← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 102

Sashe 26

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana hauwa tabi bayansa da kallo tasan yayanta bai da kirki amman me zasu iya yi akai ?”yayyunta ma baya jin maganarsu bare ita da ko kusa da inda yake bata isa taje ba matsawar bashi ne ya bukata ba .”tana zaune yaya hisham ya fito da key din motarsa ya nufi kofar fita “ta mike da sauri tana cewa “ina zuwa kuma ?fita zanyi baka ci abinci ba fa?ya juyo ya tsaya tare da tsura mata ido kawai yana qare mata kallo batare da yace mata komai ba kafin daga baya yasa kai ya fice daga parlour’n ya barta tsaye cikin tashin hankali dan tasan wajen nuzla zashi zama tayi tare da zabga tagumi .”

*******

Tashin hankalin da ba'a sa masa rana wayewar gari yau din nan subaia suka tashi da mutuwar mahaifinta sosai suka shiga tashin hankali ita da kannenta wanda baki bazai fad'a ba tabbas rayuwarsu zata sake shiga cikin matsala babba yanzu saura abinda ya rage masu mahaifiyarsu ce itama kuma ba wani isashen lafiya gareta ba lallai suna cikin tsaka mai wuya basu da mataimaki sai allah shiyasa sunyi kuka kamar me maryama taje ta kuma ta tausaya mata matuka dan tana tausayin kanta amman idan ta tuna rayuwar subai'a sai taga gara ita akanta from rich to poor is not easy .”

a bayan can mahaifinsu mai arziki ne sai dai bai yiwa kanshi tanadin komai ba har zuwa lokacin da yayi accident ya samu matsala a bayanshi ."alokacin da yake tsaka da jinya sai yayi tunanin da zaman da yake na rashin sanin ranar warkewarsa mai zai hana bazai hada kwssamominsa da abokansa guda biyu ba tunda shi bazai iya komai ba su kuma daman ba wani samu suke ba kusan a karkashinsa suke samu alhj sani da alhj dan umma ,tofa tun daga wannan lokacin daya hadasu komai ya sauya agareshi domin kuwa babu abinda ya biyo baya sai danasani dan kuwa tunda suka fara samun kudi suka juya masa baya basuyi tunanin su taimaka masa ba.”

tun suna masa naci har yazo ya gagaresu sai rufin asiri allah mahaifinsu na cikin wannan halin mahaifiyarsa ta kamu da hawan jini ga diebites daman tana dashi , shekaru biyar yayi yana jinyar sai yau rai yayi halinsa aunty tazo da ummah zaune su subai da kanneta suke wajan gaisuwa amman da ka kalli fusk'okinsu kasan suna cikin rud'u da tashin hankali ."sai dai fatan samu sausauci daga Allah.”

Ranar asabar da misalin karfe tara na safiya bayan an shirya komai na bangaren umma tsaf yayinda aunty salma tayi duk wani shiri domin janye zuciyar yusif ta hanyar malaminta ya koma kan soyayyar daya daga cikin yayanta , kausar data gama gaisawa da umma ta fito neman maryama tana kwance acikin kalubalin rayuwa da yake zuwan mata lokaci lokaci ita gbdy ma data sanin girmanta take domin gara tana yarinya radadin rashin mahaifi ne kawai Ke damunta da kuma cin zarafin yan gidansu amman bata taba kwana da abinda Ke daga mata hankali har ya hanata runtsawa ba ."

Da gudu kausar ta fado kanta tana cewa masoyiya I miss you a lot duk da halin qunci da take ciki bai hanata nuna mata itama tayi farinciki da zuwanta ba "wallahi gidanmu kullum zanceki muke kowa mamaki yake wai yaya yusif yaga mace Kuma yana sonta har kuma ya kasa samun sukuni saboda ita tayi shiru kawai domin neman take ta daurawa zuciyarta damuwa acikin kahon zuciyarta domin dai ita tuni ta rufe babinsa da komai rayuwarta kawai take "dan Allah masoyiya ki tashi ki shirya yana parlour'n umma nasan ke kadai yake jira ."

Maganarta ta bata mamaki to idan haka ne ina batun baba gali da yace yusif din ya amince da auren shikura abbanau ya yarda da batun da baba yaje masa dashi maryama batayi nauyin baki ba kamar yadda ta saba tace “ai ina ganin Ke akwai abinda bakisani ba kausar ta kalleta cikin rashin fahimta tace "kamar me fa ?bayan tafiyarku baba yace sunyi magana da abbanku an maida wa yusif shukura amatsayina “kausar ta zaro ido tace "saboda ana hauka Ke waya ya fad'a miki wannna" baba !"

Sakina da shikura kuwa duk wani abinda ya Kamata aunty salma tayi masu wanda zasu jewa yusif dashi dan hK suka shirya cikin hadaddiyar kwaliya mai daukar hankali suka dauki abinda aka tanada domin shi suka nufi bangaren umma yana zaune jin tafiya yasashi fad'a da murmushinsa har wani mikewa yayi amman ganin sabanin abinda zuciyrsa Ke mararin gani ya dauke idanunshi daga kallonsu sukai sallama cikin siririyar murya tare da durkusawa suka ajiye mishi farati gabanshi suka zauna "ina kwana ya kuma hanya ?”ya dan kallesu "sannna ya tsaida kallonsa akan sakina yana cewa "kece sakina ?"

"Eh nice tayi mgnr tana sunkuyar da kanta "sannuku da kokari atare suka sakar masa wani kayataccen murmushi "me mukayi na Godiya batare da ya kalleta ba yace “ya cancanta na gode tunda kunyi aikin da baku ya kamata kuyi ba maryama ta baku wahala domin wannan aikinta ne tazo gareni da abinda zan saka abakina idan ma da hali ta ciyar dani” gbdy jikinsu yayi sanyi ta gyara zama "ai ya cancata muyi maka haka ya dan gyara zama sannna ya fuskancesu da wani iyayi da suke masa "akan me kenan ?sukai shiru hankalinsu ya soma tashi "tabbas wannan mutumin mai wuyar shaani ne idan da hali ma suce masa dan wulakanci, akace daya daga cikinmu zata iya maye gurbin maryama a wajenka ko baa fad’a maka bane .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 9

"Yusif ya d'an yi dariya kad'an sannan yace "saboda kuma kawai a garin mahaukata ake sai ku maye gurbinta? " maye  gurbin maryama ko mace' yar kasar england ce maryama  tafi gabanta awajena ." Jikin a sa'bule  suka d'an yi shiru daga bisani shukura tace "amma baka san cewar akwai wanda yake son maryama  ba har ma ana shirye shiryen kawo kudin auren ta?"wani mugun  harara yusif ya buga mata yana d'aga kafad'unsa alamun ko ajikinshi ."

Ta sake bud'e baki zatai magana a fusace yace,"Ku dan Allah ban son sakarci da iskanci banza ku ta shi kuje ku sanar da maryama dominta kawai  na zo gidan  nan ba dan wasu 'yan iska ba ,ta yi sauri tazo  ta samar da nutsuwa acikin raina ita kad'ai zuciyata Ke muradin son gani baku marasa kamun kai ba"

sakina da shikura sukai shiru  suna kallonsa tare da jinjina girman wulakancinsa, yayinda zuciyar shukura ke  qara lissafo mata abinda zata sake fad'a masa  amman  ta kasa domin tsoron amsar da yusif  din zai bata "lallai wannan ba wanda zasu zo suyiwa  wargi bane, dole sai mahaifiyarsu  ta sake shiri akanshi  atare suka tashi jikin babu kwari suka  fice daga d'akin cike da 'bacin rai ."

Aunty salma na zaune tana tunanin ya yusif zai kar'bi ya'yanta sai gasu sun shigo mata rai 'bace ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike tsaye da sauri cike da  fargaba duk da  dai bata da já akan aikin malaminta  tsayawa  tayi tana kallonsu  d'aya bayan d'aya  kafin daga baya tace "yana ga kun dawo min jiki a sanyaye .?"

"wallahi mama wannan mutumin mugun d'an wulakanci ne na bugawa a jarida nan shukura ta zayyane wa aunty salma komai daya faru cikin 'bacin rai sakina tace ,"ni dai gsky mama ki hakura ki barwa maryama yusif ta aura tunda ya nuna ita din dai yake so bashi da abinda zai yi damu  ita kuma shukura sai  ta auri malam yahuza " .bayan aunty salma ta gama jin abinda ya faru tas da abinda sakina ta fad'a tace "bazaa hakura abar mata shi ba  wannan auren muddin ina raye sai anyisa da d'aya daga cikinku ."

"to gsky mama ni dai banda ni sai dai ki aura masa shikura taje can su qarata dan bazan iya da wulakancinsa ba "na gode sosai yar'uwa dan dama zuciyata tana cikin d'ard'ar ne kar shirin mama yayi tasiri akanki gashi daman  dani yafi dacewa  tun dana d'aura kwayar idanuna akanshi na kamu da matsanancin  qaunarsa  "inji cewar shukura ".

"yauwa shukurata nasan bazaki ta'ba bani kunya ba daman kuma kamaninmu d'aya  "haka ne kuma dole halinku yazo d'aya ba" sakina ta fad'a acikin ranta sannan fili  tace "yar wahala sai kije kiyita fama amman kisani bazaki ta'ba daraja acikin idanunshi ba  karshe ma ki qarasa rayuwarki a wahala "tana gama fadar haka tasa  kai ta shige d'akinsu ta barsu tana jin babu dadi aranta duk da ahalin  yanzu babu  wani shakuwa da soyayya a tsakaninta da maryama  amman a wasu lokutan tana jin babu dadin abinda mahaifiyarta take mata ."

"Kece yar wahala daga nace ina son shi sai Kiyi min mummunar fata in sha allahu akanki zai qare "aunty salma taja hannun shukura  zuwa cikin d'akinta tana cewa "manta da sakina muyi abinda Ke gabanmu  "ta saki hannunta   ta qarasa gaban wasu kwanuka
ta bud'e d'aya daga ciki ta d'auko tandun kwalli ta mikawa shukura tana cewa "ungo nan shukurata maza ki shafa  wannan kwallin à idanunki" shukura ta kar'ba ta soma qoqarin shafawa yayinda aunty salma ta juya da sauri ta sake d'auko wani qaramin gwan gwani wanda Ke d'auke da wani bakin magani ta sake dawowa inda shukura take tsaye  ta miko mata hannunta d'aya tana cewa  "bani kwalli ki bani tafin hannunki idan yasan wata ai bai san wata ba zai san dani yake ".

Cike da farinciki shukura ta mika mata tandun kwallin sannan ta mika mata tafin hannunta kamar yadda ta buqata cikin sauri ta zuba mata bakin maganin  tana cewa "ki fad'i sunansa sau uku sannan ki fad'i  duk abinda kike son yayi miki idan kin isa gabansa ina mai tabbatar miki bazai sake  miki mutsu akan komai ba sai akan abinda kika fad'a masa zai yi aiki dashi kuma zai bi umarninki ."
Chapter 26 · 0% Book details