← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 102

Sashe 92

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aunty salma ta kalli umma wacce  har lokacin kwayar idanunta  na kanta cike da tarin 'bacin rai sannan ta waiga inda baba gali da aunty hasana suke tsaye suma cike da mamakin umma .aunty salma ta daure zuciyarta da maganar umma tace "irin fatan da zaki mana kenan ?"irin fatan dai da  kukewa  kanku kenan." da sauri umma ta bata amsa da haka sannan tana cigaba da cewa  " maza ku fice min daga parlour bana son ganinku  kuma wannan ya zamo karo na farko dana qarshe da zaku  shigo inda nike kuyi lamarinku nayi nawa bana son ganin gaba d'ayanku a inda nake kowa ya zauna inda allah ya ajiyesa ."saboda an ta'ba miki yar so zaki fad'a mana haka ? Inji cewar aunty hasana "kwarai kuwa zan ma iya yin abinda yafi haka matuqar akan maryama ne aunty hasana ta numfasa kana tace "idan bake ba aunty ai murna zakiyi da abinda ake wa yarinyar nan yarinyar da ta zama silar rasa tilon d'anki  "sadam dai d'ana ne dana   haifa da cikina  duk kuma  wanda rashinsa zai wa ciwo a bayana yake to na barwa Allah kada wanda ya sake dawo min da hannun agogo baya kuje na sallameku bana son ganinku, yadda baku qaunar maryama nima wallahi a yanzu bana qaunarku daga yau na yanke duk wata halaka daku ." da sauri aunty salma ta qaraso ta durkushe gaban ummah ta rike qafafuwan umma da duka hannuwanta ta soma girgiza mata kai kamar wata kadangariya tana kuka tana bata hakuri "dan girman allah aunty kiyi hakuri  bazamu sake cewa komai akan lamarin mutuwar sadam da gadonsa ba ki yafe mu dan Allah wallahi sai yanzu nake jin nadamar abinda nayi in sha allahu bazan sake ba tabbas maryama tamkar diyarmu ce Allah ya huci zuciyarki wallahi bazamu sake ba ."

gwalalo idanu aunty hasana da baba gali sukai suna kallon  makirci irin na aunty salma ,sam basu ta'ba tunanin zata aikata haka ba "lallai ta cika babba makira ta qarshe "kiyi hakuri dan Allah aunty ta sake  fad'a tana mai sakar ma umma qafafun ta kamo hannunta numfashi umma ta sauke da karfi sannan ta samu waje ta zauna akan kujera tana runtse idanunta tare da dafe goshinta" sigina aunty salma tayiwa baba gali da aunty hassana alamun suma suce wani abu ai kuwa nan da nan suka matso kusa da umma suna mata magiya da ban hakuri "shikenan komai ya wuce allah ya yafe muna gabadaya amman dai kusani maryama bata cancanci haka daga gareku ba ,maryama a yanzu tafi bukatar kulawa da tausayawa da soyayya tattare da rarrashi daga gareku tun daga farkon rayuwarta baku qaunaceta ba wallahi kuji tsoron allah na rashin rike zumunci tsakani da Allah da kukayi ,wani abun mutane sunayi ne dan ganin ido wani dan zumunci zasu fake suci amana mussaman zumuncin wannan zamani amman ku babu wanda kukayi aciki kona ganin idon ma bakuyi ba bare bayan ido amman wallahi kusani zumunci a duniya wajibi ne duk kuma wanda bai yisa a duniya ba zai yisa a lahira alahirar ma acikin wutan jahannama ta fad'a tana jin wata irin natsuwa a cikin zuciyarta ".

"wannan tabbas haka ne allah ya shireyar damu gaba daya allah kuma ya bamu ikon sadar da zumunci dan allah ba dan kwadayin ko neman wata biyan bukata ba "baba gali ya fad'a yana mai  cike da nuna tausayawa ga maryama wacce hawaye biyu biyu ke bin kuncinta yace "diyata maryama Kiyi hakuri kinji in sha allahu kuka da damuwarki sunzo qarshe domin a yanzu a shirye nike dana baki duk wata kulawa da uba zai bawa diyar cikinsa ."da sauri maryama ta d'ago kwayar idanunta da suka jeme ta tsurawa baba gali cike da mamakin jin furucinsa  aunty salma  tayi tsigil tace "ki daina mamaki jin abinda babanki ya fad'a ,daa na shiga zuciyar mutun a ga abinda yake ciki da mun bude miki zukatanmu a yau kinga irin tarin nadamar da mukayi a yanzu babu wacce muke son gani cikin farinciki kamarki ki yafe mana duk da bamu dace da a yafe mana ba saboda abubuwan da muka dauki tsawon shekaru muna yi miki "in a slow voice maryama tace "babu aunty salma komai na wuce na yafe maku ." murmushin bakinciki suka sakar mata kafin ahankali suka shiga wata hirar allah sarki umma har ga allah ta hakura domin ta d'auka nadamar gasky sukai ,ta sake dasu sosai tayita masu nasiha kuma  duk akan zumunci ne bayan kamar mintuna shabiyar d'aya byn d'aya sukai wa umma sallama suka  fice suka bar umma da maryama .

"Umma nah !"
maryama ta kira sunanta cikin sanyin murya "na'am maryama kina bukatar wani abu ne ?bana bukatar komai umma ,ina dai jin dadi ne tare da godewa allah daya   bani ke amatsayin uwata kuma uwar mijina , ya  allah ka bani ikon kyautata ma umma nah   ,ya Allah ka bani ikon yi mata biyayya, ya Allah ka dawo mana da yaya sadam cikin koshin lafiya ka azurtamu da samun zuria masu albarka dashi ,ya Allah kasa mu kasance  har a aljannatul firdausi atare "ameen maryama ina alfahari dake, nima haka umma ina sonki "baki kai wa ni ba  maryama sonki ajinina  yake maryama, allah ya za'ba miki abinda yafi zama alkhairi arayuwarki,Allah ya bamu ikon cinye jarabawar mu ,ahankali suka dinga kwantarwa da zukantansu hankali har suka samu natsuwa sai dai da zarar ka d'aura idanunka akansu zaka fahimci zallar tashin hankali da damuwar da suke "ummah ina jin kauri "bari naje na duba ina ganin abincin da auntynki hasana ta daura ne yake kauri  ."a'a umma Kiyi zamanki bari naje"uhm uhm maryama  bana son kina damun kanki "a'a ummah nah sai dai muje tare ta fad'a tare da mikewa ta tsaya kusa da ummah, umma tayi murmushi a tare suka nufi hanyar kitchen."

*******

tsaye nuzlah take ajikin wondo d'akinta tana zubar da hawayen nadama  a yanzu damuwa tayiwa zuciyarta mummunar kamu  dan ko abinci bata ci tunaninta kaf ya tafi ne akan son sanin matsayinta a wajen yaya hisham ,shin zai aureta ne ko kuma zai zillewa aurenta ne ?kanta yayi mugun kullewa mafuta kawai take nema "idan har bai aureta ba tayi biyu babu kenan bata ga auren ata bata ga nashi auren idan kuwa haka ne ta cuci kanta da kanta tana cikin wannan halin ta  hango shigowar motar yaya hisham din cikin haraban estate dinsu da sauri ta  saki labalen ta qarasa gaban mirrow ta soma gyara fuskarta ta d'auki bakin mayafin abayar da take sanye dashi tayi rolling kanta ta feshe ilahirin jikinta da turare ta fito cikin sauri wanda alokacin har sun samu waje sunyi parking din motarsu sun fito suna taku yaya hisham na rike da jakar nana hauwa'u yayinda nana hauwa'u take takawa da kyar saboda cikinta ya tsufa ."da  sauri nuzla take daga kafafunwanta lokacin data qaraso daf dasu ta kira sunansa "yaya hisham!" cak suka tsaya a tare shi da nana hauwa'u sai dai ita bata juyo ba dan tasan muryar wacce  ,muryar nuzla a raunane tace "yaya hisham ina son muyi magana da kai "jin haka yasa nana hauwa'u ta  daidaita natsuwarta tare da danne zuciyarta da kishin mijinta ba dan komai ba sai dan ta qara kankaro wa kanta mutunci a idanunsa domin ba komai ake magana akai ba hakan yana zubar da martabar mace a idanun mijinta sai dai wani irin bugawa zuciyarta keyi da karfin gaske saboda tsananin kishin mijinta ."

ahankali ta cigaba da d'aka qafafuwanta domin basu dama  hakan yasa yaya hisham  ya juya bayansa  tare da zubawa nuzla ido yana kallonta a tsanake " duk ta rame ta d'ashe kamar wacce tayi shekara babu lafiya ko wacce babu jini ajikinta "idan na kiraka baka d'aga kirana yaya hisham laifin me nayi maka ?tayi maganar cike da rauni ,yayinda hawaye suka cika kwarnin idanunta" ban ta'ba expecting haka daga gareka ba well duk a ajiye wannan maganar ya batun aurenmu dan naga kamar yanzu ka fara canza raayinka akaina ?"Eh tô nuzla kamar haka ne dan a yanzu dai gsky bana jin wannan abu zai kasance a tsakaninmu "me yasa yaya hisham ?ta tambayesa  tana mai kamo hannunsa cikin tsananin tashin hankali "babu wani dalili kawai matata ta isheni daman can giyar soyayyarki ce ta hanani gane quality's dinta a yanzu kuma idanuna sun bud'e na fahimci duk duniya babu salahar mace kamar nana hauwa'u mace ce mai hakuri mai biyayya mai kyautatawa mai kawaici bazan iya had'ata da wata mace ba ita kad'ai ta isheni na qarasa rayuwata ,na godewa allah na godewa mahaifiyata da tayi silar da nana hauwa'u ta zamo mata agareni "dan girman allah yaya hisham kayi hakuri ka aureni nima zanyi maka duk abinda ka lissafa "bazaki iya ba nuzla bazaki iya hakurin da nana hauwa'u take dani ba "saboda me ?murmshin takaici yaya hisham yayi yana girgiza mata kai "kayi tunani akaina yaya hisham karka hukuntani akan laifin da nayi maka wallahi sharrin sheidan ne  ,ita soyayya fahimtar juna ne kuma tun farko bamu fahimci junanmu dake ba shiyasa muka samu matsala,ina sonki baki sona zuciyarki na kan wanina wanda ke a karon kanki Kinsan bazaki ta'ba samunsa  ba "yanzu nake qara jin wannan nadamar da dana sanin abubuwan da nayi maka dan girman allah kayi hakuri wallahi har da sharrin sheidan ".
Chapter 92 · 0% Book details