← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 102

Sashe 21

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin ya sauke numfashi tare da d’aura hannuwansa duka sama jijiyarsa ya dafe ,ta sake durkushewa a gabansa ta tsura masa ido “ina sonka adamcyn mami wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba . sonka yayi min mugun kamu I love you my adam, sonka da qaunarka sun yi min kamun da bazan iya fushi da duk wani wulakanci da zaka min ba .”ta sake kai hannunta qirjinsa tana adduar allah yasa kar ya farka ya kamata cike da matsanancin tsoro ta fara shafa qirjinsa tana sauke numfashi .”wani wahallen numfashi ya sauke yana mai jin wani mugun felings a gabad’aya ilahirin jikinsa, ita kanta wani iri ta dinga ji ajikinta tmkr ana jona mata wutar lantarki .”

ta sauke numfashi tana mai matso da bakinta dai dai nashi nan warin sigari ya bugi hancinta amman cikin ikon allah sai lumshe idanunta tayi tana jin dadin shakar kamshin sigari da numfashi shad’e ”
Cike da tsoro ta soma tsotsan lip’s dinsa na kasa tana hura masa numfashinta tana tsotsa lip’s dinsa tana shafa kwantaccen gashin qirjinsa cikin wani irin yanayi ya kai hannunsa d’aya yana shafa sumar kanta yana ma bakinta wani irin sha yana juya harshensa tmkr yana neman wani abu acikin bakinta har ya samu yayi nasarar cafko harshenta ya fara tsotsa cikin kwarewa yana sha yana had’awa da hakoranta da lip’s dinta sosai ata ya dinga sarrafa bakinta cikin rashin sani .”

Allah sarki maryam wani irin farinciki ne da mugun tsoro ne ya shigeta alokacin d’aya dadinta yadda yake sarrafa bakinta tsoronta kuma ya farka ya gansu haka nan da nan dadin take jin yana bin jikinta ta daina jin komai sai tsananin tsoro da fargaba dan tayi imani muddin ya bud’e idanunshi ya ganta ta mutu sai dai wata maryam din ba ita ba bayan tozarci ma sai ya kusan kasheta da duka dan haka cikin tsananin tsoro ta zare bakinta tare da d’auke hannunta a saman qirjinsa tana rawar jiki .”

Shi kuma jin ta zare bakinsa ya fara motsi yana fitar da numfashi da sauri sauri yana neman abinda ya kufce masa ya dawo masa domin shi zatonsa mafarkinsa ne . maryam ta tsura masa ido sosai cikin tsananin tsoro ganin yadda yake fidda numfashi yana damke jijiyarsa da hannuwansa duka qoqarin bud’e idanunshi yake taí saurin juya masa bayanta qirjinta na wani irin luguden bugu “.

Idanunshi ya bud’e da kyar yana jin sauyin yanayi a gbdy ilahirin jikinsa bai ce uhm ba bare uhm illa kallon saman parlour’n da yake batare da yace uffan ba ,cikin yanayi najin fad’uwar gaba ya sauke idanunshi dake cike da bacci akanta duk da baya kawai ya gani amman yasan wacece ko dan mugun gajartata, mamakin ganinta yayi adaidai lokacin da suke tsakar dare” me take yi tsaye ya kai idanunshi ga bangon parlour’n daidai inda agogo yake manne “hudu saura ya tabbatar karshen dare suke ya ‘bata a qalla minti biyar sannan yayi wuf ya mike tsaye yana tafiya da kyar ya isa gabanta ya tsaya idanunshi cike da bacci .”

“Ke me kikeyi anan ?ta tsura masa ido tana kam kame jikinta waje d’aya “ko dai mayya ce ke ?still shiru tayi tana jin mummunar fad’uwar gaba Kmr ta kwasa da gudu ta haye sama “ina miki mgn kinyi min shiru “mayya ce Ke?okay okay !!na fahimta kin tashi rawar dare ne ko ?maganarsa taso bata dariya amman tasan muddin tayi mugun duka ne zai biyo baya “idan ma mayya ce ke sai dai kin cinye kanki da uwarki da ubanki amman ni namana da daci nonsense girl kawai kizo kin wani tsaya wa mutun akai zaki shanye min jini “ya qarasa mgnr yana jan tsaki ya nufi hanyar sama .”

Tabi bayansa da kallo qararrawar zuciyarta na kad’awa fiyye da kaida yana shiga d’akinsa bai koma ya kwanta ba ,ya shiga bathroom yayi wanka dan yana jin jikinsa wani iri ya d’auro alwala ya fito ya saka rigarsa ya tada sallah .”koda ta hau sama ta tsaya bakin kofar d’akinsa ta tura kofar d’akin ahankali a saman abun sallah ta ganshi zaune yana jan casbaha ,ganin zai juyo ta juya da sauri ta shige d’akinta ta kulle ta kwanta tare da qudundune jikinta tana jin feelings dinsa na ratsa lugun da sako na jikinta .”shi kuwa bai koma ya kwanta ba sai da yayi sallolinsa sannan ya koma saman gadonsa ya kwanta bakinsa d’auke da tasbihi ga I bangijinta ahaka bacci mai dadi ya daukesa .”

bai tashi ba sai wajajen karfe tara da minti talatin ya sauko da kyar ya shige bathroom, minti shabiyar tsakani ya turo kofar bathroom ya fito d’aure da towel a kugunsa yayinda jikinsa ke jike da ruwa ya tsaya a gaban mirrow yana goge jikinsa da gefen towel kamar ance ya kalli cikin mirrow ganinta yayi tsaye tana watsa da yatsun hannunta wani dogon tsaki yaja yana d’auke kanshi cike da dakewa da daure fuska tmkr bai ganta ba ya cigaba da goge jikinsa yana mamakin abinda ta shigo yi kamar ba ita yayi wa kyakkyawan warning ba akan zuwa inda yake ba .”

Bayan ya gama goge jikinsa ya shafa lotion ajikinsa ya bude ma ajiyar kayansa ganin haka yasa ta juya masa baya tana mai jin nauyi da fad’uwar gaba
madadin ya d’auki kayansa sai ya gyara daurin towel din kugunsa da kyau yayi taku uku ya qarasa inda take da sauri ta d’auke numfashi sakamakon wata irin damka da taji ta bayan wuyanta “wani razananniyar qara ta saki wanda yasa gbdy gidan ya amsa ,bai tsaya wata wata ba ya jata kiiiiii yayi waje daita bai tsaya akoina ba sai d’akinta yayi wuli daita a tsakar d’aki sauran kad’an gefen idanunta ya bugu da abun gado allah ya kiyaye “dan ubanki me ya shigo dake d’akina “?

ta mike a matukar gigice tana dubansa “ban fad’a miki bana son ganin wannan bazan fuskar taki ba ?ka..ka !! fad’a min daman ..”tass tasss taji ya d’auke da wasu maruka masu kyau sai da wani haske ya gilma acikin kwayar idanunta ta fashe da kuka tana dafe kuncinta“idan kikayi qoqarin shiga rayuwata zaki sha wahala a hannuna domin kuwa zan bata miki fuska ta hanyar canza miki kamani , tsay a way from me I don’t want to see your face “yana gama fad’ar haka ya juya a matukar fusace ya bar d’akin .”
Durkushewa tayi a wajen tana fashewa da kuka mai tsanani “ta rasa wani irin tsana ya adam yayi mata wani irin kuka take saboda ciwon abinda yake mata ,ta share hawayenta alokacin da taji motsin rufe kofar d’akinsa “.

Ahankali taji taku takalminsa yana taka step wanda duk takun da yayi daidai yake da bugun zuciyarta jikinta a sanyaye ta mike ta soma d’aga kafafunta tana zubar da hawaye har ta kai bakin kofa taji motsin takunsa alamun yana haurowa da hanzari ta koma da sauri tana jin fad’uwar gaba tsayuwarsa ta gani a bakin kofar yana cewa “Ke ina kwalin sigarina? muryarta cike da in ..ina tace “amm uhm na ..na ..”sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa mgnr dan tasan tana fad’a masa ta zubar a shara sai ta gane bata da wayo ya qara taku biyu ya shigo cikin d’akin sosai yana mata wani irin mugun kallo wanda yasa hantar cikinta kad’awa “ina kwalin sigarina ?akaro biyu don’t let me repeat my self .”

“Na ..na zubar a shara “ta fad’a hawaye na ganga rowa bisa kuncinta “what !? ya fad’a a matukar tsawace tayi baya da sauri ta manne da bangon d’akin tana bashi hakuri “kayi hakuri dan allah .”“sigarin nawa kika zubar ashara saboda Ke dakikiya ce ?bansan cewar baka gama dashi ba amman kayi hakuri “ numfashi ya fesar tare da rike kugunsa ya taka ya isa bakin window ya yaye labulan window yana kallon haraban gidan masu tsaronsa ne suke shawagi da alamun sun gama shi kawai suke jira ya saki labule da karfi wanda yasa maryam ta firgita cikinta ya duri ruwa. fuskarsa a murtuke yace “ki tabbatar kin nemo min sigarina kafin na dawo gidan nan idan ba haka ba wallahi wallahi ki kuka da kanki “yana fita kamfani ya nufa .”

cikin hanzari suna isa ya fito.”kai tsaye ya d’auki hanyar comfrence room domin wata gagarumar matsala dake son kunno kai cikin kasuwancinsa kuma tunda ya sanarwa P.A dinsa yasan by this time shi kad’ai ake jira yana shiga ya iske kowa kamar yadda yayi expecting har ma da ammar da hisham cike da girmamawa manya ma’aikatan da dake zaune suka dinga gaishesa tare da qoqarin kashe wayoyinsu dan sun san dokarsa idan yana magana baya son jin motsin kowa bare qarar waya ya mikawa ammar hannu batare da ya kalli inda hisham yake ba shima kuma bai kallesa ba .”ya samu waje ya zauna.”

sun dade suna tautaunawa da manyan ma’aikatansa domin kawowa kamfanisa cigaba ahankali P.A dinsa mustapha umar hassan dinsa ya mike ya kawo masa coffe karfe biyu daidai ya sallame kowa shima ya fito tare da ammar suka nufi massalacin dake cikin kamfani yana bawa direbansa umarni cikin harshen tsadadden turancinsa su juya kan motoci fita zai yi da zarar ya fito .”Ina kuma zaka ?zanje naga sweetheart dina “ya fad’a cike da jin fad’uwar gaban da bai san dalili ba”.

a natse suka qarasa wajen yin alwala suna magana kasa kasa ATA yace “share maganar hisham kai bakasan abinda yayi min ba muddin kaga mun dawo kamar da to naga auta kuma naga kwanciyar atare daita bayan sun idar da sallah ammar ya rigasa fitowa ya tsaya acikin wata runfa rungume da hannuwan sa a qirji yana jiran fitowar ata yana tsaye ya hango bayan maryama idanunshi kyam akanta har sanda ATA ya qaraso ya tsaya kusa dashi yana cewa “me ya d’auki hankalinka da kayi concentre haka ?zubin halitta mai kyau nake kallo ”ya bashi amsa da haka kana ya cigaba da magana “ kalli can abokina ka gani tsayuwarta ma kawai abun burgewa ne .”
Chapter 21 · 0% Book details