← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 102

Sashe 60

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Makalewa tayi a bangon koridor hawaye masu dumi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta ta goge shi kuwa rufo kofarsa yayi ya murda key a galabaice ya fad'a bed dinsa ya runtse idanushi ya sake jan laulausar bargo ya lullube jikinsa maryam kuwa natsuwarta take qoqarin daidaitawa amman ta kasa dan hawayenta ya gagara tsayawa bata koma dakinta ba sai wajen karfe daya wanda a tunaninta zuwa  wannna lokacin  mami tayi bacci sannan ta nufi dakinta tana danne sheshekar  kukanta Koda tashiga dakin mami na kwance , maryam ta haye saman gado ta kwanta lamo abayan mami tare da kamkame jikinta wani irin kewa da son mijinta ce ke damunta amman shi babu halittar daya tsana kamarta , kuka take son yi dan rage damuwarta amman bbu dama domin damuwarta zata iya haifawar da mami damuwa , a dalilinta mami zata iya muzgunawa yaya Adam , ita km abinda bazata so ba kenan, batason abinda zai sake hassalashi akanta
ta kai hannunta ta dafe daidai satin zuciyarta dake mata ciwo bayan Kmr minti goma mami ta tashi zaune ta dubeta tana mata kallon tsab batare da tayi magana ba sannna ta sauko ta shiga bayi ta dauro alwala ta fara gabatar da nafilflii .”

" juyi tayi tare da sake kamkame jikinta “yanzu ita yaya zatayi da rayuwarta ?”mayye zatayi ?”ga soyayyarsa ga tsananin sha,awarsa duk sun taru sun hade mata ,take zuciyarta ta bata amsa da kima kama kanki da rashin hakurinki dan muddin kikayi kuskure sake zuwa inda yake zai iya kasheki tunda har ya rantse “ya allah ka taimakeni kasa na samu ciki a karon mu na biyu dashi yanzu ta shiryawa kowani rigima zaiyi idan ciki ya bayyana ajikinta a boye take goge hawayen dake bin kuncinta ,har mami tagama tayi laziminta da sauran addu'o,inta
.bacci bai yi nasarar daukar maryam ba kuka take qasa qasa . Tana jin motsin mikewar mami ta shanye kukanta Tare da goge hawayen idanunta amman hakan bai hana mami gane wani abu ba ,daidai inda fuskarta take tazo ta zauna tare da kamo hannuta ,"me kike tunanin maryam ko kuma nace me ya dawo dake dakin nan har ya hanaki bacci ?

Kafin maryam tace wani abu mami ta km jiho mata wata tmbyr “sai ma naga kmr kuka kika yi ko?
Maryam ta Mike zaune suna fuskartan juna da mami ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka yi nasarar zubowa...."mayye km abin kuka tmbyrki kawai nayi fa? sai km ki kama min kuka.” wani abu adamcy yayi miki ?ahankali ta girgirwa mami kanta “ki fad’a min idan wani abu yayi miki da kyar maryam ta iya bude bakinta ..." ammi me yasa yaya Adam ya tsaneni haka ?kullum so nake naga na rayu dashi har qarshen rayuwa amman shi kullum burinsa ya ruguza rayuwar gidan aurenmu da ni kaina bansan yadda zanyi abubuwa su dawo min daidai tamkar kowasu maurata ".

“basan abinda na aikata masa ba da kullum yake son ganina cikin qaqa na kanyi .Ida abubuwa da yake min suka cigaba da faruwa bana tunanin zuciyar dake kirjina zata cigaba da bugawa , mami tambayar min shi laifin me nayi masa ?”wallahi ni ina qaunar zama dashi muddin raina .”mami ta rungumeta ajikinta tana mai tausaya mata "kukan ya isa haka babu abinda kika masa halinsa ne haka
halin bakar zuciya irin tasa yana damuna ni kaina na gaji da halinsa ,amman matsawar Ina raye ba zaki taba kasancewa cikin bakinciki ba , bugu da qari har yanzu kina da sauran damar rabuwa dashi dan bazan cigaba da baki hakuri ki cigaba da zama dashi ba dan duk wani abinda zaa masa anyi masa idan dai ba rayuwarmu yake nema ba .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 19

Sosai mami ta dinga rarrashin maryam tana masu addua “allah ya daidaita tsakaninku ,Allah ya saka tausayinki acikin zuciyar adamcy ,allah ya kawo zaman lafiya a tsakaninku har qarshen rayuwarku “ahankali maryam Ke amsawa da “Ameen mami ,sai abu na gaba maryam na fahimci kina sakaci da addua ,Ina son kinsan wani abu ba’a nasara sai an rike Allah,idan ka rike Allah,Allah ta’ala zai taimakeka ki jajurce da adduoi maryam “ki rage wasu abubuwa ki maida lamarinki zuwa ga Allah maryam ta gyad’a mata kai alamun taji ,tana nan kwance ajikin mami har ta fara gyangyad’i alamun bacci .ahankali mami ta d’an buga bayanta tana cewa “maryam kwanta kiyi bacci da sannu allah zai kawo mana saukin wannan tashin hankali sannan ya kawo fahimtar juna a tsakaninki da mijinki .“maryam ta tashi daga jikin mami tana shafa idanunta sannan ta zame ta kwanta zuciyarta cike da soyayyar mijinta mami ta mike itama ta samu gurin nan kusa da maryam ta kwanta sai dai ita sam bacci yaki d’aukarta, kwakwaluwarta ne ya shiga cajin tunani
dan dole tasan abun yi tun kafin adamcy ya kashe maryam da bakincikinsa dan zuwa yanzu hakurinta ya fara qarewa akanshi .”

Juyi kawai mami take akan katifa kafin ahankali ta taashi ta sauko daga saman katifa ta tsaya gaban maryam tana kallon fuskarta bacci take, sai dai kana kallonta zaka san a matuqar wahale take baccin dan kana kallon yadda take sauke numfashi da ajiyar zuciya da karfi .”d’auke kwayar idanunta mami tayi ta fara zagaye d’akin kafin ta fara zance zuci ita kad’ai “dan dole zulai kiyi wani abu akan zaman ya’yanki “ to mai zanyi ?mai zanyi ? ta tambayi kanta har sau biyu tana cure hannuwanta waje d’aya “Kiyi qoqari adamcy ya kusanci maryam ko Allah zai basu rabo wata killa sanadiyyar hakan ya sauko ya sausauta mata ya rungume aurensu. “tabbas haka zakiyi zuciyarta ta bata wannan shawarar “to ta yaya zan masa magana ya fahimci abinda nake nufi ?”ta sake jefawa kwakwaluwarta tambaya shiru tayi yayinda ta koma ta kwanta akan katifa tana sauke numfashi tana mai sake had’e hannuwanta guri d’aya kafin ahankali ta soma sakin wani irin murmushi sakamakon abinda zuciyarta ta shirya mata wanda zai kawo mata saukin al’amuran ta, alokaci d’aya ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya “dole dai kina bukatar shawarar shahida kafin ki aikata komai .”

Washegari da misalin karfe tara na safe maryam tana zaune akan kujerar sofa tana danna waya yayinda mami ke zaune akan salayya tana lazimi ATA ya shigo bakinsa d’auke da sallama sallamarsa kawai maryam ta amsa batare da ta kallesa ba ta cigaba da daddanna wayarta shima ko kallonta bai yi ba ya cigaba da tsayuwa mami ta d’an kallesa yana sanye da jallabiya yayi mata kyau sosai sai dai bata jin dadin ganin yadda ko yaushe fuskar nan tashi take a had’e’ ,sannan bata jin dadin ganin shi da maryam haka zaman su sam babu sha’awa kana ganin yanayinsu kasan gabad’aya zukatansu basa cikin walwala da jin dadi most especially adamcy wanda zaka fahimci baya son ko bisa kuskure ya kasance a duk inda maryam take .yayinda ita kuma tafi qaunar su kasance tare akoda yaushe ya rungumeta babu kyama ,mami na kallonsa ya juya cikin takun isa ya fita daga d’akin ganin tana lazimi ,bayansa mrym tabi da kallo har ya fice gabad’aya tasa hannu d’aya ta dafe goshinta tana jin wani tuttukin bakinciki tana jin zafi da ciwon abinda yake mata na kyarma da rashin son kallonta inda take ,amman ita ta rasa dalilin da yasa zuciyarta kullum take sake macewa akanshi ,a kullum zata d’aura kwayar idanunta akanshi to wallahi son shi da qaunarsa ne Ke sake huda zuciyarta da gangar jikinta” zata so ta mallakesa kamar yadda mahaifiyarta take buri amman hakan taki samuwa kullum babu abinda take hangowa attare dashi sai zallar qiyayyarta sam komai nata baya burgesa ita kuwa kwarjininsa kesa bata iya d’aukarwa kanta mataki ,bata iya tunkurarsa da komai tana matuqar jin tsoronsa aranta “da sanyi jiki mami ta qaraso inda take zaune ta kai hannunta ta dafata, ta d’ago tana duban mami da idanunta dake cike da ruwan hawaye mami tasa gefen hijab dinta ta goge mata hawayen da suka zubo mata batare da saninta ba wani wahallen ajiyar zuciya ta sauke tana kawar da fuskarta gefe“

“maryam !”

Mami ta kira sunanta ahankali maryam ta waigo inda mami take ta sake zuba mata idanunta tana kallonta fuskarta da tsananin damuwa ahankali ta sauke idanunta “ki daina damun kanki akan adamcy idan ba haka ba zaki rasa lafiyarki idan hakan kuma ta kasance babu ruwansa hasalima bazai ta’ba zama damuwarsa ba sai dai ta zama damuwarmu “kiyi hakuri ki dinga kawar da damuwar nan aranki sannan ki dinga kaiwa allah kukanki ,nasani maryam kina hakurin zama da adamcy ne saboda Kina matuqar ganin girmana da mutuntani da kuma qaunar da Kike masa nima kuma haka ne acikin zuciyata maryam ina qaunarki ina qaunar ku kasance a inuwa d’aya dashi .”numfashi ta sauke da karfi tana kallon mami “eh shine ma dalilin da yasa bakya son na rabaku maryam .
Chapter 60 · 0% Book details