← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 102

Sashe 20

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a kallon da yake mata yana iya ganin yadda qirjinta ke bugawa da sauri wanda hakan ke tabbatar masa da tsananin tsoronsa da take ji ne ,wannan ne kawai abinda yake d’an so daga gareta bayan shi babu komai ,ta koina bai ga ta yadda zai sota ba bare har suyi rayuwar aure daita .”tsaki yaja tare da d’auke kanshi yana cewa “minti d’aya!minti d’aya kawai na baki ki tattara ki bar nan kuma daga yau karki sake na shigo parlour’n nan na d’aura kwayar idanuna akanki dan bana son ganinki “me nace ?ya tmbyeta yana watsa mata harara “.

“kar na sake ka shigo parlour’n nan ka d’aura kwayar idanunka akaina dan baka son ganina “ta fad’a idanunta na cikowa da ruwa hawayen tausayin kanta “good idan kuma kin isa ki fad’a ki janyo wa kanki massefa dan wallahi matsawar sweetheart ta sake zuwa gidan nan da wata matsala na rantse da girman allah sai na kawo karshen auren nan bayan na gana miki azaba mai rad’ad’in “.ya fad’a cikin zafin rai.”
“bazan ..”! shut up nonsense girl kawai bar nan yanzu kafin na sauya miki kamani guntuwa kawai mara fasali ina magana kina magana sa’anki ne ?.”

da sauri ta d’auki basket din da babbar kula da qarami yake ciki ta nufi hanyar kitchen ,ajiyar zuciya ta sauke bayan ta shiga kitchen din tasa hannu ta share hawayenta “wani irin mutun né shi da bai da imani haka ?”sam sam zuciyarsa bata gajiya da fad’ar bakaken maganganu , gabad’aya ko cikaken minti biyar bai yi da shigowa gidan ba har ya hargitsa mata lissafi .“Oh ni maryam ta yaya zan iya shawo Kan mutumin nan bare na samu kulawar sa ?ya Allah kasan yadda ka jarabeni da soyayyarsa ya allah shima ka jarabesa da soyayyata ko dan yaji yadda nake ji akanshi “ta fad’a a fili tana neman inda zata juye abinci “.

“zaman uban me kike yi aciki ?”ammmm uhmm gani nan fitowa ,ta samu wani kwanon silver ta juye abincin haka ma stew din ta bud’e fridge ta saka bata tsaya wanke kulalin ba ta fito da sauri ta d’auki plet din abinci data fara ci tayi d’akinta tana sauke numfashi .”a natse ya haura sama ya shiga d’akinshi bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwa ya jima ruwa na sauka akanshi sannan ya fito yazo ya sauya kaya marasa nauyi ya dawo parlour’n kasa ya zauna tare da d’aukar remut ya canza channel zuwa na labarai yana cewa “useless girl kawai babu abinda tasani sani sai kallon abinda bazata samu ba .”

bayan kamar minti goma yaji cikinsa ya fara masa zafi alamun yana bukatar ya saka masa wani abu .”
Wayarsa ya d’auka ya kira d’aya daga cikin masu tsaronsa a gaugauce sale adamu ya qaraso bakin kofar shigowa ya tsaya yana neman izini shigowa “may i coming sir”coming! ya fad’a batare da ya kalli kofar ba sale adamu ya shigo bakinsa d’auke da sallama kasancewarsa muslim ne “ina bukatar abinci da sigari “okay sir” ya fad’a masa inda yake bukatar yayi masa order din abinci sannan ya mike ya sake komawa d’akinsa bai jima ba ya sauko ya zauna ya mika masa kudi yana fad’a masa irin abinci da yake bukata “cike da girmamawa sale adamu ya amsa ya juya ya fice daga parlour’n .”

Tsakanin gidan da wajen siyar da abinci babu wani nisa shiyasa bai wani jima ba ya dawo a natse ya turo kofar ya shigo dan yasan halin mai gidansa baya son yawon kwaramniyya ,ahankali ya maida kofar ya rufe , wanda tuni shi ata idanunshi a runtse suke yana tunanin mami yana sake jin aransa kamar bai kyauta mata ba ,ko zata iya runtsawa yau “?shi kanshi idan ya tuna furucinsa gareta yana jin fad’uwar gaba mai tsanani , yana jin ciwo sosai aransa, idan d’an daya haifa ne yayi masa abinda yayiwa mahaifiyarsa yau ya zai ji ?ya tmbyi kanshi .

Cike da girmamawa sale adamu ya ajiye ledodin daya shigo dashi akan dogon kujerar din dake gabansa yana cewa “sir gashi na siyo duk abinda ka bukata” kanshi kawai ya iya gyada masa ,sale adamu ya juya ya fice ATA ya sauke idanushi akan ledodi kafin ahankali ya janyo ya fara bud’ewa “yaushe rabonsa yaci abinci daga waje ?”matsawar yana qasar abincin mahaifiyarsa yake ci amman gashi yau sanadiyyar auren maryam zai koma cin abinci daga waje.”tsaki ya ja sannan ya bud’e robar abinci inda idanunshi ya soma cin karo da shimkafa ‘yar waje da gasashiyar kaza ya fito da robar fresh milk dana ruwan tataccen inibi .

a natse ya soma ci yana korawa da ruwan inibi kusan kazar kawai ya iya ci da ruwan ininbi da fresh milk bayan ya gama ya kunna sigari ya sha iya shansa ya mike ya rufe koina ya haye sama .”yana shiga d’akin ya cire kayan jikinsa ya saura daga shi sai qaramin plan pant ya kwanta flat akan katifa yana kallon saman d’akin yana shafa kwantaccen gargasar gashin qirjinsa dake kwance luf luf ,lokacin da zuciyarsa take son hasko masa fuskar mafarkinsa yayi saurin kawar da hakan ya sako tunanin mahaifiyarsa ,cikin haka wayarsa ta soma ringing bai mike ba har sai data katse aka sake kira sannan ya yunkura ya tashi ya d’auka yana duba screen din wayar sunan mb ya gani yana yawo ya d’auka ya koma ya kwanta .”

Acikin wayarsu da mb ne yake koro masa yadda sukai da mami shima dai fad’a yayi masa sosai tare da nuna masa mahimmancinta arayuwarsa, yayi qoqarin tun abun bai yi tsawo ba yaje ya bata hakuri ya nemi yafiyata, ya jima yana waya dashi saka makon baccin daya soma ji ne yayi masa sallama ya sake mike wa ya kashe wutar d’akin ya bar na bacci guda biyu ya koma ya kwanta ya lullube rabin jikinsa ya runtse idanunshi yana aiyana gobe daga office direct gidan mami za shi ya bata hakuri ko zai samu natsuwar zuciya da kwanciyar hankali .”

Lullube jikinsa Ke da wuya bacci ya d’auke masa cak tamkar wutar nepa sakamakon hoton mafarkinsa bud’e idanushi yayi sosai yana sauke numfashi tare da amboton sunan allah “wani iri juyi yayi ya canza yanayin kwanciyarsa sai dai yasan tunda ya fara da tunanin acikin irin wannan yanayin ba lalle bane bacci ya d’auke shi sai yayi da gaske.” yayi juyi yafi sau d’ari nan da nan ya soma jin haushin kansa ya kamata ya cireta gbdy arayuwarsa ya samu yayi rayuwa kamar kowani mutun” ko kuma ka maye gurbinta da wannan yarinyar ba “ wannan tunanin ya fad’o masa arai abinda bai ta’ba ji cikin ranshi ba Kenan sai a yanzu .”

dogon tsaki yaja yana furta “allah karka nuna min wannna bak’ar ranar .”da dai na sota ai gara na tabbata ina mafarkina ,a qalla ya kwashe sama da wanni biyu kwance ahaka yana juyi da tunani marasa Kan gado ,gabansa kuwa banda fad’uwa babu abinda yake ya kasa runtsawa aiko haushi ya ishesa tunawa da yayi idan fa bai samu isashen bacci ba alokacin zai samu matsala gobe a office .”ya sake runtse idanushi ko bacci zai daukeshi amman still dai abinda baya son gani shi yake gani.”

Ya bud’e idanunshi still dai mafarkinsa yake gani live tana kusanto inda yake ahankali ya mike tsaye ya sauko daga Kan gadon ya kunna wutan d’akin ya d’auki gajere wondo daya cire iya cinya iya ya saka ya fito daga d’akinsa ya sauko kasa ya zauna .”
ya d’auki kwalin sigari ya bud’e ya zari kara d’aya ya kai bakinsa ya kunna ya fara zuqa yana fitar da hayaki ta hanci ta baki nan da nan kwayar idanunshi ya canza ya dinga lumlumshe idanu alamun bacci ,ya gyara ya kwanta akan kujera mai zaman mutun uku ya dafe goshinsa yana karonto duk wata addua da ya iya ,cikin ikon allah bacci yayi awon gaba dashi .”

Kishin ruwa ne ya tada maryam daga baccinta ,ta fito daga d’akinta zuwa parlour’n kasa mutun ta gani kwance hannunsa d’aya a daidai saman marasarsa yayinda d’ayan hannun kuma ya dafe goshinsa dashi, batayi tsammanin ganinsa ba dan hk ahankali ta dinga takawa har ta qaraso garesa ta tsura masa ido kawai tana kallon yadda yake sauke numfashi ahankali.”ganinsa haka yayi matukar burgeta, ta dinga jin wani iri yanayi a sansar jikinta,numfashi ta sauke ta kalli center table din gabansa idanunta ya sauka akan kwalin sigari wani numfashi ta sauke aranta tace “dole haukanka yayi over wani abun ma ba acikin hayacinka kake yi ba .”

Ahankali ta shiga tattara komai dake kan table din ta nufi kitchen na zubar ashara ta zubar wanda har da kwalin sigarinsa da yayi saura, fresh milk dinsa tasa masa a fridge ta dawo cikin sand’a cike da tsoro ta durkushe gabansa tana kallon kyakkyawar fuskarsa a duk yanayin da yake kyau yake yi wani abu ta dinga yana fizgarta akanshi har bata san sanda ta kai hannunta saman faffad’an qirjinsa ba ahankali taji yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi kusan minti biyu tayi durkushe amman bai motsa ba tasan baccinsa yayi nauyi .”

Ahankali ta soma shafa qirjinsa zuwa kasan marasa dake shafe tamkar baya cin abinci , idanuta tayi kasa dasu bata tsaya akoina ba sai daidai jijiyarsa dake mike acikin wondo ‘tai shiru tana qarewa halittarsa kallo tsab “kai ata duniya ne komai nashi mai kyau da tsari ne cikakken nmj ne har da qari hakika tayi sa’ar samu kyakkyawan miji fatanta allah yabi bayanta ya juyo da hankalinsa gareta su rayu cikin farinciki.” ta lumshe idanunta tana sauke wani zazzafan numfashi da sauri sauri hannunta na rawa ta d’aura saman qirjinsa daidai nipples dinsa sai da yayi wata irin zabura kad’an wanda yasa mryam saurin d’auke hannunta tana qoqarin guduwa ya koma ya gyaya kwanaciya ya cigaba da baccinsa .”
Chapter 20 · 0% Book details