← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 102

Sashe 76

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batun sakin maryam ya bazu acikin abdullahi estate masu murna nayi ,masu bakinciki nayi aunty abida kam tafi kowa murna faruwar wannna sakin dan lokacin da taji har wani tsalle da rawa tayi a bangarenta batare da kid’a ba tana cewa “shikenan nan sultana zaki dawo a saa, kece zaki maye gurbin kowace mace a wajen adamcy ,inganga inganga !!rawa tayi sosai tamkr wata zararriya a qarshe ta suri wayarta ta shiga neman layin mahaifiyarta sun d’auki mintuna talatin suna waya sannna sukai sallama ta kira sultana tana d’auka tace “wai zaman me kike yi ne har yanzu ?” Kiyi qoqari ki dawo dama biyu ta samemu ya saki matarsa ga kuma neman masu kwararrun zane da yake nasan yana ganin zanen Kanwata zai rud’e daga nan kuma shinkenan “okay to shikenan dan girman allah ki ajiye komai ki dawo kar murasa damarmu okay bye ta katse kiran tana cigaba da rawa yesmin ta fito daga dakinta tana kallonta murmushi ta sakar mata tana cewa “yesmin kin kusan zama cikakkiyar ‘ya a wajen babanki AD “‘ya kuma mum ?yes auntynki sultana zai aura ta qarasa maganar tana rungumeta“.tsabar murna washegari aunty abinda ta shirya walima gabdaya estate din babu wanda bata aikawa da snks da drink ba duk wanda ya kalleta zai fahimci tana cikin murna .”

nan da nan zance ya kai kunnen mami babu abinda tace face “allah ya shiryeta domin duk mace mai hankali bazatayi murna dan an saki yaruwarta mace ba ita yanzu bazata sake matsawa adamcy ba amman kullum cikin yi masa addua take idan da rabo allah ya daidaita su. .allah sarki maryam ta dad'e kwance akan gado tana sak'e-sak'e a ranta, dan ta ji zafin abinda aunty abida tayi ,tsaki taja tare da mik'ewa tsaye tana d'an zagaya d'akin "dole ne na nuna ma
abida kuskurenta,zan nuna mata baa kishi da irin mu yaran zamani, tunda na lura shiru baya mata sosai abinda aunty abida tayi ya 6ata ma maryam rai, zan nuna mata iskancinta wasa ne wannan karon a bayyane tayi maganar tana wani shu'umin murmishi.”

*********

Zaune yaya sadam yake a haraban gidansu akan daya daga cikin kujerun dashi ne ya ajiyesu saboda abokansa domin zama yana sanye cikin farin yadi idanunshi manne da farin glass idanunshi kar akan wayarsa yana karanta sakon Nadia a natse ta fito zuwa garesa ahankali ya soma ganin tahowarwata ta kasan idanu shi cikin tafiya ta Kamala sanye cikin doguwar riga yellow ya dago kanshi ya tsura mata ido tana kyau sosai dan maza zai had’ata da nadia ba har ta gama qarasowa garesa fuskarta dauke da murmushin farincikin ganinsa tace "sannu yaya dan allah kayi hakuri na barka zaune ka kadai“
murmushi ya sakar mata tare da lumshe mata idanunshi "karki damu ko zan kwana ina jiranki bazan gaji ba sauraniyar kyawawan mata duniya kuma zabin umma nan ki zauna ya nuna mata kusa dashi ta zauna a natse tana kallonsa cike da jin kunyarsa "ina yini ya aiki da fatan komai Lfy ?tayi masa tmbyr a jere tana sunkuyar da kanta kasa tare da kamo yatsun hannunta tana wasa dashi "maryama duk Alhamdulillah mun godewa allah ya mumcy take ?ta gyda masa kai kawai alamun lafiya a hankali ya soma janta da hira sai dai bata wani mgn daga uhm sai uhm take cewa "maryama ! Ya kira sunanta ta dago a natse ta kallesa na second daya ta sake maida kanta ta sunkuyar "ga dukkanin alamun kamar agajeye kike ? Tai murmushi batare data dago ba "nan da sati uku zaki kasance a gidana a yanzu nake jin na matsu naga kin kasance a gidana” ajiyar zuciya mai karfi ta sauke tana dago kanta ta tsura masa idanunta "ta so ya kurewar tamvayarta aikin da take fita nema kullum amman sai ya wani kawo mata maganar aure .”

ta fahimcesa sosai shi mutun ne da bai da caring me taci ko me tayi ko a wani hali take duk ba damuwarsa bace idan ma yazo gurinta ba wani hirar soyayya yake mata ba wanda zai dauki hankalinta zai kama gabansa shiyasa duk tsawon lokacin da mahaifiyarsa ta hadasu bata ta'ba jin komai akansa ba sai dai tana danne komai saboda mahaifiyarta da mahaifiyarsa .”yana ganin girman mahaifiyarta sosai yana kula dasu sosai tun kafin a had’asu aure "kinyi shiru kina kallona kice wani abu mana ?shiru ne dai Ya sake biyosa baya har sanda wayarsa ta dauki qara sauti Ya dauki wayarsa dake ajiye a gefensa ya duba sunan nadia ya gani yana yawo a screen din wayar cike da firgic ya dubi inda maryama take sannan ya sake maida idanunshi akan wayar da kyar ya sauke naunayen ajiyar zuciya yayi disconnecting din kiran ya cigaba da magana " a she dai ni ne wanda zanyi wuf da wannna kyakkyawar yarinyar magana yake amman zuciyar maryama ta kasa samun natsuwar allah sarki yusif ashe Ke din ba rabonsa bace ?naunayen ajiyar zuciya ta sauke “kina da kyau sosai na godewa ummah datayi tunanin hadani dake na gaji da ganinmu haka ina son na killaceki a gidana "kana son ka killaceni agidan cike da rashin yanci ba ?tayi masa tmbyr a zuciyarta .”

“maganar da nake miki yanzu haka komai da zan saka agidanmu ya kammala zamu yi rayuwa mai dadi ko kina son na ajiyeki a wajen umma ne saboda yanayin aikina.”? yana gama fadar haka Ya mike sakamakon wayarsa data sake daukar qara  "excuse me! ya kamata ace kana duba yanayina yaya sadam har yanzu ban ji amincewarka akan aikina ba zaka yarda na cigaba da yiwa kafanunka zane ko kuwa ?.”“bana son sai bayan munyi aure kace bakasan da zance ba wannan aikin rayuwata ce kuma ina son ya kai ni matakin da ya zarta yadda nake a yanzu babban burina bai wuce na samu aiki kafanin AGC ba .taí shiru tana jiran taji mai zai ce amman yayi mata shiru saboda raayinsa amman dole yanzu kam ya amince dan yasan idan yaki amincewa zai ta’ba zuciyar ummansa ya tsura mata ido yana nazarinta a yanayinta zata iya komai akan aikinta  ." ta mike a natse tana dubansa "kayi shiru yaya sadam kace wani abu mu kawo qarshen maganarmu banason muyi aure daga baya muzo muna samun matsala akan aikina "ka amince zaka aureni da aikina sannan zaka min hanya naga mai kafanin AGC ? ta fad’a hk sbd tasan su yusif nada hanya da karfin iko shiru yayi yaki cewa komai yana sauke numfashi da kyar, domin kuwa abu biyu né suka hade masa guri daya ga tambayar maryama ga kiran da nadia ta damesa dashi wanda baya  jin zai iya duka abu biyu din ."

“Ina duba yanayi na zaman takewar aurene yaya sadam domin kuwa kai kana cikin mutanen da suka san koni wacce irin rayuwar gidanmu mahaifiyata da mahaifina taí mgnr tmkr zatai zubar da hawaye dan gbdy idanunta har sun canza kala daga fari zuwa yellow "ya kamata mu tsara komai yaya sadam domin kuwa banason damuwa arayuwar aurena ta qarasa mgnr tare da kai yatsun hannunta biyu ta dauke hawayen dake kokarin saukowa kuncinta ".
numfashi ya sauke da karfi sannan yace "shikenan zakiyi aikinki “bari naje ana nema zamuyi waya ya fada yana kokarin barinta tsaye tare da manna waya a kunnensa ya nufi kofar fita taí shiru tsaye tana duban bayansa "yanzu irin wannan mijin zata aura tai rayuwar aure dashi ?anya kuwa idan ta auresa zata ji dadin rayuwar aure kuwa yadda yake da rashin nuna caring ?” yanzu a halin da take ciki kowa Ya ganta yasan tana cikin damuwa dan gbdy komai nata Ya canza amman kalli yadda ya bar gabanta batare da Ya tsaya ya fahimci matsalarta ba bare ya kawo mata mafuta oh allah karkasa nayi Kuskuren aure irin wanda Mahaifiyata tayi ya allah ka taimakeni kasa ya canza duk da banason shi saboda rashin caring dinsa dan kusan matan duniya shine matsalarsu a gidajen mazajensu a yanzu, cike da sanyin jiki har  ya bacewa ganinta tana tsaye a wurin rungume da hannunwanta a kirji  jiki a sanyaye ta nufi kofar part dinsu ."

*******

motarsa na shigowa haraban ma'aikatan yaji gabansa yayi wani mummunar faduwa da karfin gaske shiru yaki fitowa daga cikin motar  yana tunanin abinda yasa yaji hk byn tun a gida bai tsinci kansa cikin wannan yanayi ba sai daya shigo ma'aikatan iskar ya furzar ya daga kafadunsa alamun babu komai a hankali ya zuro kafafunsa dan tuni an bude masa kofar mota  ya fito yana gyara zaman suit din jikinsa sannan ya soma taku a hankali qirjinsa na cigaba da luguden bugu yayi qoqarin kawar da yanayin da  gangar jikinsa ya shiga ta hanyar tura hannusa daya cikin aljihun wondonsa." duk inda ya wulga maaikata ne Ke kokarin kawo gaisuwa sai dai kai kawai yake gyada wasu ,wasu   kuma yayi masu banza har ya hau lift da zai kaisa  sama na uku inda anan office dinsa yake yana sauka yaji wani sabon faduwar gaba wanda ya rasa dalili nan ya dan rage tafiyar da yake ya dawo yana daga kafafunsa da kyar saboda sanyin daya ziyarcesu alokacin daya tun daga nesa ya hango bayan wata yarinya suna magana da wasu daga cikin maaikata  kamar ya tsaya sai kuma  ya karya kwanan da zata kaisa office dinsa cak yaja ya tsaya sakamakon jiyo sautin muryar yarinyar  shiru yayi yana cigaba da saurara maganarta tamkar dai  mafarkin da daya saba yi “anya kuwa muryar  tace ko dai mafarkin daya saba yi daita ne suna hira ?.
Chapter 76 · 0% Book details