← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 102

Sashe 13

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“A tunanina idan akayi aure shikenan kusancinka da miji kan sashi ya canza ashe ba haka ba, sai yanzu nake ganin gskyrki da kike kin auren yaya adam hakika shawo Kan yaya hisham ya gagareni bare ya adam” you're my life sister i love you so much duk duniya yanzu kece kawai wacce zan iya fad’awa damuwata ,ina shakar bakinciki a gidan yaya hisham most especially akan nuxla “ ni ban hanashi aurenta ba bare ma ban isa na hanashi ba, kawai ni abinda nafi buqata daga garesa ya kwantar min da hankalina shine kawai abinda nike so amman yaki kullum cikin d’aga min hankali yake ,ga yawon wayan da suke daita wani lokaci har asuba .”

“abinda ya bani mamaki daman nuzla tana son yaya hishsm ne? “ kamar tana son shi sister “idan tana son shi me yasa ta gudu ta barshi?"allah masani nima haka nagani abun nasu har da gayya amman ni na mika lamarina ga allah kullum shi nake roka ya zaba min abinda yafi zama alkhairi “ajiyar zuciya maryam ta sauke dan tuni farincikinta ya gushe ahankali kuma take jin wani irin tsanar nuzla na shigarta domin duk abinda zai damu sister ya dameta kuma zata iya yin komai akai "bari na fad'a miki irin abubuwan da nakewa yaya hisham da basu yi tasiri ajikinsa ba amman ki gwada yi wata kila yayi tasiri ajikin yaya adam "ki rufa min asiri sister kema kin kasa shawo Kan yaya hisham bare ni?
“ zaki iya nima da babu digon soyayyarsa nayi bare ke da na fahimci tsananin son da kikewa yaya."

“Kai sister !kai sister ko gsky "baki bazai iya misalta irin son da kike masa ba you just keep it in your mind naunayen ajiyar zuciya ta sake saukewa tace "haka ne sister ina tsananin son shi kuma bana jin zai daina wannan son har zuwa lokacin da numfashina zai bar jikina shine kad’ai muradin raina zan zauna dashi a kowani hali wannan alqawar ne “ shiru nana hauwa'u tayi  tana sauraron  bayaninta “uhmm ai nasani gbdy yayana ya tafi da komai naki ya bar min saura ."harara maryam ta sakar mata kamar tana gabanta stil fuskarta dauke da murmushi ta cigaba da magana "sister ko bai sona na kasance dashi hakan zai dangwamar dani cikin farinciki ko bazai soni ba zan rayu dashi ."

“Ina rokon allah idan har dole dayanmu ne zai samu farinciki samun soyayyar gidan aure to ya zamanto kece zanji dadi zanyi farinciki domin kece kike tare da abinda kike so ni kuma daman banyi aure dan soyayya ba ,”ni kuma ina rokon allah dukkaninmu mu dace mu samu soyayyar mazajenmu so na har abada “mrym ta qarasa mgnr tana hawaye yayinda itama nana hauwa'u hawaye take zuciyar kowacce na cike da tunani .”maryam na tunanin halin da zata shiga a gidan aurenta yayinda nana hauwa’u ke tunanin halin da take ciki a gidanta sun jima suna waya nana hauwa'u na fad'a mata abubuwan da zatayi domin janyo hankalin yayanta sannan sukai sallama.”

Maryam ta zauna shiru tana mamakin hakurin nana hauwa’u zata iya hakuri akan komai na gidan miji amman banda hakuri akan wata ko bata dauki mataki akan miji ba lallai zata dauka akan duk wacce zata ra’bi mijinta ,mijinta nata né ita kad’ai dan haka babu wacce zata daukarwa rainin” ta dade zaune tana saka da warwara kafin daga bisani ta mike ta nufi d’akin mami inda su aunty shahida suke,jiki a sanyaye ta tura kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama gbdynsu suka maida hankalinsu gareta cike da girmamawa tace “aunty shahida me zaa daura maku ?.”

Aunty shahida tayi murmushi kana ta dubi sauran yan’uwanta tace “ me zaku ci ? duk abinda zaki ci shi zamu ci “okay mrym kin iya fankaso?mrym tayi shiru na second biyu sannan ta gyada mata kai alamun” eh! “tô kiyi mana fankaso na kwana biyu ban ci ba ,suma kuma nasan zasu ji dadi ahankali tace “tô !ta juya ta bar d’akin zuwa kitchen tana kiran masu aikin gidan cikin kankanin lokaci suka bayyana agabanta nan ta fad’a masu abinda take son su tayata ita kuma ta soma qoqarin kwa’ba fulawa duk abinda mrym tayi ranar cikin sanyin jiki tayisa tare da tunanin halin da nana hauwa’u take ciki .”

Washegari  da misalin karfe shida na yamma ATA ya tashi daga bacci wanda ya soma tun karfe biyu dan baccin ne ma ya dawo dashi gida, mika yayi tare da salati sannna ya sauko daga shi sai boxer ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya fito kugunsa d’aure da towel yayinda hannunsa ke rike da wani qaramin towel yana goge sansar jikinsa bayan ya gama ya feshe ilahirin jikinsa da body spray sannan ya qarasa inda kayansa yake ya dauko   blak and whit rigar mai hade da wula ya saka yayi kyau sosai tamkr wani matashi d’an shekara talatin a duniya ya gabatar da sallah la’asar ya fito parlour ’nsa ya bud’e fridge ya dauki holladia milk mai sanyi ya sha sannan ya sauko daga samansa ya nufi gurin mami yana qarasowa ta ajiye jaridar hannunta tare da mika masa hannu.”

ya qaraso ya zauna kusa daita kallonsa tayi cike da kulawa "shigowata uku  ina duba ka baka tashi ba daman tun da naga  irin kwanciyar da kayi nasan ka gaji domin bacci kake  mai tattare da stress ."
numfashi kawai ya sauke batare da yace komai ba "muje kaci abinci kallonta yayi cike da qauna aransa ,yace "sweetheart na sha hollondia milk bana jin yunwa yanzu may be kafin na kwanta yayi mgnr yana zuba mata kwayar idanunshi ."adamcy nah !
ta kira sunansa yaji wani faduwar gaba dan duk sanda ta kirasa haka yasan akwai damuwa.”

"dan allah mar.."no sweetheart karki ce wani abu yanzu we 'll talk later amman right now karki ce min komai akanta dan allah ki barni na huta da mgnrta haka ,kullum magana daya kmr wata zinariya "yayi mgnr cikin fushi murmushi tayi tana dungure masa kai "bazaka bari nayi maka nasiha ba "wani nasiha kuma sweetheart ?nasihar da acikinta muka tashi idan ma nasihar ce ita ya kamata kiyiwa nasiha dan ni dai kinsan bana son qazanta a gidana , ina buqatar kamshi akoina na shiga  bana son shirme da hauka agidana “ya qarasa mgnr tare da yi  shiru "sai me kuma ?thats all I need bayan wadan nan bana buqatar komai ."

"shi gyara shim....fi...da.." rawar da muryarta ta fara da in ina saboda kallon daya tsareta dashi  yasa da kyar ta samu zancen ya kai qarshe tace “me yasa kake kallona haka kmar zaka cinyeni ?”allah adamcy zaka iya kashe mutun da kallon nan naka ,mutun sai mugun kallo “lumshe tsumammun idanunshi yayi tare da riko hannunta daya cikin nashi yace "sorry sweetheart ban fahimci abinda kike nufi bane shi yasa kika ga ina miki kallo haka "ajiyar zuciya ta sauke tace " ina son jikoki daga wajenka shine maaanar gyara shimfida dan karka ce zaka ki hada shimfida daita ".ta qarasa mgnr tana dubansa .”

"Sweetheart iya jikokin da kike dasu sun isheki haka ba sai kin samu qari daga gareni ba” ya fad'a yana zare hannunsa daga cikin nata yana sake kallon fuskarta ganin yana qoqarin mikewa tayi saurin rikosa za tayi magana ya katseta da cewa "ina son haihuwa amman bana bukatar haihuwa daga gareta d'an haka tun wuri sweetheart ki daina tunanin zaki samu jikoki daga gareta dan bazaki samu ba ."
murmushin karfin hali mami tayi cikin tsigar rarrashi tace "ka dai bi ahankali karka zo kana rage wa diyata murya fa ."na gwamaci mutuwa  akan nayi haka "come on adamcy nah ka daina cika baki karka zo kana min kuka kana sonta fa ."

zare hannunsa yayi tare da barin gurin ya nufi hanyar fita yana cawa “sai na dawo!   bayansa tabi da kallo tana jin wani irin zafi na taso mata duk da ac dake aiki a parlour'n komawa tayi ta jingina jikinta zuciyarta na tsalle saboda sarai tunda ya nuna baya só baya só né kuma zai yi wuya ya só ko yayi wani abu da mrym amman tunda akayi wannan auren babu mai kashesa sai allah, duk yadda zatayi sai tayi ya só mrym ,shiru tayi tana tunanin dan bata son takura wa d’anta har karfe goma bai shigo gidan ba mami ta kasa shiga ta kwanta duk ta kasa sukuni saboda bata son yana dadewa awaje  haka ma maryam yadda mami bata runtsa ba itama bata kwanta ba tana kusa daita "

Suna  zaune suna duba agaogo ya shigo tamkar wani zaki ganinta cikin wani yanayi yasa ya qaraso ya zauna kusa daita kallonsa tayi tana sauke ajiyar zuwa ganin babu wani sauyi atare dashi "sannu da zuwa yaya "mrym ta fada. yayi mata banza tmkr bai ji ba yana cewa "sweetheart ba kiyi bacci ba ?cike da kulawa tace “taya zan iya bacci byn adamcy
nah bai shigo ba “ina kaje.?" naje waya unguwa né amman na dawo since muna tare da mb né “ baka ci komai ba har yanzu”? numfashi ya sauke daman yasan sai ta tambayesa "bana jin cin komai sai da safe naci "kana son barin kanka da yunwa mrym maza tashi zubo masa abinci kafin mrym ta mike ya mike ya nufi samansa ."

Mrym tayi dining ta zubo masa abinci ta dawo mami gashi” yi hakuri mrym ki bar abincin nan bari na hada masa coffee nasan zai sha tunani tayi tasan halinsa tunda yace baya ci bazai ci ba  zagayeta tayi ta hada masa  coffe tayi samansa tana shiga parlour'n ta taraar dashi zaune idanushi a lumshe "adamcy nah "ta kirasa ahankali tare d zama kusa dashi gyara zamansa yayi ya zuba mata ido bai ce komai ba "ga coffe ka sha babu musu ya karba ya soma sha ahankali tana tare dashi har sai daya shiga wanka sannan ta sauko ta shige dakinta tayi alwala tazo tayi shafai da wutiri ta kwanta ."
Chapter 13 · 0% Book details