← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 102

Sashe 82

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiru tayi kafin ahankali cikin sanyin jiki ta juya ta shige toilet ta d'auro alwala ta fito ta tada sallah a natse yana zaune yana kallonta yana waya ,ganin har ta idar da sallah bai tashi ba bare shima  yayi tunanin ya tashi yayi sallar  yasa  tayi zaton ko ya  manta daita acikin office din ne hakan yasa ahankali ta matso kusa dashi ta motsa labbanta"sir abani aikin da zanyi bani da ishashen lokaci da gefen idanunsa ya kalleta a d'age sannan muryarsa ta biyo baya  a dake "kece kika zana ni? muryarta a sanyaye tace "eh nice sir !kinsan ko ni waye ?"shiru tayi har kusan mintuna goma tana nazarin maganarsa sannan cike da girmamawa tace "eh sir !
"Waye ni ?ya sake tmbyrta a dake tamkar bashi yayi maganar ba "kai ne shararren dan kasuwan nan  da kasar nan dama duniya gabad'aya take ji dashi "tana gama fad'ar ya juyo a matuqar fusace ya fuskaanceta yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "shine dan iskanci kamfanina ya  buqaci yin aiki dake amman kikayi rejecting?ya qarasa maganar a matukar tsawace yana zare mata idanunshi .”

nan da nan hankalinta yayi matseefar tashi tayi saurin matsawa baya jikinta na kyarma "aikin banza kawai yanzu haka ke din ba diyar kowa bace amman kin d'auki girman kan tsiya kin d'aura wa kanki nonsense" yana gama fad'ar haka ya mike ya barta tsaye sake da baki "nice nonsense? ta tambayi kanta cike da mamaki jin abinda ya fad'a mata “nonsense!ta sake maimaitawa a fili tana mai jin d’acin kalmar domin tunda take ba’a ta’ba dangantata da kalmar ba .tana kallonsa  ya nufi wani  d'aki tana mai jin wani irin tuttukin bakinciki tare da damuwa mai tarin yawa har ya tura kofar zai shiga sai kuma yaja ya tsaya yana jan tsaki "give me ten minutes "
yana gama fad'ar haka ya qarasa shigewa .”
runtse  idanunta tayi "wannan kuma wani irin sabon salon wulakanci da 'bata lokaci né ? ya kuwa san me ake kira da zane ?"abu ne da yake bukatar isashen  lokaci "ita bama kanta  take ji ba kamar yaya sadam mutumin daya sadaukar da farincikinsa ya biyota cike da zafin zuciya ta juya zata fita daga office din sai ga mr segun , ya tsaidaita yana cewa  "ina zuwa kuma ?zan wuce ne dan bana tunanin aikin nan zai yuwu "calm down madam  ki samu natsuwa kiyi abinda ya kawoki baqaramin sa'a kika taka ba da mai gida ya bukaci yin aiki dake "yana 'bata min lokaci gashi tare da mijina muke "nasani yanzu me yace ko tunda na fita bai yi magana dake ba ?"Yayi a qarshe  wai na bashi ten minutes ."tayi mgnr kamar zatayi kuka "ok kiyi hakuri ki bashi lokacin dayace kin 'bata sama da awa acikin office din nan sai mintuna goma né kawai zai gagara watakilla ma bazaki yi aikin a yau ba ,zai baki ne kije gida kiyi idan kin gama sai  ki kawo cike da jan hankali ya dinga karfafa mata zuciyarta  dan haka ta cigaba da tsayuwar jiran ATA  ."

kusan mintuna goma sha ya d'auka sai gashi ya fito tare da furta "kika ce kice kika zana ni? Kamar tace masa a'a dan taga abun nasa akwai rainin hankali ciki .amman sai ta tsinci kanta da jin tsoro dan haka ta maida kwayar idanunta ta lumshe masa tana wasa da agogon tsarka hannunta wanda ya qara wa zanen lallenta kyau ,lallen yabi da wani shu'umin kallo tun da yake bai ta'ba ganin zanen lallen da yayi masa kyau har ya d'auki hankalinsa ba sai nata yaji kamar ya kamo yatsun hannunta ,ya d'ago idanunshi a natse ya kalli fuskarta nan da nan  idanunsu ya tsarke cikin juna wannan karon sauri cire kwayar idanunta cikin nashi tayi tana mai kawar da fuskarta gefe tare da danne bugun zuciyarta "shi kuwa wani yanayi ya tsinci kanshi ciki mai sarkakkiya da wuyar misaltuwa sakamakon idanunsu da suka sake tsarkewa cikin juna abinda ya lura atattare daita itama tana da jin kai da miskilanci"a natse ya sake bin zanen lallenta da kallo wani irin kallo ta watsa masa gabanta na fad'uwa wanda ta rasa dalilin jin haka ."

Ahankali ya samu waje akan  kujerun kushin dake office din  ya zauna batare daya bata umarnin zama ba  "bata zauna ba sai ma idanunta data tsura masa tana kallonsa tana sauke numfashi dan itama taci alwashin bazata yi mgn ba har sai yagaji dan kansa yayi . abinda batasani ba shi  ko ajikin ATA da zasu  kwana  a haka ma  bazai damu ba abinda yasani ne ba zai barta taje koina ba har sai tayi masa abinda yake buqata daga gareta ."ya lumshe tsumammun idanunshi yana jijiga kafarsa d'aya yana jira daga gareta ."a qalla sun kusan minti talatin yana zaune ita da segun suna  tsaye ta kalli agogon dake d'aure a hannunta a karo na kusan biyar a kasan ranta taja qaramin tsaki bata san me ya janyota zuwa wannan aiki ba nan take kwakwaluwarta ta shiga aikin neman mata mafuta ."kafin ahankali ta samo zance zuci"maryama dole ki ajiye komai ki  qarasa gabansa Kiyi masa magana idan aikin nan zai yuwu ayi idan bazai yuwu ba ya sallameki ki kama gabanki tun kafin hakurin mijinki ya qare"da sanyi jiki take qarasowa zuwa inda yake ahankali ahankali har ta iso ta zauna a kujerar dake facing dinsa "wani irin zane  zanyi "? tayi tmbyr cike da sanyi murya "ahankali ya motsa lip's dinsa "ina kayan aikinki ?da hanzari ta bud'e jakar kayan aikinta   ta fito da kayan aikinta tare da janyo kujerar gabanta zata ajiye ta jiyo sautin muryarsa "ba'a nan zakiyi ba” ya fad'a tare da mikewa tsaye "biyoni ! "

fitowa sukai daga office din yana gaba tana biye dashi haka ma segun  yayinda gbdy hankalinta ya rabu gida biyu wani yana gurin mijinta wani yana gurin ATA  ."wani office ya shiga daita kai tsaye  gaban wani farin baod yaja ya tsaya tare da jingina jikinsa da bango segun yayi saurin  janyo kujeru guda biyu daya a gaban baod din dazaayi zane  d'aya kuma a inda ATA zai zauna "sir ka zauna ! ya zauna tare da daura kafarsa d'aya akan d'aya jiki a sanyaye  maryama ta zauna  tana jiransa sai daya gama shan kamshinsa sannna ya sallami segu ya fara mata bayani  tana jin ya fara magana ta d'aura hannunta akan boad ta fara fidda kyakkyawar shep din jikin zanen da yake buqata , yana mata bayani tana zanawa lokacin data zana karan hancinta taji wani mummunar tsoro ya shigeta cak ta tsaya ta kasa cigaba da zanen da take ta tsurawa baod din gabanta ido kwaayr idanunta ta zana da hancinta har ma da yanayin jikinta babu abinda yazo zuciyarta kamar zanenta data gani a office din m . malik “ nan da nan gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta.shi kuwa gyara zamansa yayi sosai yana kallon zanen lallen hannunta da yadda take tafiyar da aikinta bai san ya'akayi ba yaji saukar hannunsa akan hannunta yana shafawa ."

Cikin gigita gangan jikinta ya kama rawa wanda  yasa ATA ya dawo haiyacinsa sai dai ya kasa d'auke hannunsa ajikinta da kwayar idanunshi wani irin tsoro da matsanancin firgici ATA  yaga ya bayyana afuskar maryama ,yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa, cikin sanyin jiki ta sabule hannunta cikin bacin rai  tace "meye haka ?"dan allah aiki nazo yi banason irin
wannan wasan iskanci  mai barazana ga rayuwata wannan ya zamo karo na farko da qarshe karka sake kuskuren sake kai hannunka jikinta "ta fad’a tana jan tsaki" ajiyar zuciya ya sauke tare da kafa mata tsumammun idanunsa cikin sayin murya yace "look at me “ta kallesa Kmr yadda ya buqata  babu wasa acikin kwayar idanunshi   "Kinga nayi miki kama da dan iska ?sosai kuwa dan gashi naga alama daga zuwa aiki sai ka bige da kai hannunka jikina batare da kayi laakari da ni din matar aure bace ko kuwa budurwa bace ".hakan nan yaji ya tsinci kanshi da adduar allah yasa single ce ba matar aure ba  ya sake kai hannunsa tsintsiyar hannunta tayi saurin zare hannunta har agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta ya zame cikin nashi “wai meye haka dan allah nifa matar aure ce kuma tare da mijina nazo aikin nan “ta fad'a hankalinta a matukar tashe shiru yayi yana qare mata kallo qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin  karfi wanda baya jin haka akan kowace mace sai akan mafarkinsa.”

ahankali ya motsa labbansa "ko zan iya ganin fuskarki ?"ya tmbyeta yana qara gyara zamansa
"no !ta bashi amsa a matukar tsorace ya sauke numfashi tare da mikewa tsaye ta sake ja baya tana cewa "karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba  ganin tana nema ta fice daga hayyacinta ya sanyashi kamota  hadi da zaunar da ita "lokacin daya kamota wani irin socking ne ya ziyarci zuciya dama gangar jikinsa nan take bugawar da zuciyarsa take ta qaru fiyye da kaida sai dai ya kasa magana a fili sai a zuci "ki natsu wallahi babu abinda zan miki ni kaina bansan meke damuna ba yau , tun da kika kasance tare dani naji komai nawa ya sauya .”
Yayi shiru tare da tsura mata ido ita kuwa banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi, neman hanyar guduwa take daga garesa ."yayinda wasu irin hawayene masu azabar zafi suka taru a kurmin idanunta "wallahi ka cuceni tun da nake babu wani nmj daya ta'ba kai hannunsa jikina tun ina matsayin budurwa sai yau dana kasance mallakin wani  tana gama fad’ar haka ta   fashe da wani irin kuka "okay ki zauna ki qarasa min aikina na sallameki and ki yafe min bisa kuskurena kafin ya gama mgnrsa har ta soma tattara  kayan aikinta ta zuba cikin jaka ta fice da sauri ."da sauri ya fito ya  biyota yana kiranta "ke!!!
Chapter 82 · 0% Book details