← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 102

Sashe 71

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana hauwa'u tace. “mami ina auntynmu take?”  nan da nan mami ta kallesa sai lokacin kanta ya kawo wuta “Ina Maryam ɗin da nace kazo min daita  Ko tana cikin mota ne?” ATA ya  ɗan sosa ƙeya “na barota a gida a cewarta  tayi baƙuwa”  da mamaki mami ta tsura masa ido “ka barota a gida adamcy acewarta tayi baƙuwa kuma?”eh !haka tace idan ta gama zata taho  don bazan iya zaman jiranta ba, kuma wallahi sweetheart kiyi ma yarinyar congret warning dan kwanakin nan  wasu ƴan iska qawayenta  take tara min a gida alhalin ni gidana ba dan ƴan iska na ginashi ba” cikin fushi mami tace. “adamcy  kasan me kake faɗa kuwa? Ƴar tawa da take aurenka zaka cewa Ƴar iska tana tara ƴan iska ?” “ai sweetheart wannan yarinyar ta wuce ƴar iska a gaban ita wanna Ƴar iska ƙawartata  take ce min wa..” hannu mami ta ɗaga  masa cikin fushi ta fara magana. “saurara! bana son jin komai daga bakinka, ka tashi yanzu ka koma gidan ka ɗaukota tun rai na bai gama ɓaci ba...” ATA  ya gyara zamansa  cikin damuwa yana kallonta kafin ahankali ya motsa laɓɓansa “haba sweetheart me yasa kike nuna mini wariyar launin fata a tsakanina da yarinyar nan ? Ni fa kika haifa ba ita ba” cikin fushi  tace.“dan  kana ɗan cikina sai in goyi bayan riƙon sakainar kashin da kake mata?” ATA yace. “To ai bata gama shiryawa bane tana hira da Ƴar iskar ƙawarta”

“Yanzu ka tashi   ka koma gidan  ka jirata har sai ta gama kimtsawa idan ma sai ta sallami ƙawarta ne ka jira sannan kuzo min tare yanda nace” mami bata kai ga rufe bakinta ba  Ni'ima  da maryam suka shigo cikin falon Ni'ima na riƙe da Maryam a kafaɗarta wanda goshinta yake a fashe yana ɗigar da jini, mayafinta da ɗankwalinta  yana a hannun Ni'ima nana hauwa'u ce ta fara lura dasu ta soma salati tare da faɗin.“lnnalilahi wa'inna ilaihir raji'un!”jinj !
Nan mami da sauran ƴaƴanta suka juya da sauri suka kalli maryam “Subhanallahi!” mami ta furta a ruɗe  tana  kallon ATA  “Adamcy kaga abinda ka janyo ko? don me ka barta a gida  Kashe min ƴa zakayi?”Adamcy  ya kalli mami a  natse ya juya ya kalli inda maryam take gbɗy ya kasa magana juwa ne ya ɗibi maryam ta sulale ƙasa a sume, nana hauwa'u ta ƙarasa da gudu suka tallafo ta ita da Ni'ima
mami da ƴaƴanta suka nufi wajenta da sauri suna jijigata jikin mami na rawa tace. “ku kwantar da ita akan kujera shahida taimaka ki duba min ita” duk mami ta ruɗe shi kuwa gogan ko ajikinsa dan haka nan yaji ajikinsa suman ƙarya tayi.Mami banzo da kayan aiki na ba, a kira doctor nasir” da sauri mami tace. “Auta maza shiga ɗakina ki ɗauko min wayata” da sauri nana hauwa'u ta nufi ɗakin mami ta ɗauko wayar tana niman layinsa yayinda aunty shahida ke bata taimakon gaugauwa shi kuwa ATA mikewa tsaye yayi yana jan tsaki ya ra’ba ta gefensu ya fice yama bar gidan gbdy .”

Bayan awa uku

Maryam na  zaune a kujera tana sauke numfashi ansa auduga da plasta an rufe raunin goshinta yayinda  mami ke zaune a gefenta riƙe da hannunta Dr.Nasir Ya miƙe tsaye sanye da coat da farin gilashi hannunsa riƙe da first-aid box ya miƙawa mami  Ƙaramar takardan magunguna   “hajiya ga wannan takardar magungunan da zatayi amfani dashi ne  insha Allah da zarar tasha a hankali ƙarfin jikinta zai dawo  baboda naga Allah ya taƙaita babu wani babban rauni da zai sa muyi admitting ɗinta  asibiti ko kuma yiwa cikin jikinta illa  Wannan treating ɗin ma da nayi mata is okay for her” mami ta jinjina kai tana faɗaɗa fuska cikin farinciki tace.  “doctor kace ciki gareta?”  Doctor Nasir yace. “ƙwarai kuwa hajiya in sha allahu ranar monday akawota hospital domin yi mata scan dan mu san iya adadin kwanakinsa”  “masha Allah Dr.Nasir nagode sosai ka min albishiri mai daɗi” na dade ba’a fada min maganar data saka zuciyata farinciki ba dr nasir ya kalli maryam da murmushi a fuskarsa “to hajiya Mar-Adam zance ko Mrs Adam? Allah ya bada lafiya” maryam tayi murmushin ƙarfin hali  tana kallonsa  zuciyarta na rawa dan tun daya fara maganar ciki ta shiga damuwa mai tsananin dan ita kanta tana zargin ciki gareta duba da watan ta na uku kenan bata ga period ɗinta ba. “Allah ya sauwaƙe  ya bada lafiya” da  “Amin” ta amsa cikin ƙarfin hali.

Dr.Nasir Ya juya ya fita daga gidan farinciki agurin mami da ƴaƴanta ba'a magana kowa ka kalli fuskarsa kwance yake da annurin farinciki gabaɗayansu murna suke har sun kasa ɓoye murnarsu mami ta riƙo hannun maryam cikin nata tana kallonta cike da kulawa tace “ke kuwa Maryam garin ya akayi kika samu rauni?” maraym tace. “walalhi mami  muna qoqarin karya kwana ne akayi akasi wani me mashin ya kwaso a guje, ganin kamar zai yo kan motar ne sai ido na ya rufe daga hk ni dai bansan yadda akayi ba kaina ya bugu da stearing” mami tace. “yanzu banda Allah ya taƙaita ai da abun ya wuce haka ga ciki ajikinki”  .nana hauwa'u tace. “Alhamdulillah da Allah ya taƙaita” cike da murna ta ƙarasa maganar.  “ai duk adamcy ne ya janyo da yanzu wani abu ya samu cikin jikinta me za'ace?” nan da nan mami ta shiga zuba wa Adam  faɗa da baya nan akan me yasa bai jira Maryam  ta gama shiryawa sun fito tare ba?  cikin raunin murya “daman ai duk shi yaja mana wannan matsalar, wallahi mami  in kinga abubuwan da yayi mata agabana   sai kin tausaya mata” cewar ni'ima “kamar wata baiwa ya ajiye a gidansa ba matarsa ba” mami ta tsurawa Ni'ima ido tana kallon fuskarta kar dai itace Ƴar iskar ƙawarta da yake faɗa? “ko abinci ta girka sai yaga dama yake ci, komai tayi bata  masa gwaninta, sai yayi tayi mata  tsawa yana hantarar ta wannan wani irin aure ne?” mrym tayi saurin take ƙafar Ni'ima “kinga malama ki bari ayi magana yanzu an daina auren wahala idan bazai iya ba ya sallame ki, ki kama gabanki idan kin haife abinda yake cikinki ki kawo masa ki dire ai namiji goma ba uba goma bane " Hjy zulai da mamaki take cigaba da kallon Ni'ima tana tunanin in da tasan fuskar “haba Ni'ima wai meye haka ne ?dan Allah kizo ki wuce gida dan Allah nace miki ina son rabuwa da mijina ne? koni na faɗa miki yana min duk abinda kika furta “au karesa zakiyi saboda baki da hankali ai duk abinda idanuna suka gane min kamar na faɗawa ummah na gama” tana gama faɗar haka ta juya cikin tsananin fushi.”

Cike da ɓacin rai nana hauwa'u tace. “sister wannan fa wacece ita? Jiki a sanyaye ” Maryam tace. “ɗiyar sister ɗin ummammu ce “kai shiyasa nake ta mata kallon sani kar dai ɗiyar umaima ce?” Maryam ta gyaɗa mata kai alamun eh. “shine zata dinga faɗar magana akan yaya? kuma ai kice kika bata  wannan damar” “kamar ya sister?” maryam ta faɗa jikinta na ɗan rawa “idan baki faɗa mata komai akanshi ba ya'akayi tasan irin zaman da kuke yi?” aunty shahida ta faɗa ranta a ɓace “karfa kiga duk muna bayanki  ki ɗauka bama son shi ne, adam rayuwarmu ne kema kuma kinsan da haka Maryam ta runtse idanunta sai ga hawaye masu zafi cike da tashin hankali take jin yadda numfashinta ke sauka da ƙarfi. shi kenan Ni'ima ta haɗa mata bala'i “duk muna bayanki sakamakon irin tsanar da yake nuna miki da kuma irin ƙaunar da mahaifiyarmu ke miki” “ dan Allah aunty shahida kuyi hakuri ba'a bakina taji komai ba ummace ta faɗa amman..” katseta aunty khadija tayi ta hanyar cewa. “ita umman taki meye amfanin faɗawa mutane? mun sani sarai adam bai kyautawa amman kuma meye abun faɗawa mutane anan? mufa mun sani sarai ummanki bata ƙaunar danuwanmu, amman mu dai-dai rana ɗaya mun taɓa sauke haushin haka akanki ? kullum yanda rayuwarki zata samu cigaba a gidansa muke" .
Maryam tasa kuka cikin tsananin damuwa .”

“dan Allah ya isa karku saka min yarinya gaba da bala'i dame zataji ?da maseefar ɗan'uwanku ko da naku sai kun harbe mata zuciya ta mutu kowa ya huta ? kuma ai bai barku ba bare ku shigar masa” kuma karya aka fada akanshi ?halinsa ne fa ?“koma dai menene mami bazamu lamunta ba kuma kar mu sake jin taje gidanki daman shima yace ayiwa ƴar iskar ƙawarki congrent warning karta sake shigar masa gida  ilai kuwa ashe ƴar iskar ce ai duk abinda kika ji yaya yayi mgn akai mai mahimanci ne”  cewar zabiba nana hauwa'u kam tun maganar farko bata sake cewa komai ba, atare suka miƙe aunty shahida aunty Khadija da zabiba sukai ma mami sallama tayi masu addu'a tare da yi masu fatan  alkhairi  nana hauwa'u bata sake cewa komai ba mami ta laluɓo wayarta daga gefenta ta ɗauka ta soma ƙoƙarin kiran ATA “Bari ina zuwa na kirasa dani yake zancen wato cin mutunci da tozarci har agaban mutane?"  maraym tayi saurin riko hannun mami  tana kuka tace. “dan Allah mami ki rufa min asiri kar kiyi masa magana yanzu idan ma son samu ne karki ce masa komai” mami  ta ƙara wayar a kunnenta tana cewa. “rabu dani gara na faɗa masa halin da'ake ciki tun kafin baƙin cikinsa yasa a rasa cikin jikinki .”
Chapter 71 · 0% Book details