← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 102

Sashe 55

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dan allah karki d’aga hankalinki mu jira lokaci amman ni nasan da gaske zai so abinda zaki haifa idan allah yasa an samu domin sosai yaya Adam yake son yara tun maryam na iya bawa nana hauwa’u amsa har tazo tayi shiru sakamakon baccin daya d’auketa ta lullu’be mata jiki ta fito domin siyo mata magungunan da doctor ta rubuta .”bangaren ATA kuwa bai farka ba sai karfe goma daidai ya tashi da matsanancin ciwon kai da ciwon jiki mai tsanani yana tangadi ya tashi ya fad’a kan kujera safo kwaya d’aya dake dakin ya rike kanshi dake sarawa yana tunanin tare da son tuna abinda ya faru dashi ,iskancin maryam na jiya ya shiga dawo masa ,yanayin shigarta da zamanta da kuma coffee din daya sha tsaki yaja ,yayita qoqarin ya tuna abinda ya faru bayan wannna amman ya qasa tuna komai saboda karfin maganin ,lumshe tsumammun idanunshi yayi kawai ya yunkura da kyar ya tashi yana had’a hanya ya daura hannunsa akan handle din kofar shiga bayi sai kuma ya dan tsaya yana ciza lip’s dinsa “amman dai kamar kayi mafarkinka daka saba jiya?” yes nayi mafarkin princess dina ya bawa zuciyarsa amsa da haka sannan ya shiga yayi wanka tsarki ya fito ya tsaya yana kallon d’akin kafin ahankali idanunshi ya sauka akan bedsheets wanda duk ya baci da spam shiru yayi yana mamakin ganin sha shin spam wanda bai saba ganin haka ba a duk sanda yayi mafarkinsa , dan qaramin tsaki yaja sannan ya janye zanin gadon ya nad’e ya ajiye a gefe ya dauki fari bedsheet ya shimfid’a ya shirya ya fita zuwa office.”

Wunin ranar a gidan nana hauwa’u ta wuni tana kula da maryam sunyi hira mai mahimanci maryam tace “sister Kiyi min alqawari babu wanda zai san da faruwar abinda ya faru a tsananina da yayanki “idan ya zama ciki fa ?maryam tayi shiru cikin tsananin tashin hankali “zan so faruwar hakan amman ina jin tsoro zan so ace yana cikin haiyacinsa komai ya faru sister wallahi tunanina me zai je yazo yayinda ciki ya shiga ?kai sister dan allah ki bar wani tunanin abinda zai faru “sai bayan la’asar sannan nana hauwa’u tayiwa maryam sallama ta koma gida “.
Tsawon kwanaki uku nana hauwa’u na zuwa gidan amman ko sau daya basu had’u da ATA ba dan tana zuwa Qarfe shabiyu ta wuce bayan laasar a haka har maryam taji sauki sosai sai dai zuciyarta da gangar jikinta amatukar tsorace suke .”

Yau sati d’aya kenan da faruwar abinda ya faru a tsakaninta da ATA tana zaune a parlour’n sanye da kayan shan iska sai dai ba irin na ranar nan bane wannan yana da d’an dama domin wonda da riga ne masu taushi green colour touch of white wonda iya cinyarta yayinda rigar ta kasance hamles hannunta rike da waya tana chart a group dinsu na matan so ya shigo ko kallon inda take zaune bai yi ba ya nufi hanyar sama yana furzar da hucin iska daga bakinsa da sauri ta d’ago daga abinda take tabi bayansa da kallo tana tuno gamuwarta dashi tana sake jin wani sonshi na shigarta amman shi ko kad’an bata hango sausauci daga garesa ba har yanzu yana Kan nashi kudirin na rashin sonta kuma ta tabbatarwa kanta da wahala ya sota din dan bata hangowa kanta dalili ko abinda zai sanya shi nemanta ba koda zasu shekara dubu a haka ne , ita yanzu kanta take tausayawa dan duk ranar daya fahimci ya kusancenta wanda itace silar faruwar haka ta kade .”

Mikewa tayi da sauri tun kafin ya kai ga hawa sama ta sha gabansa tana masa sannu da zuwa tare da qoqarin amsar jakar hannunsa ,wani kallo ya d’auketa dashi tun daga sama har qasa sannan yaja tsaki “meye haka ?ya fad’a a tsawace “sannu da zuwa nayi maka sannan ka kawo jakar na kai maka d’aki wani tsaki yaja “kina da matsala wallahi wai sau nawa zan nuna miki bana son duk wani abinda zai had’a ni dake ?sau babu adadi “ ta bashi amsa da haka tana kallon cikin idanunshi “okay tsayawa matsayinki ne bazakiyi ba kome ?Ko d’aya wannan hakin daya rataya a wuyana ne kaga dole na sauke kallonta yayi kawai sannan ya cigaba da magana “wad’an nan kayan na jikinki da wanda kika saka last week kar na qara ganin kin sashi acikin gidan idan ba haka zaki had’u da damuwa yanzu ma kije ki ciresu bana son ganinsu idan ma kina sakasu dani ne kinyi aikin banza dan wallahil azim bazaki dauki hankalina ba saboda bana ganinki a matsayin mace “ yana gama fad’ar haka yabi gefenta ya hau sama.”

ta biyasa ta shiga d’akinsa alokacin yana tsaye a bakin gado ya soma cire kayan jikinsa ta cikin madubi ya hangota tsaye still da kayan da yace ta cire tsaki yaja yayi cilli da kayan daya cire ya shige bathroom fitsari yayi ya fito ya kwanta flat akan katifa yana sauke numfashi tare da runtse idanunshi dan wani irin ciwo kanshi Ke masa wanda ya rasa dalili tun last week yake fama dashi ahankali bacci ya fara fixgarsa , cikin sand’a ta shige bayin ta had’a masa ruwan wanka ta fito domin had’a masa coffe dinsa na gado baccin minti goma yayi ya mike ya fad’a bayi yana shirin hada ruwan wanka tsayawa yayi cike da tunani bai yi mamaki ba dan yasan aikinta ne ,haka take masa a duk sanda ta samu damar shigowa d’akinsa . ya sanya hannunsa cikin ruwan babu shiri ya shiga dan ruwan yayi masa yadda yake so dan har wani qamshi yake bai bata lokaci ba ya shige bathtube ya kwanta luf aciki kamar wani qaramin yaro dumin ruwan na ratsashi ahankali gajiyar jikinsa ke warwarewa yayinda acan bedrom dinsa maryam tuni ta hau tattara kayan daya cire ta kai inda yake ajiyewa ta sake gyara masa dakin ta feshe da air freshener .”

Shiru yayi kwance acikin ruwan yana tunanin irin qoqarinta garesa duk duniya a yanzu bayan sweetheart dinsa tafi kowa sanin abinda yake so sannan tana iyakar qoqarinta akanshi sai dai bai san dalilin da har yanzu zuciyarsa ta qasa amincewa daita ba ,zuciyarsa tashiga wasi wasi anya bazai hakura da mafarkinsa ya rungume qaddararsa ba tunda ya rasa mafarkinsa ?hisham ya hakura ya rungume qaddararsa suna zaune lafiya ,daidai gwargwado yarinyar tana binsa tana masa biyayya tana jin tsoronsa wanda abinda yafi buqata kenan ga matar aurensa.”

idanunshi ya daga ya kalli saman bayin “karka kuskura ka karbi wannan yarinyar yanzu ta yaya zata nuna irin wannan matar a idon duniya matsayin matarka ?mace sam babu tsari mace kamar ba halitta mutane ba wannan yarinyar kad’an ya rage bata zamo wada ba .tunani ya dinga yi ya dauki wannan ya duba ya ajiye akanta a qarshe yace “ no way Adam you can do that sam sam bata cancata ba kwata kwata ma bawan nan tunani ya kamata ka tsayi ba kai da kake da tafiya agabanka a gobe gara ma ka tafi ko zuciyarka zata samu natsuwa dan yawon ganin ayyukan alkhairinta gareka zai iya sauko da zuciyarka kuma abinda bazaka so faruwarsa ba kenan “ wannan tunanin yasa shi mikewa daga cikin bathtube ba dan ya gama awanni daya saba yi ciki ba ya saba sabulu ya qarasa wanke jikisa ya daura towel ya fito .”

Abakin madubi ya tsaya da niyyar shafa mai yaji ta shigo ta matso kusa dashi zata kai hannunta jikinsa yayi saurin matsawa yana mata wani irin kallo yana mai jin zafi da haushin shishigi irinta bata damu da irin kallon tsanar da yake mata ba ta sake matsoshi wani mugun tsaki yaja yana sake matsawa tare da jin zafi, zuciyarsa na sake tsanarta ya qarasa gefen gadonsa wani abu ya danna a gefen gadon take duk wasu kayan shafe shafensa suka bayyana ya soma dauka daya bayan daya yana amfani dashi tayi taku uku ta tsaya abayansa har yana jin saukar hucin numfashinta ya juyo a fusace tayi saurin ja baya hanyar fita ya nuna mata da yatsan hannunsa yana cewa “wai me yasa baki da zuciya ne ?dole ne ?! nace dole?!! nace banayi banason ganinki a inda nake ki kama kanki mana ko dole sai mun hada inuwa daya dake ?nasani ba dole bane amman ni ina qoqarin sauke hakinka dake wuya ne “nace bana so ,In your life don’t you ever enter this room again idan ba haka ba duk abinda nayi miki kice kika jawowa kanki leave ya sake nuna mata hanyar fita .”

“Shikenan zan fita amman ga flaks din coffe can na kawo maka nasan zaka buqata “oh my goodness god “ya furta yana dafe goshinsa murmushi tayi sannan ta fita tana leka fuskar shi bayan ta fita yaja tsaki sannan ya cigaba da abinda yake byn ya kammala ya fitar da qananun kaya ya saka sanann ya sanya takalmi silifas wanda ya dace da kayan jikinsa a nutse yake saukowa qasa, har yanzu parlour’n shiru yake bata ma cikinsa bai damu ba sai ma dadi yaji da bai tarar daita ,tunanin abinda zai sakawa cikinsa yake dan tun safe zuwa yanzu bai ci komai ba
hankali ya samu waje ya zauan yana kiran daya daga cikin masu tsaronsa byn ya dauka yace a turo masa musa domin samo masa abinda zai ci .”cikin kankanin loaci musa yayi knocking ya bashi izinin ya shigo ya fad’a masa abinda yake so ya ciro wallet dinsa, fararen sababbin yan dubu dubu guda goma shabiyar ya mika masa ya juya ya fita da sauri shi kuma ya mike akan kujera ya kwanta ya daura hannunsa daya akan cikinsa yana shafa lafaffen cikinsa .”
Chapter 55 · 0% Book details