← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 102

Sashe 73

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

bata  bar  ɗakin ba  kamar  yanda ya furta  sai   rarrafawa  tayi ta koma  gefen doguwar kujerar   kushin  ƙwaya ɗaya  dake  ɗakin  ta rakuɓe ,  tana kallonsa ya miƙe  ya  shiga bayi batare  daya cire  kayan jikinsa  ba   saukar ruwa a  bayin   yasa  ta fahimci wanka  yake  a hankali  ta rike gefen  kanta dake sara   tana  haɗeye wani ƙululun baƙin ciki  tare da  share  hawayen dake tsiyoyo mata, ta tattara tukunyar tsafin ta kai dakinta ta ajiye ta dawo ɗakinsa ta zauna dan babu in da zata aurenta dashi mutu ka raba ya saketa amman bata saku ba dan tayi imani mami naji zata maidaita."Da mamaki ya fito ya isketa kallon mamaki da naci irin nata yake “zaman me kikewa mutane a d’aki ?” ya faɗa Yana kallonta “babu fa inda zani har sai ka maidani ” wani mugun kallo yayi mata sannan ya ɗauki jug din coffee da zafinsa wanda ta kawo masa bai sha ba ya dawo inda take ya juye mata tsab a jikinta wata razananniyar ƙara  ta saka da sauri ta shiga kakkaɓe rigar dake jikinta  , cikin faɗa wanda bai hana zazzaƙar muryarsa fitowa ba yace. “banace ki bar min ɗakina ba ?” Ya faɗa yana ware mata idanunsa dake cike da bala'i  jikinta na rawa sosai ga kuma zafin coffee da yake ratsa illahirin fatar jikinta  wanda har cikin naman jikinta take jin zafin, babu shiri ta bar masa ɗaki zuwa nata tana zubar da hawaye .”

ranar Maryam bata runtsa ba kuma tayi dauriya domin dai bata kira kowa acikin ahlinsa ba  washe gari kuwa tun da  asuba tabi mota zuwa abuja taso shiga jirgi amma saboda bata da kuɗin jirgi kamar  ta tambayi mami  kuɗin ticket amma tasan hakan zai sa ta gane akwai matsala shiyasa ta shiga motar haya
Tunda suka ɗau hanya  kanta na kife ,rufe ido tayi sosai tana zubar da hawaye masu zafi sannan acikin ranta tana ƙissima yanda zata hana rayuwar adam samun kwanciyar hankali  yadda bata ji dadi agidansa ba bazata bari Ya kawo wata yaji dadin rayuwarsa daita yadda gallazawa rayuwarta wallahi tayi alqawarin sai ya gallazawa duk wacce ta rabesa zatayi komai akan yanke masa duk wani jin dadin rayuwa .” ɓangaren ATA shima tana barin gidan ya bar ƙasar zuwa hollond .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 22

Kwanaki hamsin kenan da ATA yasa anemo masa kwararrun masu zane wanda yayi daidai da sauran sati uku daurin auren maryama da yaya sadam acikin lokacin nan babu abinda maryama take sai zariyar zuwa AGC domin gabatar da zanenta, haka zalika ta saki jikinta sosai da yaya sadam domin ta fara cire rashin son da bata masa tana ta qoqarin dasa soyayyarsa mai karfi acikin zuciyarta ,shima kuma bangarensa yana qoqarin kyautata mata shiyasa a yanzu damuwarta ad’auketa aiki akar ka shin AGC ne .” idan kaga maryama da yaya sadam a yanzu zaka d’auka tun asali masoya ne wadan da suka d’auki tsawon lokaci suna son juna, abu d’aya ne kawai dai har yanzu yake damun zuciyar maryama shine yawon shiru da shiga tunani mai zurfi da yaya sadam din yake ko suna tare ko yana shi kad’ai ko ayita kiransa a waya baya d’auka agabanta wanda ita hakan na damunta, kuma haka nan take ji ajikinta kamar akwai wani abu dake damunsa wanda yake boye mata , tayi iyakar qoqarinta tasan meye damuwarsa amman abun ya cutura domin dai abu d’aya ne kullum yake fad’a mata babu komai al’amuran aiki ne .”

mami na zaune a had’ad’den parlour’nta na farko idanunta na kallon tv yayinda hannunta Ke rike da casbaha tana ja ahankali kira ya shigo wayarta, tasa hannu ta d’auki wayarta tana dubawa sunan d’anuwanta data gani yana yawo a screen din wayar ne yasa tayi saurin kara wayar a kunneta bakinta d’auke da sallama “wani irin mikewa mami tayi jikinta na rawa tare da furta kalma “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagisu aslili shaani kulluhu wala takilni ila nafsin d’urfata’ai “kace yau kwana biyu kenan da faruwar sakin ?ta tambayesa cikin tsananin damuwa da shiga tashin hankali “yayinda cikin tsananin fushi d’an uwanta ya cigaba da sheida mata abinda ya faru .”“wallahi Abdul ban san komai akan sakin nan ba”
ta fad’a jikinta na wani irin ‘bari haka ma zuciyarta
bayan ya katse kiran kuka mami tasa tare da jin wani kullin bakinciki ya tsaya mata a qirji yaki gaba yaki baya wayarta ta lalubo ta soma neman layukansa amman shiru bata shiga dan haka ta kira Amar nan ta samu labarin tafiya yayi zuwa hollond abun yayi mata ciwo fiyye da tunanin mai karatu ammar din ma yana tambayarta ko tana son wani abu amman tuni ta katse kiran .”

batayi sanya a gwiwa ba ta kira ya’yanta a waya ai kuwa washegari gabdayansu suka hallara a gidan cikin tsananin tashin hankali aiko mami tasa masu kuka tana kiran “adamcy zai kasheni shikenan ya zama sila shiga tsakanina da d’anuwana muna zamanmu gwanin sha’awa, kana ganinmu kasan akwai shakuwa da soyayya a tskaninmu, muna ta qoqarin had’a kanmu dana ahlimu, mun rungume juna babu kyarma muna tsananin son juna amman yau sanadiyar adamcy ran d’anuwana ya sosu yayi min abinda bai ta’ba min ba .Abdul ra’uf bai ta’ba min magana cikin fushi ko ‘bacin rai ba sai a jiya “ni zulai na shiga uku nah me yasa na had’a auren nan ?”wallahi dana san abinda zai biyo baya kenan da ban had’a ba dana bar adamcy ya cigaba da rayuwarsa haka babu aure dan duk abinda zai lalata zumuncina da yan’uwana bana qaunarsa”.”

“kiyi hakuri mami ki daina kuka haka Allah ya qaddara kowani bawa da kalar qaddararsa wannna rabon dake tsakaninsu fa idan baa yi auren ba ta ina zaa samu ?inji cewar aunty shahida ,”kuka fa ya zamammin dole abdul’rauf na min biyayya duk abinda nace shi yake yi bai ta’ba sa’bawa umarnina ba "wai mami zaginki yayi ne ko me ?zabiba ta tambayeta “ko d’aya zabiba abdul bazai ta’ba zagina ba amman yayi min magana cikin fushi abinda bai ta’ba min ba sai jiya” nifa na kasa gane abubuwan nan na yaya adam mutun kamar babu tausayi a cikin zuciyarsa gsky mami yakamata ki san yadda za'ayi da yaya ga ciki ga saki dame sister zataji wallahi ni tausayi take ba ya dawo daita kawai .”nana hauwa’u ta qarasa mgnr tana sheshekan kuka aunty shahida ta numfasa kana tace “karki d’aga hankalinki auta kinga kema bake kad’ai bace za'a haukatar dashi bari ya dawo daga hollond lafiya amman dan dolensa ya maidaita ta haihu a gidansa idan ba haka ba wallahi wannan karon zai had’u da tashin hankali da bai ta’ba gani ba “ku dai bi komai a hankali domin dai acikinku babu wanda bai san waye yaya adam ba kusan yafi buqatar rarrashi da lalama muddin da tashin hankali zakuje masa wallahi bazai maku abinda kuke so ba .”

“da mamaki aunty khadija ta kalleta “abinda muke so kuma ke banda ke ?”gsky banda ni abinda kuke so am sorry to say dani yanzu bazan sake goyawa zaman aurensu baya ba ,ya kamata zuwa yanzu abarsu haka kada a takura masa ku kyalesa ya huta idan yayi ra’ayin maidaita da kanshi zai yi idan kuma iyakar zamansu kenan Allah yasa ya zama alkhairi ,sun d’auki lokaci suna tautaunawa a tsakaninsu sai dai zabiba ta tsaya akan raayinta wanda bai yi masu ba har mami .”
Bayan kwana uku ahankali oga ATA yake saukowa daga cikin jirki tare da yaransa mutu biyu kai tsaye in da driver da masu tsaronsa ke jiranshi suka nufa, ya qara kyau aciki kwanaki uku kacal farinsa ya sake fitowa ga cigaba da ya samu da nasarori akan business ,yana sanye da royal blue three piece suit daya daga cikin yarasa na sak'ale da bak'ar jakarsa daka ganshi kaga wayayye wanda yasan duniya ko nace duniya ke damawa dashi, yayinda idan ka kalleshi zaka d'auka d'an shekara talatin da biyar ne amma gaskiyar lamari shekararsa arba'in da wani abu yake, da sauri aka bude masa gidan baya ya shiga ya kame yana shan kamshi daya daga cikin wayoyin ne ta soma ringin ya dauka ya soma magana a natse yana ciccin magani har suka qaraso unguwarsu waya yake bai ji komai ajikinsa ba sai da suka shiga cikin haraban estate dinsu yaji gabanshi ya fad'i sakamakon bai san abinda zai tarar ba amman a kudurtawa ransa komai zai faru sai dai ya faru amman har abada bazai qara zama da mrym ba".
Chapter 73 · 0% Book details