← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 102

Sashe 32

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai sadam kalleni nan  ya d'ago kwayar idanunshi da kyar ya kalli Aunty fati  "karka boye min komai sadam kasan matsayinka a wajena ina sonka fiyye da ya'yan cikina  nan kuma jikin ummah ya fara yin sanyi ,"nan ji  duk abinda mahaifiyarka ta fad'a amman ina son naji gskyar magana daga  bakinka ,da gaske ne sadam kana son auren maryama"?  ya runtse idanunshi gam yana jin wani sabon tashin hankali  na ta'ba zuciyarsa da kwalkwaluwarsa sai data sake tmbyrsa sannan ya bude idanunshi ya kalli mahaifiyarsa dake tsaye cikin tashin hankali tana dubansa ,a yanayin yadda take kallonsa bazai iya kunyatata a bayyanan nasi ba".

"kai nake sauraro sadam wallahi da gaske zan iya bar maka maryama na nema muktar wata matukar kana sonta " jikin ummah ya sake yin dan tasan akwai soyayya a tsakaninsu ,"kace wani abu "da gaske ne aunty ?ya fad'a cikin wata irin murya mai cike da tsananin tashin hankali "aunty salma ta zaro ido tana cewa "kai wallahi aunty fati karya ne , babu wata soyayya a tsananinsu "kinga salma magana ta qare sadam nawa ne koda karya ne tunda ya amsa da bakinsa bani da ja domin soyayyar sa dabam ce acikin zuciyata "shiru aunty salma tayi dan ta dade dasanin son da take wa mahaifinsa ne ya juye kanshi  .dariyar mugunta aunty salma tayi ta   juya ta koma bangarenta abun bai mata dadi ba dan bata son maryama ta riga ya'yanta aure  amman zata yi iya yinta taga ya'yanta sun rigata aure ita da take da suruki kamar yusuf me zai dameta da wani  sadam gashi  ga dukkanin alamun dole akayi wa sadam din zai aureta."

aunty fati tace" sadam d'ana ina maka fatan alkhairi suna gama fadar haka suka bar wajen zuwa bangaren aunty hassana suna shiga aunty hassana tace "yanzu ke kin yarda da wannan tsarin"?nasan karya ne dole akayi masa amman tunda ta zabi haka ki zuba ido Kiyi kallon abinda zai biyo baya da wannan maganar suka kawo karshen zance suka shiga wata ."maryama na  zaune cikin  halin tashin hankali umma ta shigo parlour'n tana ganin ummah ta mike ta  rungumeta tana kuka "ummah me nayiwa su aunty fati ?"me  zanyi  su soni  ?wallahi banason muktar ki taimakeni ummah kar a d'aura auren nan   laifin me nayi masu ummah ?ina ta  bawa zuciyata hakurin  rayuwa dasu, amman kullum burinsu suga bayana ."ta karashe mgnr tana kuka."

"ki qara  hakuri da kowa da komai  akan wanda kikeyi maryama rayuwarki  qaddara ce zuwa yanzu ya kamata ace kin saba da qaddararki karta dinga baki tsoro "wallahi ummah  jarabawa bata bani tsoro saboda na maida alamarina zuwa ga allah "yauwa abinda nake son ji kenan kowa ce  rayuwata cike take da  lullubali  da qaddara kuma sai allah yana sonka yake jarabaka domin yaga karfin imaninka idan kuma akace haka dole sai ka shirya, jarabawa ko ta class ce yaya kike jinta bare jarabawa daga allah? fatana allah ya bamu ikon cinye jarabawa ."ta fad'a tana shafa bayanta tana jin fad'uwar gaba ."tana Tunanin yadda zata shigo mata da zance sadam  taji sautin muryar maryama tana cewa "ni dai ummah kisa abar maganar muktar ke kad'ai ce nake da yakinin zata min wannan gatan ."

ummah  ta zareta ajikinta ta kamo fuskar maryama da hannuwanta duka tana  kallon fuskarta  tace "babu wani muktar da zaki aura na yanke shawarar zaki auri yayanki sadam, maryama ta zaro idanu  tana duban umma cike da matsanamcin mamaki "yaya sadam kuma  ummah ?"a matukar rikice  ummah tace "Eh ko baki sonshi."ahankali ta shiga girgiza mata kai domin dai tasan  ko giya ta sha bazata iya furta hakan gareta ba ,bare kuma tasan
tayi hakan ne dan yantota daga hannunsu aunty fati ."ai ko bata son yaya sadam ta karba kuma ta amince sai dai fargaban yadda yaya sadam din zai karbeta muryarta a raunane tace "ummah kina tunanin yaya sadam din zai  amince   ?

"ya ma amince  maryama "kuka ta fashe dashi  mai karfi "shikenan mafarkinta ya tabbata"ya allah kabani kwarin gwiwar cinye jarabawar da duk zaka min "alhamdulillah alhamdulillah shine kawai abinda umma taji yana fitowa daga bakinta "allah ne abun godiya maryama babu abinda zai biyo bayan wannan auren sai alkhari, karshen wahalarki yazo ta fad'a tana sake  rungumeta ajikinta " aunty ta qaraso ta zauna kasa kusa da kafafuwan ummah "ban san da wace irin kalmar godiya zanyi amfani dashi wajen gode miki ba amman zan zabi wannan kalmar allah yay miki sakamakon da gidan aljana "na gode na gode !!sai kuka ya kufce mata daga maryama har Aunty  suka saka ummah tsakiya suna mata kuka ."

koda habib ya dawo yaji hukuncin ummah abun yayi masa dadi sosai  dan gara sadam sau million akan wani muktar fatan alkhairi yayi yana tmbyr aunty maryama .""Tana d'aki  !" ta fad'a atakaice tana sauke numfashi a daki ya iske maryama kwance  akan katifa tayi kuka har idanunta sun kunbura tana tunanin  yadda qaddarori suka yita zuwa mata daki daki akan aurenta a she tana tare da mijinta bata sani ba "ya zauna kusa daita  yana kiran sunanta "heartbeat ".ta sauke numfashi tana dubansa da kunburarrun idanunta "bakiji dadin hukuncinsu umma ba ko ?ta langwabar da kanta kawai  batare da tace komai ba "heartbeat idan da wani aka baki zance Aa amman yaya sadam dabam ne karki ce aa bazaki samu kamarsa ba "

"kai ma ka amince dashi  ?sosai kuwa dan mutumin kirki ne kuma yana duk wasu quality's da zaa so shi ta sakar masa murmushi  wanda ya bayyana wushiriyarta sama da kasa tana gyara kwanciyarta
ta jingina bayanta da abun gado ta janyo pillow ta rungume tana jin wani nauyi a qirjinta"bana jin son yaya sadam  ko kad'an acikin raina amman bani option zan rayu dashi muddin rai "yayi shiru kawai yana kallonta cike da tausayawa dan bai san me zai sake cewa ba ,domin farincikinta farincikinsa ne haka zalika damuwarta damuwarsa ne zai sake magana ta katsesa ta hanyar cewa "karka ce komai after dad tunda har ka amince  daman kai kawai nake jira naji raayinka tana gama fadar haka ta sauko "muje parlour'n muci abinci ta riko hannunsa binta kawai yake jikinsa a sanyaye ."

*******

Tun bayan da ummah ta furta   maganar aureta da yaya sadam habib  bai zauna ba ya shiga buga bugan neman aiki karfi daga wannan kamfani zuwa wannan duk kuma saboda ita da mahaifiyarsu ne daman da karatu da kwallon kafa ya dogara dan yana d'an  samu a buga kwallon kafa amman ba wani samu sosai ba dan kudin ba wani kudin azo agani bane amman babu laifi yana toshe  masu wata kafar dan  hatta mashin din da yake dashi yanzu  da dan kudin da yake samu ya siya ."matslar dai   ba koda yaushe ake samu  ba sai a dauki alokaci baa daukesa ba shiyasa yaga gara ya had'a da aikin kamfani ranar da'akayi dashi za'a d'aukesa  a ranar ya samu damar  buga kwallon kafa  zuwa ogun state kenan  ya samu promotion daga  jahar lagos zuwa wata jahar  ."

Adaidai wannan lokacin maryama ta kammala bautar kasa tare da kawarta subai'a babu inda take zuwa tana zaune a gida abinda tafi tsana kenan zaman gida sam a yanzu bata son zaman gidansu  gashi dai tana samun kulawa gata sangarta só qauna soyayya tarairaya daga  mahaifiyarta  haka ma habib sai ummah wacce sanadiyyar sadam yasa yanzu motsin kad'an tana bibiyar me take ciki komai ta samu ita zata  bawa amman zaman gidan baya mata dadi saboda zuciyarta ta rasa abu d'aya wato mai d'ebewa zuciyarta kewa dan gabad'aya tunda akayi maganar aurensu da yaya sadam ta rasa gane kanta dashi karon kashi sadam din sai ma taga ya rage bata kulawar daya saba bata ada can baya ."

****
A hankali ATA ya shiga office dinsa babban ma'akacinsa  mai tantance ma'aikata na  kamfaninsa Z&A na biye dashi  abaya ,ya zauna a mazauninsa yana kallonsa  batare da yace komai ba "good morning sir ? ya gaishesa cike da girmamawa "uhm ! yayi gyara murya kawai alamun yana jinsa  yana maida hankalinsa Kan system "uhm amm  sir ko zan iya magana yanzu "uhm ! ya fad'a a takaice "adadin mutane kimanin dubu dari uku ne suke bukatar aiki a karkahainmu ,sir wannan shekara ko zaa hada da  masu degree ? Ko kuma daga master zuwa sama ne zaa dauka ."?" ka ma da kake maganar daga wani mataki ka  fara aiki ?"sorry sir ya fad'a a tsorace "duk mutumin da aka tabbatar takurdunsa sunyi kyau ayi  masa interview idan ya cancata a d'aukesa ."
"sai  abu na gaba kada a Kuskure akarba'  kwabo duk wani mutun domin samar masa aiki a duba cancanta yana gama magana ya dauke idanunshi akan system zuwa wani bangare dabam  yana cewa fatan" ka fahimta "yes sir sai kuma game da compaing dake kasar  togo sun kira suna bukatar almustapha "me zance masu?" kai komai bazakayi da tunanin kanka ba sai ka tmby ? "am sorry sir"ya juya da sauri ya bar office din ."

Ranar  monday   tun asuba da maryama ta tashi tayi sallah bata koma ta kwanta ba ta soma shirin zuwa wajen interview duk abinda tasan zaa buqata ta had'asu waje d'aya  acikin jakarta hatta kayan da zata saka ta fito dashi sannan ta shiga wanka karfe bakwa  daidai ta gama shirinta ta fito parlour'n ta hango aunty tsaye a kitchen ta qarasa ta rungumeta ta baya "good morning mumy "ta kai hannunta ta shafa gefen fuskarta morning my princess har kin fito ?yes !ta fad'a tana duba agogon dake daure da tsintsiyar hannunta "muje ki karya kafin ki fita "aunty da kin bar breakfast din nan Kiyi min addua kawai" bakince akwai wanda zai tsaya maku  ba ?aunty ta fad'a tana fitowa daga kitchen maryama ta biyo bayanta tana cewa "akwai but bashi zai mana interview ba amman dai ina ji ajikina zamu samu nida subai'a "to Allah yasa a dace "Ameen !ta fad'a a lokacin da wayarta ta d'auki qara ta ciro ta duba tana cewa "aunty subai'a ce ."
Chapter 32 · 0% Book details