← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 102

Sashe 49

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dan allah malama bana són munafurci ki daidaita natsuwarki ga waya kuyi magana daita da sauri ta goge hawayenta da hannuwanta duka tana shafa qirjinta dan dawo da natsuwarta sannan ta mika masa hannunta wai kallon banza yayi mata yasa wayar a speaker yana rike da wayar” hello tajiyo sautin muryar mami zuciyarta cike da rauni tace “hello mami ina yini “yauwa maryam lafiya qalau daman dake nake son magana lafiya naji muryarki haka ?ta kalli inda ATA yake ,mugun kallon daya dauketa dashi ne yasa ta dauke kwayar idanunta akanshi , ta kalli cikin wayar “lafiya qalau mami “to mai ya samu wayarki an kiraki bai shiga ?maryam tayi shiru tana jin rauni atare daita “mahaifiyarki tun shekaranjiya take neman layinki ni kuma tun jiya nake kiranki haka ma auta idan akwai damuwa ki fad’a min”.

ta waiga ta kalli ATA dake binta da mugayen idanunshi “adamcy na wajen ne ?”uhm !ta bata amsa atakaice,okay kina jina zan miki tmby idan gsky ne kice “eh! idan karya ne a’a !“Tun daga ranar da abun nan ya faru a tsakaninki da adamcy ya kwana a gidan ?“muryarta na rawa tace “eh !mami tayi shiru can tace mikawa adamcy wayar “ai wayar tana hannunsa “mami ta furta “aa ! cike da tsananin mamaki mami tace “wayar ma bazaka iya bata ba kamar wata mugun abu ?aransa yace”ai ta zarce haka acikin zuciyata amman a fili cewa yayi “ina jinki sweetheart “muje what’sapp tana gama fadar haka ta katse kiran ta kirasa vedio call ido cikin ido suke kallon juna tace “ina maryam take ?”

ya haska mata fuskarta dake kode alamun wahala “maryam natsu ki fad’a min gsky babu abinda zai iya miki me ya sameki duk naga kin dawo wani iri haka “me kuwa zai sameta ?” wai sweetheart mai yasa bakya son zaman lafiya ne ? kin tmbyi yarinyar tace babu komai ,kina son lallai sai ta kirkiro karya ta fad’a miki akaina “Ke dan ubanki meke damunki ? ya fad’a a tsawace ”maryam tayi saurin girgiza kai tana cewa “mami babu komai ! adamcy karka nemi ka raina min hankali maryam fad’a min gsky gani nan zuwa yanzu “a’a mami dan girman allah karki zo wallahi babu abinda yake min kawai dai kwana biyu bana jin dadi ne “wato adamcy dai ka raina ni da gsky “.

“me kuma nayi sweetheart ?“taya yarinya bata da lafiya har tsawon kwanakin nan amman kai daka ajiyeta baka sani ba ?“ wa kenan ya ajiyeta sweetheart ? “inna lillahi! mami ta furta “tô ai maganar gsky ne sweetheart ni ban ajiyeta ba ba kuma zamana take acikin gidan ba, zamanki take dan Ke kike aurenta bani ba “okay haka ma zaka fad’a min ? am sorry sweetheart amman kin dade dasani zamanki take acikin gidan nan “okay har kana sake jaddada min? to wallahi bazaka qara jin dadina ba haka kawai ka dinga ganawa yarinyar mutane azaba laifi ne dan ta rufa maka asiri ta aureka ?“.

“wace azaba kuma sweetheart yarinyar da babu abinda Ke hadani daita, ya kalli maryam Kiyi mata bayani mana kinyi shiru kina kallona da wata munafukar fuskarki ?maryam kam shiru tayi ta tsaya tana kallon fuska mami ,ya sake mata alamar tayi magana akaro na biyu a matukar fusace “Ke kina hauka ne ya buga mata tsawa “ ki bud’e baki mata bayani “Allah babu abinda yake min “ karki sake ki min karya maryam “wai sweetheart me nene haka ne ?ya kalli maryam yana cewa “wallahi idan baki bari ta yarda babu komai ba sai na canza miki kamani, ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali tace “mami dan girman allah ki bar maganar nan ni babu abinda yake min kawai zazzabi dare nake fama dashi kuma walalhi laifina ne ban fad’a masa ba nasan dana fad’a masa zai kai ni hospital ko ya kira min doctor “tana gama fadar haka ta juya kafin mami ta sake cewa wani abu .”

mami tayi shiru tana dubansa ta cikin waya “sweetheart kinyi shiru “me zance adamcy tunda kafi karfina ka rainani ka nuna min ban isa da kai ba duk lokacin da nace ga abinda zakayi bazakayi ba amman wallahi bazanyi kaffara ba muddin ba cigaba da zaman lafiya da maryam a cikin gidan nan ba na rantse da girman allah babu ni babu kai “ki kwantar da hankalinki sweetheart kin ma kusan rasani gabad’aya “bangane na kusan rasaka gabad’aya ba ?“eh mana na zabi mutuwa akan cigaba da rayuwa da wannan munafakar yarinyar akowani lokaci zaki bud’e idanunki baki ki daina ganin adamcynki “bazaka iya aikatawa kanka komai ba kai fa muslimi ne kuma kasan hukunci haka addininance dan haka ka bar maganar nan bana son na sake jin ka fad’a kazo gobe akwai maganar da nake son nayi da kai mai mahimanci,amman dan allah na roki arziki ka bar yarinyar maryam ta samu natsuwa acikin gidan nan “naji !iya abinda ya fad’a kenan sukai sallama.”

Maryam na shiga dakinta ta rushe da kuka tana cikin kuka wutan gidan ya kama sai datayi kuka mai isarta sannna ta janyo wayarta ta jona caji ta fito lokacin baya parlour’n kitchen ta nufa direct aiko taga key makale naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana godewa allah cike da rawar jiki ta kai hannunta tana waigen bayanta babu alamunsa ta zare key daya ta tura cikin rigar nononta sannan ta murd’a kofar ta shiga ta bud’e fridge duk abinda Ke ciki da d’an sanyin amman da zai sake d’aukar time zasu tashi aiki ire iren abincin data saba ci tana ajiyewa a firdge shi ta dauko tasa a microviw cikin mintunan da basu wuce uku ba yayi zafi jikinta har rawa yake wajen fito dashi .

a kitchen ta zauna taci nan da nan zufa ya rufe ta da kyar ta mike ta ajiye plet acikin zink ta sake bud’e frdge ta d’auki vatermilk ta kafa abakinta bata ajiye kwalbar ba sai data shanye tass sannna ta ciro apple da inibi ta daura akan plet ta yayyaka kanana ta dawo d’akinta koda ta shigo wayarta ta kunna kanta ta kulle dakinta ta zauan ta dauki wayarta ta hau what’s app tana duba sakwanin kawayenta suna ta tambayata “ ina ta shige kwana biyu wasu kuma suce wai dadin aure yasa yanzu ta rage hawa online ita dai dariya kawai take musu tana fad’a masu yadda tayi mugu kewarsu bayn ta gama dasu ta kira mahaifiyar ta sun jima suna waya inda take jaddada mata lallai taje airport gobe ta karbo sakonta tun washegarin ranar da sukai magana ta aiko .”

Washegar da ATA zai fita bai bada umarnin cire wutan gidan ba sai dai ya zare key kitchen ya wuce dashi koda ta sauko taga babu key ta fashe da dariya har da tafa hannu ta koma d’akinta ta d’auki waya ta turawa auta sako akan abinda yayanta yayi tana dariya nan take nana hauwa’u ta kira suna masa dariya maryam tace “ga keyn dana sace zanyi amfani dashi wallahi sister wannan yayan naki mugu a duniya babu kamarsa ,ki dai bi ahankali kar ya gane azabtar min dake kunnenta makale da waya ta sauko ta bud’e kitchen lafiyayyen breakfast tayi mai kyau tana ci suna waya da nana hauwa’u bayan gama ta sallami nana hauwa’u ta bar gidan batare da izinin ATA ba zuwa airport ta karbo sakonta a parlour’n gidan ta tsaya tana bud’e bakar jakar dake rike a hannunta wata yar qaramar tukunya ta gani ta sauke numfashi tare da maida tukun yar cikin jakar ta mike ta shige d’akinta tayi masa kyakkyawan ajiya acikin duro dinta har zata rufe durowar idanunta ya sauka akan littafin addu’oin da mami ta bata lokacin da zata tare ,ta dauka tana dubawa ko sau d’aya batayi tunanin ta duba tayi amfani da wasu abubuwa daga ciki ba ta zauna rike da littafin tana qoqarin dubawa wayarta ta fara ringing dan haka ta ajiye ta d’auki wayarta kiran mahaifiyarta ne .”

Har karfe goma shadaya na dare maryam na zaune tana jiran dawowar ATA sai dai shiru bai dawo gida ba, karfe shabiyu daidai ya shigo tana jin motsin shigowar motocinsa ta zabura ta mike tare da adduar neman saa jikin labulenta ta qarasa cikin sauri taga yana tafiya har sanda ya nufi kofar shigowa ta saki labalen tana cewa “ya Allah ka bani sa’a akan maganin nan bakin kofar d’akinta ta dawo ta labe tana kallonsa ya bud’e kofar dakinsa ya shiga batare daya zare key ba wanda ga dukkanin alamu ya manta ne sadaf sadaf ta bud’e kofar d’akinta ta fito ta tura kofar d’akinsa ta leka baya nan sai kayansa ta hango akan katifa alamun ya shiga wanka ta janyo kofar ta rufe ahankali sannan cike da tsoro ta cire key d’aya acikin key’n dakinsa tayi wuf ta fad’a d’akinta ta kulle tana dafe qirjinta da hannuwanta duka tare da furta.”

“allah na gode maka da kabani wannan saar gobe da safe yana fice wa daga gidan zan shiga nayi abinda zanyi “kai maryam mai yasa zaki dogara da irin wadan nan abubuwan wannan fa shirka ne qarara zaki aikata domin tukun yar tsaf ce ummah ta aiko miki dashi rayuwar nan fa babu tabbas babu yadda allah bazai yi ikonsa ba qaddara kuma tana fadawa bawa daidai yadda allah ya hukunto masa amman addua itace mafuta cikin ,rayuwar aurenki da Adam qaddara ce ki cigaba da hakuri zama dashi haka sarewa ta kalli mukulli hannunta kafin ahankali ta kira wayar mahaifiyarta ta koma can karshen dakin tana dauka “tace umma abin nan kuwa zan iya sakawa yaya Adam shi ? bana son abinda zanyi na cutar dashi ,sannnan hakan nan wannan aikin yake bani tsoro tun da kika fad’a min zai iya mance har mami tsoro ya shigeni ,rayuwar mami babu Adam akwai damuwa bugu da qari ta damqa min amanarsa idan na cutar mata dashi allah bazai barni ba “.
Chapter 49 · 0% Book details