← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 102

Sashe 22

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ATA yaja tsaki yana cewa “nonsense ! ba tsaki zaka já ba ka kalla ka gani kai kanka zaka fahimci abinda nake nufi, yarinyar da nake fada maka ce, ata da yayi niyyar kallonta ya fasa ya cigaba da kallon ammar fuskar tashi nan babu wani annurin kirki sai dai bugun zuciyarsa ya qaru sosai fiyye da duk wani tunanin mai karatu ” maryama mai kyau !Ammar ya kira sunanta “saurin juyawa ATA yayi yanayin bugun zuciyarsa bai saisaita ba, maryama kuwa juyowa tayi ahankali sanye cikin kanki bautar kasa ta nade kanta da qaramin hijab kayan sun matukar yiwa jikinta kyau “ mr ammar ta hango tare da bayan wani tsaye .”

“Mai kyau qaraso mana mu gaisa “ tayi murmushi wanda yake qara tafiyar da imaninmu mutun “ahankali ta soma takowa zuwa inda suke tsaye tana wata irin tafiya da mutane suke ganin tsabar yanga ce tayi mata yawa nan kuwa rashin kibar da bata dashi né ya janyo haka “kalleta abokina gashi tana nufomu zaka fi qare mata kallo sosai wallahi yriyar ta had’u” bazan kalleta ba tunda ta had’u ka aureta mana ,duk kabi ka damu mutane Kmr wanda bai ta’ba ganin mace ba “bai fi sauran taku biyu ta karaso zuwa inda suke tsaye ba ATA ya soma d’aga kafafunsa bai tsaya akoina ba sai a inda motarsa take tun kafin ya qaraso masu tsaronsa sun zagayesa .”

Murmushi kawai ammar yayi yana d’auke idanunsa daga kallon bayan ATA “mr ammar barka da rana ya fama da jamaa ?tayi mgn a natse cikin sanyayyar muryarta “na kusan sumewa da wannan murya fa “ maryama ta d’an zaro ido tana cewa “wace ni dan allah ka rufa min asiri kar madam tasamu wannan labarin na shiga uku na “mu shi uku dai “ya fad’a had’e da murmushi, cikin marairaicewa tace “kaji ba ashe kaima tsoronta kake ji “yasa dariya adaidai lokacin da motocin ata suka fice yayinda ammar ya cigaba janta Kmr yadda ya saba .”

kai tsaye abdullahi estate ata yace a wuce dashi ana gama daidaita parking ya fito ya nufi gidan mami tana daga zaune taji ana yunkurin bude kofar ta tsaida idanunta akan kofar dan ko baa fad’a mata ba jikinta ya gama bata d’an lelenta ne ke tunkarota “a natse ya turo kofar ya shigo kana ya maida kofar ya rufe akan mami idanunshi suka fara sauka bayan ta kallesa ta dauke idanunta akanshi zuwa wani gefe tana jijiga kafarta tayi tmkr bata ji dadin ganinsa ba alhalin kuwa wani farinciki ne ya mamayeta domin tun da ta gansa tasan tayi winning yazo ban hakuri ne .”

Ahankali ya tako zuwa inda take zaune akan kujera wanda zuwa lokacin tunin ta runtse idanunta durkusawa yayi a gabanta yana sauke numfashi tare da d’auran hannuwansa akan gwiwowinta “Kiyi hakuri sweetheart ki yafe min nasan ban kyauta miki ba ,ban san abinda yasa na aikata haka ga mahaifiyata ba wacce bani da kamarta ,duk duniya itace take dani nake daita.”nan da nan hawaye ya jike gashin idanun mami “yanzu zagin wad’an da suka manyanta a zamaninku ya zama wani abun ado shiyasa kayi min son ranka kuma agaban matarka , me kake tunani idan ba maryam ka aura ba ? “kaga kenan ka siya min raini ne a wajenta ko kuma nuna mata kofar yi min abinda ta ga dama .”

“ sweet heart na aikata hakan ne abisa kuskure amman kiyi hakuri dan allah “ ta d’aura hannunta a saman nashi kawai batare da ta sake cewa komai ba tana jin tsananin qaunarsa .“Kiyi hakuri kiyi min addua sweetheart ko allah zai sa min son diyarki a zuciyata ko kad’an ne , sweetheart har yanzu na kasa manta mafarkina ina tsananin sonta gashi bansan inda zan sameta ba sannan duk yadda naso na cireta araina na manta daita na kasa manta komai nata .”bugun zuciyarta, numfashinta fuskarta da kamshinta idanuwanta murmushinta hawayenta sautin numfashinta sweetheart bazan boye miki ba na sha saduwa daita acikin mafarkina .”

Mami ta tsura masa idanunta tana kallonsa “na fara shan sigari duk dan saboda ita haka zalika a qoqarin na manta daita ne na fara shan giya ina danne zuciyata akanta ,nayi iya yina domin na manta daita amman wallahi sweetheart abun yaki aiki har yanzu koina na juya ciwo nake ji acikin zuciyata “mami tayi shiru zuciyata cike da tsananin tunani abu daya ne yayi mata dadi acikin magangunsa shine rokon adduarta na allah ya saka masa son mrym ko kad’an ne wannan abu ya sanyaya zuciyarta kuma daman tana wannna adduar .”

“Sweetheart nifa abun tausayi ne abun a tausayawa ne akwai ciwo mai zafi acikin qirjina bana buqatar tausayawar kowa sai taki kece kawai zaki tausaya min domin kece kawai kika san ciwona kuma kece kawai kike sona tsakanin da allah.“mami ta numfasa tana cewa “adamcy nah ina tsananin sonka da tausayinka kai ma ka sani ..”“na sani sweetheart amman akan yarinyar nan kin canza min koma nace kinfi sonta akaina,mami ta kallesa kawai “sweetheart ki janye maganarki akaina zan cigaba da rayuwa daita Kmr yadda kika bukata amman batu na samammarta farinciki babu shi domin ni kaina zuciyata baa cikin farinciki take ba dan haka dan Allah ki janye magarki akaina .”

Ta girgiza kai alamun a’a “sweetheart kin janye dan idan nayi kuskure kin bin umarninki wani abu zai faru dani idan kuma wani abu ya sameni kece kike da asara sam ita ba asararta bace kina ji kuma kina gani zata komawa wani ta bar miki d’anki da rayuwar daya tsinci kanshi .” muryarta a sanyaye tace “babu abinda zai sameka adamcy kuma Ina rokon Allah ya kawo maka saukin abinda Ke damunka "ta qarasa fada tana rufe fuskarta da tafin hanunta hadi da rushewa da kuka .”

“why sweetheart me yasa zaki min asarar hawayenki bayan kin min addua?”addua nafi bukata daga gareki kuma kinyi min na kuma gode Kiyi haquri don Allah ki daina kuka ni dai kin janye furucin ki akaina “na janye kai ma kuma kayi min alqawarin bazaka takura rayuwar maryam ba .”dan allah ka barta tayi farinciki a gidanka wallahi bancin mutane zasu zageni da na raba aurenku kowa ya huta“
“sweetheart babu mai zaginki kuma da zaki min haka wallahi da naji dadi da samun kwanciyar hankali “uhmm adamcy taa girgiza masa kai “kayi hakuri kawai adamcy zan maka addua kamar yadda ka bukata ya sauke wani numfashi yana mikewa ya zauna gefenta ya zauna yana kiran sunanta .”

“sweetheart!”
“ina jinka adamcy “ina son zan qara aure“bazan hanaka qara aure ba adamcy amman dan allah ka bari zuwa nan gaba kad’an dan bazan ta’ba yarda ka shigo da wata gidanka ba alhalin diyata bata da matsayin komai a wajenka “why sweetheart “?mu bar wannan maganar adamcy muyi wata dan bana son jinta for now shiru kawai yayi yana mai runtse idanunshi shi kad’ai yasan zafin da ciwon da zuciyarsa keyi .”

“Sweetheart cikin satin nan in sha allahu zan bar kasar nan zuwa holland “da sauri mami ta kallesa sam maganar bata mata dadi ba ,kuma tasan dan ya nisanta kanshi da maryam ne “zaka bar kasar nan saboda maryam ko ?tayi maganar kamar zatayi kuka “ko d’aya sweetheart “saboda me zan yi tafiya saboda ita ?”kema kinsan tafiye tafiye yana cikin tsarin aikina” mami tayi shiru ya riko tafin hannunta cikin nashi “sweetheart!”ta sake kallonsa “ki kwantar da hankalinki nifa banki na daina tafiya zuwa koina ba saboda ke “wa na ajiye a inda zani ?”

“Me zakaje yi a hallond?yayi shiru yana kallonta “naga duka yaushe maryam ta tare da zaka tsiro tafiya gsky nidai idan son raina ne ka bar tafiyar nan ka wakilta wani ka d’an zauna da maryam “shikenan sweetheart “ya bata amsa da hakan cikin halin damuwa ya mike tsaye yana mata sallama murmushi ta sakar masa amman gida zaka wuce ko ? ya gyada mata kai kawai “to allah yayi maka albarka ka gaishe min da maryam anjima manu direba zai kawo maku abinci “to !kawai ya fad’a a takaice sannan yasa kai ya fice daga parlour’n massalacin ya nufa domin gabatar da sallar laasar .”

Hisham zaune akan kujera yana waya da nuzla “eh har yanzu ina office , allah kuwa da gaske nike amman bari nayi sallar laasar na tura miki babu mamaki ma idan na tashi aiki zanzo na gaki kafin na wuce gida , sosai kuwa ya fad’a yana murmushi kmr yana gabanta ,ahankali yaji ana Knocking din kofar office dinsa amman ya share yaki bada umarni shigowa ya cigaba da waya da nuzlah har kusan mintuna shabiyar sannan yace wa nuzla “bari zan kiraki nan da minti biyar acan bangaren nuzla cike da shagwaba tace “a’a ban yarda ba “okay to shikenan zakiji komai da zanyi “yana gama fadar haka ya bada umarni shigowa ga diyar aminin abbansa dake aiki akarkashinsa .”

Zakiya ta tura kofar office din ta shigo ahankali ta tsaya agabansa amman bai d’ago ya kalleta ba ya cigaba da wayar da yake .”a tsanake ta bude bakinta ta kira sunansa “hisha…yayi saurin d’aga mata hannu yana cewa alamun tayi shiru dan da yasan itace bazai bada umarnin shigowa ba “a’a abdull ne ya shigo akwai maganar da zamuyi dashi shiyasa nace ki bani minti biyar “okay naji da zarar na gama dashi zan kiraki ya katse kiran sannan ya kalli zakiya yace “yaya akayi ?sai data numfasa kana tace “akwai matsala fa “me ya faru “ya budurwa zata zauna ta dinga tayar maka da hankali haka?” nifa abokiyar aikinka ce kuma kusan yaruwarka wacce ko matarka tasan da zamana bata ta’ba nuna damuwarta ba sai wata can .”

“aa dakata zakiya banason haka matsayin nuzla dabam a wajena tana sama da kowacce mace a wajena ba wai wata bace kin fahimta ko ?“ kana nufin har matarka ?“eh bakiji nayi generalizing ba nace kowa , tafi kowace mace dan haka bana had’a maganarta data kowa ki kyaleni ke bani ma abinda ya kawoki ki bar min office menene ma ya kawoki “
? ”mr Ibrahim yace ka tura masa idan ka gama “tô naji zaki iya wucewa please ya fad’a yana nuna mata kofar fita da yatsun hannunsa .”
Chapter 22 · 0% Book details