—e bakinta da ya yi mata nauyi ta ce "Taj." Kamar acikin mafarki haka ya ji ta kira sunanshi, buÉ—e idonshi ya yi a hankali aikuwa suka haÉ—a ido, da sauri ya tashi zaune, "Naila kin farka." Gyada hai ta yi a hankali kafin ta ce "Taj ina Æ´an biyu na?." Shuru taj ya yi ya na kallonta, hakan ya saka gabanta faÉ—uwa hawaye na taruwa a idonta ta ce "Ka da ka ce min ta mutu don zuciya ta ba zata É—auka ba." Ta faÉ—a a hankali saboda yanda zuciyarta ta yi mata nauyi ga kuma ciwo da take yi mata.

Ta yi mafarki, mafarki mai tsawo, sai yanzu ta gane wannan mafarkin da take yi, takan yi mafarkin lokaci zuwa lokaci, na wata mai irin fuskarta sak, ta na sanye da kayan sojoji, Æ´ar uwarta ce, da takan yi mamaki yaya aka yi take mafarki ta na sanye da kayan sojoji, ta yi mafarkin ba sau É—aya ba, ba sau biyu ba, ba sau uku ba, sau ba adadi, ashe Æ´ar uwarta ce take gani a mafarki, ko ba da mafarkin ba, da ta na kwance ta na jin taj lokacin da yake faÉ—a mata malak É—in yan biyunta ce, da yake in mutun na unconscious ya na jin abubuwan da suka faruwa a wajen kawai bai iya motsi ne da magana amma ya na jin komai, sannan kukan da take yi, emotional attack da take samu ba emotions dinta bane na Æ´ar uwarta ne, sai yanzu ta kamo bakin zaren, saboda koh ita yarinyar (malak) bata yi kuka ba duk da ta na cikin pain.

Ita ita ke yin kuka duk lokacin da wannan yarinyar take cikin pain,  bata taɓa jin haka ba koh a tarihi, ko azamanta na likita ta san kowa da na da nasa emotion, ta san kowa emotion ɗinsa yake ji, bata taɓa jin in da aka ce wani na jin emotion din wani ba koh da ƴan biyu na, amma su what's so special about them bata sani ba, menene connection dake tsakanin su da har suke jin emotion ɗin juna duk da basu kusa da juna duk da basu san da existence ɗin juna ba.

Ganin idanunta sun tara hawaye Taj ya yi saurin cewa "Bata mutu ba ta na raye." "Ina take ka kai ni wajenta don allah." Ta fada hawayen na ƙarasa saukowa daga idon ta, shuru Taj ya yi don ya san tun da ta ce zata je toh sai ta je, a hankali ya taimaka mata ta sauko jikinta babu karfi sosai, slippers dake bakin bed ɗin da aka tanadar ma marar lafiya ya saka mata, ya na tattare mata gashinta ya saka mata hula sannan ya dora mata karamin mayafi akai, saboda ta na sanye ne da riga da wando masu taushi na asibitin wanda aka tana da specially for only Haddad's ɗin but da yake baƙin su saif ne sannnan saif ne ya bada umarni akawo su nan so kowa ɗaukar haddad yake yi musu ana basu wani irin special care.

Nurses din na kula da ita sosai, don jiya sai da aka gyara mata jiki yau ma haka, sannan aka canza mata wasu kayan..

Kamata ya yi a hankali take tafiya saboda mararta dake yi mata ciwo amma saboda ta na son ganin Æ´ar uwarta dole ta daure, duk da ayanzu ba fuska É—aya bane da su, amma ta na jin wani irin special connection akan yarinyar, har cikin zuciya take jinta.

A hankali suka shiga ICU ward ɗin wanda suna shigowa duk sojojin dake wajen ita suke kallo da wani kalan mamaki da kuma al'ajabi suke kallon ta, saboda wannan ai fuskar Captain malak suke gani, basu daina kallon su ba har sai da suka iso wajen, da yake ba kowa ake bari ya na shiga ba, a bakin wajen ta tsaya ta na kalon malak ta cikin glass ɗin wajen,  wacce take kwance ta yi pale sosai ga monitors nan laƙe ajikinta.

Wani kalan kuka ta fashe da shi ta na dafe glass din wajen ta na cewa "Me ya sa? Me ya sa kika baki zaɓi shiga wannan halin ba sai da na zo nan, me ya sa me ya sa tun farko zaki tare min bullet ɗin, shin ke, shin ke haka kike kina tare ma mutanen da baki sani ba bullet? Ban sanki ba baki sanni ba me ya sa kika zabi ki shiga gabana, shin ka haka kike kina saka rayuwarki cikin hadari saboda wasu, ni, ni bana da rayuwar nan, kai na kawai na sani, inni ce bazan taɓa shiga gaban ki ba, haddai da ban sanki, don allah ka da ki tafi ki barni, baki san ciwon da nake ji ba."

Tafaɗa ta na dafe zuciyar ta, ko da El Bashir wato mahaifinta ya karaso wajen ya isketa hakanan shuru ya yi ya na jin wani abun saboda ba zai iya rarrashin ta ba, they are not that close hasali ma bai daɗe da sanin ita din yar shi bace, numfashi ya sauke ya zo zai shiga ɗakin ya na sanye da sterile clothes da ake sakawa idan za'a shi ga ICU da sauri naila ta isa wajen shi ta na kama hannunshi,  "Don allah ka bari in shiga nima in ganta don allah."

Ta ce hawaye na sauke daga idonta ita bata ma san me take yi ba she is not normally like this ba ƙaramin abu bane ke sakata kuka ba, kowa ya san da haka, sannan bata da tsoro koh shakka, wanda shi ne farkon abun da ya ja Taj a gareta, rashin tsoron ta ne ya saka ta auri taj ɗin, amma ba ko wacce mace ce ba zata iya auren Taj, a hankali El Bashir ya juyo ya kalleta zai yi magana ta yi saurin cewa "Don allah Abbieh. "

Wani irin sanyi ne ya ratsa jikinshi jin sunan da ta kira shi da shi, bai taɓa zaton zata kira shi da wannan sunan ba nan kusa kila don bata san halin shi bane shi ya sa, amma ya san koh mutuwa zai yi malak ba zata taɓa kiran sa da Abbieh ba saboda abun da ya yi mata.

A hankali ya daga hannun sa kamar mai jin tsoro ya shafa kanta, "toh ki bari in fito sai ki shiga kinji." Wani irin kallon shi take yi ta na jin wani iri yanda ya yi mata magana ahankali cikin rarrashi abunda kawu usman bai taɓa yi mata ba tun ta na karama sai ma da ta yi kuɗi sannan yake ɗan rarrashinta, yau mahaifinta ya yi mata, sai ta ji ta kasa musa masa ta gyaɗa kanta "Toh Abbieh amma ka da ka dade." Jinjina kai ya yi "Ba zan daɗe ba." Daga haka ya buɗe wajen ya shiga ya rufo, duba ta ya shiga yi ya ga komai normal.

Kamar yanda ya ce ma naila bai daÉ—e ba ya fito ita ma aka bata kayan ta saka sannan ta shiga.

Meemziey's pen

Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

Page _________3️⃣5️⃣

A hankali take takawa har ya ƙarasa bakin gadon da Malak ke kwance tsaye ta yi ta na kallonta idanunta na sake cikowa da hawaye, kafin a hankali ta ja kujera ta zauna a bakin gadon sannan kamar mai jin tsoro ta kama hannun malak ɗin acikin nata ta matse, kuka na kwace mata, duƙar da kai ta yi still ta na riƙe da hannun malak kafin ta ɗago kai ta kalli face ɗin malak ɗin, "Hi." Ta faɗa a hankali, "As a doctor i know ki na ji na, amma as ur twin sister i don't really know idan kina ji na coz am scared but i hope ki na jina ɗin." Ta faɗa sai kuma ta saka bayan hannunta ta share hawayenta.

"Sunana Aminatu El Bashir,  amma an fi sani na da Naila, ko kuma Dr Naila, ni likita ce, A Neurologist/Neurosurgeon,  na ta so ne a hannun kawuna, ko kuma in ce kawun mu, ƙanin mahaifiyar mu kenan, mahaifiyar mu ta rasu tun ina karama, so kawu ya raine ni, nan dai ta cigaba da faɗar abubuwa na rayuwarta, sai dai ta cire abubuwa da yawa saboda a halin da malak ɗin ke ciki labarin farin ciki ya kamata a bata, so sai ta zaɓi wasu tabata .

A bayan ta ƙare bada labarin ne ta ce, "Na san kina ji na saboda haka ina roƙon ki don allah ki tashi ki farka, wallahi ina buķatar ki a rayuwata I need u so much in my life, kin ji kin ji ƴar uwata." Ta faɗa ta na matse hannunta kaɗan, ɗan motsi hannunwa malak ɗin suka yi hakan ya saka naila kallon fuskar ta, wani murmushi  ta saki cikin kukan da take yi "Na san kin ji ni, saboda haka ki farka kin ji ina nan ina jiranki, i will never get tired. " Tafaɗa ta na sake sakin murmushi hawaye na fita daga idonta.

Sannan ta ce "Zan tafi sai na dawo kinji." Ta faɗa ta na sakin hannun malak ɗin ta miƙe har ta kai ƙofa ta juyo ta kalli malak ɗin sannan ta fice, ta na fita taj ya kama hannunta suka koma ɗaki saboda yanda sojojin dake wajen ke kallon Naila ɗin, lallai naila da malak su na da kama sosai, ada, sai dai yanzu Malak ɗin ta yi surgery ta canza fuskarta, so idan sojojin suka ganta sai su yi ta mamakin ya aka yi take da irin fuskar malak tun da dai basu san malak ɗin na da ƴar uwa ba.
Chapter 66 · 0% Book details