← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 102

Sashe 24

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani dogon tsaki yaja yana sauke hannuwansa ya rike kugunsa da hannu d'aya acikin ransa yace "wannan wace irin jaraba ce ?yarinya kamar mayya duk abinda zai mata bata damuwa ko ya zagi uwarta ya zagi ubanta duk a banza baya mata ciwo sai dai tayita bashi hakuri "ya fahimci mugun hakuri ne daita ,kuma shine dalilin da yasa mahaifiyarsa tayi masa sha'awar aurenta" tsaki yaja ya soma cire kayan jikinsa ya fad'a bathroom ya sakarwa kanshi ruwa ya fito ."

Bai sauya wasu kaya ba vest da boxcer kawai ya saka ya kwashi wayoyinsa guda biyu ya sauko zuwa parlour'n kasa ya zauna ,ya d'auki remut ya canza channel sannan ya d'auki wayarsa ya soma danne danne yana duba sakwani mutane ringing din waya ne ya karad'e parlour'n ya bar abinda yake yana yatsina fuska alamun qarar na damunsa ko ba’a fad'a masa ba yasan qarar wayarta ne ,can gefen kujera ya hango wayar yashe tsaki yaja , ya d'auke kanshi ya cigaba da abinda yake yayinda aka cigaba da kiran wayar ,qatar wayar ta dameshi sosai gashi kuma shi bazai ta'ba iya bud'e bakinsa ya kirata ba ."

cikin haka ta sauko ta shiga kitchen ta soma fito da abubuwan da zatayi amfani dashi na girki wayarta ce ta sake d'aukar qarar sauti ,ya tsaya cak ya bar abinda yake ransa na qara 'baci ,da d'an saurinta ta fito tana goge hannunta da towel ta soma duba inda wayar take ta d'auka taga sunan mahaifiyarta ce ke yawo a screen din wayar tayi shiru ta kasa d'auka a gabansa ,ta d'an d'ago ta kallesa taga ita yake kallo ta qasan idanunshi "nan take gabanta ya shiga fad'uwa "mummy ce "ta fad'a muryarta na rawa."

" yasan zaa rina dan zata fad'a masa ko wacece ta kira ,tsaki yaja "na tambayeki ne ?ya fad'a yana sake jan wani tsaki "naga kana kallona ne shiyasa nayi tunanin ko kana neman qarin bayani ne "akan me kenan zan bukata ?duk ma wanda zai kiraki ya kiraki mana menene matsalata da hakan ?kai kuwa kake da matsala dani tunda zamanka nake "ta fada tana tsura masa ido taji abinda zai sake fad’a ."bai sake cewa uffan ba yayi tmkr bai ji abinda tace ba ta juya ta koma kitchen ta kira layin mahaifiyarta tana aiki suna waya daita wanda duk hirar akan zaman aurenta ne ."

******

Da misalin karfe shida daidai hisham ya shigo gidan a gajiye  a parlour'n gidansa ya zauna  yana sauke numfashi nana hauwa'u dake zaune cikin  tsananin tashin hankalin abinda zai faru tsakanin maryam da yayanta tai masa sannu da zuwa babu yabo babu fallasa ya amsa yana furta "wash allah ! sannu ka gaji ko ?girarsa ya dage mata alamun “eh ! ko cikakken minti biyu bai yi da zama ba nana hauwa'u ta mike tsaye tana cewa “bari naje na kawo maka ruwa mai sanyi kasha ya juya "tafiyarta yabi da kallo ,yadda take jujjuya jikinta yana ta’basa.”

Daman kuma ba tun wannna lokacin ba yasan tana da kyawun jiki sosai fiyye da maryam dan tana da tsawo sosai , gyara zamansa yayi ya cigaba da kallo every step of her , .”ya runtse idanunshi sannu ga ruwa kasha da alamun ka gaji dayawa yau "ta fad'a tana miko masa cup ahankali ya bud’e idanunshi yana kallonta sannan ya karbi cup din hannunta alokacin da wayarsa ta fara ringing ,ya ajiye cup din ruwan akan table din gabansa ya ciro wayarsa a gaban aljihun rigarsa yana duba screen din wayar ."
ganin mai kiransa ya d'auka da sauri yana cewa "hello my dear "

Wani irin bugu qirjin nana hauwa’u yayi da karfi ko baa fad’a mata ba tasan ko wacece ta kirasa ta samu waje kusa dashi ta zauna tare da janyo kafafunsa ta d’aura akan cinyarta ta soma mammatsa masa “ no no!! your time is my time my time is your time am always with you,kowani lokaci naki ne karki damu am always with you my dear ai tunda nace miki zanzo zanzo  ne bari na dan watsawa jikina ruwa ,ko banzo yanzu ba zan shigo da daddare "tunda ya cigaba da wayar ta kasa cigaba da massaging din da takewa lafafunsa ta janyo wayarta tana neman layin maryam taji yadda suka qare da yayanta .”

Kira kusan biyar tayi mata bata d’aga ba yayinda hisham ya cigaba da wayarsa da nuzlah yana fad’a mata kalamai masu sanyi da sanya natsuwa wanda hakan yasa nana hauwa’u ta soma jin wani iri aranta zuciyarta ta dinga tafasa tana mata zafi  da ciwo ,nan da nan yanayinta ya sauya haka ma kwayar   idanunta ta cika da ruwan hawaye sai dai duk yadda taso ta danne amman sai da sheshekar kukanta ya bayyana "ta fara gajiya da wulakanci da yaya hisham yake mata, wallahi gara ya aro nuzla din su zauna tare da su taru su kasheta da bakincikinsu ."

runtse idanunta tayi gam tana zubar da hawaye tana sake zurfafa tunaninta " bata son ta sake masa magana akan nuzla tunda sun rigada sun gama mgn akanta sai dai duk da hakan bai kamata ta dinga d'aukar wulakanci har haka ba "wani bangare na zuciyarta ya fad'a mata haka ,ahankali ta girgiza kai sakamakon wankakkiyar zuciyarta dake bata shawara "kema ya kamata ki sake tuntubar mumy ta amince ya auri nuzla a wuce gurin ,ai kuwa gara ki tursasa mata ta amince da haka akan wannan wulakanci da suke miki, dan kuwa da zarar sunyi aure shikenan wasu abubuwa dole zasu ragu tana kallonsa ya sauke kafafunsa ya mike tsaye ya shige d’ayan parlour’nsu ."

ahankali ta dinga share hawayenta tana rarrashin kanta "meye dan ya wulakantaki ya kaskantar dake a karkashinsa fa kike ai wanda ya isa akewa haka dan allah nana hauwa'u ki sanyawa zuciyarki hakuri ki daina nuna damuwarki daman tare kika gansu dan haka ki kawar da idanunki akansu sosai ta bawa kanta hakuri kafin daga baya ta tashi ta nufi hanyar parlour’n daya shiga ta iskesa zaune yana cigaba da waya ta durkusa a gabansa muryarta a sanyaye ta kira sunansa "yaya hisham !bai amsa ba illa tsura mata ido da yayi yana kallonta "ban san me yasa ba amman ina jin kamar nayita kuka ina baka hakuri akan abinda nasan ba laifi nayi bane ."

" ina matukar tausayawa kaina a yanzu yayinda nake jin nadamar aurenka da nayi arayuwata ". jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karye da jin abinda ta fad'a sai dai ya nuna mata tamkar bai ji komai ba ya cigaba da wayar da yake ,ta kai hannunta taja dogon sajensa mai maseefar kyau da sheki tattare da d'aukar hankali ,da sauri ya ciza lips dinsa yana fadin "auchhhhh "tare da tsura mata ido sosai yana kallonta yana jin wani sauyi a gabad'aya ilahirin jikinsa ."Itama din tsura masa ido tayi tana masa murmushi wanda yafi kuka ciwo   tace "dan allah ka bar wayar nan haka."

Ya cire wayar a kunnesa yana cewa “a kan wani dalili kenan zan bar wayar ? " adalilin na baka dama ka auro nuzla ka had’amu “. wallahi a shirye nike da amsarta a matsayin abokiyar zamana ban hanaku aure ba bare hakan yasa ku zabi ku dinga  quntata min ."wallahi wallahi!! da nasan nuzla na sonka da bazanyi wasa da rayuwata ba ,hakika nayi mata laifi mai girma dana cancanci wannan hukunci daga gareta amman tayi hakuri ,na rokkeku ku yafe min ?"

nunfashi yaja ya sauke yana katse wayar gabad’aya ya ajiye a gefe ya rungume hannuwansa a qirji yana kallon kafafunsa dake sanye da safa"ku yafe min kuskuren shiga rayuwarku da nayi "sarai yaji ta amman ya shareta ya d'auki wayar ya soma danne danne ." ta kamo hannunsa d'aya cikin nata tana shafa saman tafin hannunsa ahankali ,dole ya tsaida duk wani abinda yake ya dawo da hankalinsa gareta qirjinta yabi da kallo babu abinda ta rasa kuma babu abinda nuzla tafita hasalima tafi nuzla dirin jiki mai kyau .”

Ya tsura mata ido sosai a kallon da yake mata bai san sanda ya zame hular kanta ba tulin gashinta dake d'aure ya kalla ahankali kuma yasa yatsunsa guda biyu ya zame ribbon din dake rike da gashin nan take gashin suka baje abayanta  bai tsaya wata wata ba ya fara shafa yalwataccen gashin kanta ."
Naunayen ajiyar zuciya ta sauke tace "ka auro nuzla wallahi zamu zauna lafiya da 'yaruwata idan kuma kana ganin bazaka iya had'ata dani ba ka sakeni ka aurota."sai lokacin ya d'an ja numfashi yace "bazan iya sakinki ba saboda mumy na matukar sonki sosai ba kuma zata yarda ba ".

zan fahimtar daita sannan zan bari ta yarda  zan fita arayuwarku gabad’aya , da dai ka dinga wahalar da abinda mumynka take so gara ka raba kanka daita gbdy ka huta dan .." wani qara ta saki mara sauti tare da yin shiru sakamakon yatsunsa biyu da yayi amfani dashi ya buge mata baki, ta kama bakinta dake mata zugi tana shagwabe masa fuska ."Kmr zatai kuka tace " da irin damuwar da kake kunsawa zuciyata gara ka sallameni ka bawa zuciyarka abinda take ..."shiiiii !mum wil kill me idan na sakeki ."

“Shikenan haka ni rayuwata zata qare agidan ka ?haka mumy ta tsara ,itama kuma ta tabbatar da hakan rayuwar zata qare kalamansa yasa ta zare hannunta dake cikin nashi ta mike tsaye da kyar dan kafafunta sun soma rikewa, ta juya da kyar zata bar wajen tana cewa " kayi shawara yaya hisham ni zan so rabuwar da kai ka bawa zuciyarka abinda take so karka ji komai ni zanji da mumy " hannunta ya fixgota da karfi ta juyi luuuu ta fado jikinsa ."Suka tsurawa juna ido suna exchanging din numfashi juna .”
Chapter 24 · 0% Book details