← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 102

Sashe 88

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          a natse ya maida agogon ya  ajiye ya qarasa inda wayoyinsa suke  business phone dinsa ya fara  kunnawa nan take kira James  ya shigo lumshe tsumammun idanunshi yayi batare da ya d'aga kiran ba, kiran na qoqarin tsinkewa ne ya d'aga "hello sir! good morning sir ya fad'a a tare ?"morning !ya fad'a atakaice yana hura hanci "akwai wasu mutane da suka zo da  buqatar ganin sabon creation shine nake neman izini a wajenka ko zamu nemi d'aya daga cikin kwararrun da suka kawo  zanensu ko zaa dace ?"lumshe idanunsa yayi yana jin wani irin d'acin maganarsa dan a yanzu bai buqatar ganin zanen kowa sai na wannan yarinyar amman kuma sai ya tsinci kanshi da cewa "okay ! yayi maganar a can kasan makoshi kamar mara lafiya sannan  katse kiran ya fito daga d'akin zuwa kasa ya nufi hanyar da zata kai shi bangaren mami bai wani jima ba ya fito  kai tsaye AGC aka nufa dashi "

Bayan kamar awa uku da zuwansa  office james ya shigo tare da some cike da girmamawa James  yace "sir bayan munyi waya da kai d’azu da safe sai kuma muka canza shawarar mu sake neman wannan yarinyar data zanaka dan gsky gabad'aya zanenta yafi kyau amman anyi rashin sa'a layinta baya zuwa " take ya fahimci kowace yarinya yake magana akai, bai ce masa komai ba ya cigaba da  mgn "kayi hakuri sir nasan zakaji babu dadi aranka amman  ni ina ji ajikina zata zo mana da sabon design masu ... "enough james you can leave ."sorry sir ! tamkar wanda akayi wa duka ko wanka da ruwan sanyi  ya simi simi nufi hanyar fita ."some ta sauke numfashi  tana mai gyara tsayuwarta tare da fara magana "sir masu supply din kaya daga kafaninmu wasunsu  sunki kar'bar kayanmu in group wanda ban san dalilin faruwar hakan ba  "one second! ya furta yana cigaba da operating system din gabansa shiru tayi cike da  girmamawa ,yayinda office din ya d'auki shiru baka jin motsin komai sai na qarar ac da system din gabansa sai kuma saukar numfashinsu "kuma kun tabbatar babu wata matsala a kayayyakin mu ?"no sir babu wata matsala ectually ma wasu sun kar'ba wasu ne dai basu kar'ba ba" amman ai gashi ina ganin sakoninsu cewar basa bukatar design din da akayi masu ne yanzu ke wannan ba wata matsalar bace a ganinki  ? eh nayi magana da oga Ibrahim sir  amman har yanzu bai ce komai ba ina tunanin yana son sai kuyi magana dashi ne "shikenan zan san yadda zaa gyara komai ya mike ya zagayo daga wurin zamansa yana kokarin fita yayi taku d'aya biyu ya tsaya batare daya juyo ba "kisa a   binciko min  inda yarinyar nan take da zama sannan kice james ya kira chef adisa ina son ganinsa gobe goben nan bai tsaya jin abinda some  zata fad'a ba  ya soma qoqarin ficewa "okay sir ."

A dogon koridoor suka hadu da sultan bai  kallesa ba bare ya tsaya duk da yasan wurinsa yazo ya ra'ba ta gefensa ya wuce ,har yayi taku biyu ya jiyo sautin muryarsa " Adam...! ya kira sunansa a gadarance har yanzu kai muke jira da mahaifinmu domin muna da bukatar wani kaso daga cikin kafanuni  araba abamu namu kowa yaci gashin kansa, cak ATA  ya tsaya daga tafiyar da yake ya zura hannunsa daya cikin ajihun wandonsa "idan naki fa ?yayi mgnr batare daya juyo ba " dole kabi umarnin mahaifinmu dan bazamu cigaba da aiki akarkashinka ba alhalin dukiyar nan gabadaya  tamu ce dan dole kayi wani abu akai .”a fusace ATA ya juyo gabadaya ya fuskancesa "kasani wannan dukiyar gabadayanta ta mahaifina ce kamar yadda na fad'awa mahaifinka yau da rokona kukayi zan iya daukar wani bangare na bawa mahaifinku amman tunda zalinci ne abun bazan bada ba kamar yadda na fad'a kuma  zan iya dakatar da duk wani mai numfashi dake d’akinku wanda yake karkashin ma'aikatar nan idan kace karya ne ka cigaba da shiga track dina "shiru ne ya biyo baya"kafin ahankali ata ya wucesa yana jan tsaki tare da furta "nonsense."

*****

Zaune ata yake akan kujera sanye da suit baki yana jujjuya jikinsa bayan ya watsawa chief adisa tambayoyi cikin 'bacin rai ,cheif adisa yayi shiru yana nazarin abinda zai fad'a masa "answer me !ya furta cikin tsananin bacin rai mara misaltuwa "komai zance yanzu bashi da wani amfani sir tunda  na rigada nayiwa sectary dinka bayani komai "Eh nasani but ina son naji daga bakinka ,yayi maganr yana gyara zama tare da daddana system din gabansa  batare daya dago kanshi ba , dalilin dayasa muka daina amsar produc din  design dinku sunyi matukar tsaida ne,dan alal hakikanin gsky kudin daaka sa sunyi yawa yayinda muke samun exactly irin design din a wasu wurare akan farashi mai sauki atakaice dai wannan shine dalili."
shiru ata yayi byn ya gama sauraronsa ya cigaba da tura sakonni kafin daga baya ya dago kanshi a hankali ya kafe cheif adisa dake  zaune a gabansa da ido yana qare masa kallo ta cikin farin glass dinsa sai daya furzar da iska mai zafi sannan ya bude bakinsa da kyar yace "kasan abinda abu original yake nufi ? cheif adisa yayi shiru ,"wadan da kuke siya a sauran compaing's  copy din namu ne, namu kuma asalin masu kyau  ne ". ba maganr quality  ake yi ba sir maganar contitie akeyi kafa san dan kasuwa duk wani dan kasuwa yana bukatar  farashi mai sauki wanda  shine business,  da dai zaa cigaba da bamu farashin daaka saba ne sir da komai zai tafi normal ".ATA ya sauke numfashi yana jan tsaki " ko ku siya a haka ko kuma ku barshi domin bazan rage naira daya daga farashin dana saka  ba yana gama fadar haka yace "get out .cheif adisa ya mike tsaye tare da cewa "okay sir ya dauki system dinsa  ya qara gaba tsaki yayi ta ja babu kaukautawa ,ya mike tsaye ya shiga zariya acikin office dinsa yana shafa sumar kanshi.”

ATA na tsaye a parlour'n mami  ya zuba hannunwansa duka cikin aljihun wondonsa dawowarsa  kenan daga office ko cikakken minti biyar bai yi da shigowa ba sai ga fahad   ya shigo a matukar fusace kamar an jehoshi  yana cewa "wai kai dame kake takama ne ?yayi mgnr yana nunasa  da d’an yatsantsa .""what  do you mean  ?ATA ya tmbyesa a tsawace yana watsa masa harara  a lokacin da hjy zulai ke qoqarin saukowa daga saman ata   "bani zaka tmby ba kamata yayi ka tmbyi dakikiyar kwakwaluwarka ,  taya ma zaka yanke wannan banza hukunci haka?"lafiya fahad ! ?  " mami ta tambayesa cikin rawar jiki “wannan yaron ne mana yake son  jawowa mutane asara  ,yana yin abu tamkar  shi kadai yafi kowa waye wa da ilimi
yau ko kamfanin ba group bane ai bai cancanta yayi  haka ba bare yasan wannan kafanin ba nasa bane shi kadai .ya qarasa mgnr yana kallon ATA a fusace .

Suna cikin haka sai ga yaya Ibrahim shima cikin tashin hankali ya rufesa da fad'a nan mami ta koma kansa "ki duba ki gani mami  yadda farashin komai  na kaya ya sauko daga sauran kamfanoni amman shi  tashi daya ya qara  farashi nikin baninkin gashi costumers sunki karba kaya  daga hannun kowa "very good ."ata ya furta yana hura hanci “What ?
" I said very good ,"ya sake maimaitawa a natse tmkr maganar ba daga bakinsa ta fito ba “very good ma zaka fad'a saboda baka da hankali da tunani "yes of course it good and to be your last warning da zaka kirani da mara hankali ."yaya Ibrahim bai damu da abinda ya fad’a ba yace “me yasa zakayi haka adamcy ?” me yasa zaka bata kasuwancinmu maganar gsky muddin haka zaa cigaba da tafiyar da kamfanin gara kowa ya watse a rufe kamfani kowa ya kama gabansa "okay wannan shine daman shirina ai a rufe kowa ya kama gabansa "Ibrahim da fahad suka kallesa a rude suna mai mamakin jin abinda ya fad'a " yes haka nake so "okay saboda  kasan kana da wasu compaines masu zaman kanka shiyasa kake son a rufe  wannan ?"yayi kyau yayi kyau gara daka fad'a mana muka sani ."ai daman mugunta ne acikin cikin wannan mugun mai girman kan , kai ne dai ka kasa ganewa kake daukarsa amatsayin mutumin kirki ai ga irinta nan zai janyo kowa ya rasa saboda tsabar bakinciki irin nasa da dai a rufe gara a siyar a bawa kowa hakinsa "inji cewar fahad .

Dan allah  fahad ka samu natsuwa kai ma Ibrahim ka natsu kar wannan abu ya zama damuwa " karki damu mami  ba  wani abu bane ai bazamu biye masa ba  zanyi komai domin naga business din ya tsaya da kafafunsa "ko kuma a siyar ba nifa gara a siyar dashi inji cewar fahad "wannan kuma karya ka fad'a  dan matsawar ina raye babu wanda ya isa ya siyar da AGC "mu zuba mu da kai dan halak ka fasa yadda kake ji da  taurin kai muma muna ji dashi a qarshe zan maka gargadi ka rage wannan  zakewar da jijji da kai idan ba haka ba wallahi zaka rasa rayuwarka a banza kuma babu abinda zaayi "yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuu ya fice  har zai bi bayansa mami ta sha gabansa da sauri tare da ware hannuwanta “karka kuskura kabi bayansa ,kana jin mutun yana ikirarin zai kasheka ya kashe banza shine zaka bi bayansa “sweetheart ki barni babu abinda zai iya yi “wallahi bazan barka ba idan kai baka son rayuwarka ni ina da buqatar ka a raye ,oya koma can ka tsaya ko ka wuce d’akinka, tsayawa ya kasa furta komai yana cin ransa .”
Chapter 88 · 0% Book details