← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 102

Sashe 80

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tsaye yaya sadam yake a d’akinsa muryarsa can qasa qasa yana waya da nadiya “haba nadiya nasani nasan ban miki adalci ba amman kema Kinsan yadda nake mutuwar sonki ,soyayyar shekaru biyar fa ni kad’ai nasan me nake ji ajikina tabbas nasan laifina ne da ban shigo da maganarki da wuri ba har aka zartar da wannan hukunci ,No bazan iya cewa mahaifiyata haka ba . zan dai san abun yi ki kwantar min da hankalinki ki saurareni at anytime .a natse ya fito cikin jallabiya ruwan qasa kawai yaga maryama zaune ita kad’ai a falon .”sai daya zauna sannan suka kalli juna shi da maryam gano yanayin maryama kamar tana cikin damuwa ya matsota sosai har suna iya shakar numfashi juna dan a tunaninsa ko taji wayarsa ne ahankali ya kamo yatsun hannunta wanda yasa taji wani irin zirrr a sansar jikinta nan da nan tayi qoqarin zare hannunta bai damu ba yace “lafiya na ganki haka ?daman magana nake son muyi “ina jikin me zaki fad’a min ?”amm amm daman akan wani aiki ne daaka kirani nace na fad’a maka nan dai tayi masa bayanin komai ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta “kinji abinda naji kuwa ?wani irin aiki ne har ogun state kuma a ranar daurin aurenmu ?nan da nan jikin maryama ya kama rawa “kayi hakuri bansan mgr zata bata maka rai ba na hakura ba sai naje ba na cigaba da aikina anan daman ba wai zasu d’auke bane aiki ne na lokaci zuwa lokaci kuma ba aikin kwana bane amman kayi hakuri karkayi fushi dani ta qarasa mgnr muryarta cike da rauni .”

ya kalleta cike da tausayinta sakamakon yadda take magana cikin sanyin murya da tsoro ,ita kanta a yadda take maganar tana jin babu dadi har cikin ranta “shikenan ki kwantar da hankalinki yanzu me kike ganin zamuyi ?”ya tambayeta cikin sanyin rai “tô wai idan ka amince sai muje tare da kai ,idan kuma baka amince ba wallahi babu komai na hakura allah ya zaba min abinda yafi zama alkhairi murmushi ya sakar mata yace “shikenan karki damu amaryata zamuje tare ai ni yanzu duk abinda kike so ina so ko bangon duniya kika ce zamuje tare allah ya nuna mana ranar nan da nan murmushi ya bayyana a fuskarta “amman naji dadin amincewarka wallahi baka ta’ba sakani farinciki irin na yau ba na gode sosai allah ya jikan iyayenmu Allah yasa suna aljanna Allah ya saka maka da alkhairi Allah yaja da kwanan ummah ,Allah ya bamu zaman lafiya a arayuwar aurenmu “Ameen Ameen ya Allah Allah ya nuna min kin haifa min yara masu yawa tasa hannu tana rufe fuskarta nan suka cigaba hirarsu.”

Ranar lahadi 14 ga watan October shekara ta dubu biyu da bakwai aka daura auren maryama da yayanta sadam .ana gama daurin aure suka fara shirin tafiya ogun state wanda kusan yaya sadam ne yayita matsa mata ta d’auko kayan aikinta tare suka shiga wajen ummah lokacin tana tare da yan’uwanta dana mijinta tayi masu fatan alkhairi fuskarta dauke da farinciki maryama ta zama mallakinta gabdaya lokacin da zasu wuce aunty hassna tace “yanzu dan lalacewa aunty har da murna kike tun baaje koina ba an mallake miki d’a “cak maryama ta tsaya cike da sanyin jiki “me zanyi hassana matarsa ce kuma ya amince tunda ya amince meye nawa aciki ?kunga kuyi maza ku kama hanya Allah ya tsare min ku suka sa kai zasu fice har sun kai bakin kofa umma tace “sadam ya juyo daga inda yake “ka kular min da maryama da kyau ,Allah ya tsare hanya “to ni ummah bazakice ta kular miki dani ba ?tayi murmushi shikenan “maryama ki kular min dashi Allah yayi maku albarka suka ce “ameen suka fito suka shiga mota suka d’auki hanyar ogun .”

Cikin sauri sauri ATA ya fito daga dayan bedroom dinsa cikin wasu had’ad’den kanana kaya bakake ajikinsa ,ya  shiga dayan dakinsa wanda kusan abubuwansa masu mahimanci anan suke, yadda jikinsa ke fitar da kashin turarensa reed akoda yaushe haka dakin Ke dauke da kamshin turensa, cikin sauri ya dauki farin glass dinsa   ya manna a kwayar idanunshi sannan ya qaraso ya dauki agogo baki ya daura a tsintsiyar hannunsa ya bude bedside  ya dauki  wallet dinsa ya tura cikin ajihunsa ya daura facing cup yayi mugun kyua ya fito sanyayyen kamshin turarensa na binsa cikin sauri yake taka step cikin . a zaune ya iske mami tana waya ya d’an tsaya yana kallonta dan ga dukkanin alamun da wannan yarinyar take waya gyaran murya yayi yana sham kamshi ta waigo tana dubansa “ina zuwa kuma ? wani aiki !ya bata amsa atakaice yana had’e gira sama data kasa dan kar ma tayi masa mgnr mrym “naga yau weekend ce ?eh ogun state zani zan iya dawowa a yau watakilla kuma sai gobe dan aikin nada matukar mahimanci .”yana gama fad’ar haka ya nufi kofar fita .”

To adamcy mami fatan nasara

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 25

         Tafiyar awanni hud'u ta kawosu maryama ma'aikatan ATA dake jahar ogun state yaya sadam yayi  parking din motarsa acikin haraban ma'aikatan sannan suka fito atare yana gyara zaman farar shaddar jikinsa yayinda maryama ke qoqarin neman layin mr  segun kira d'aya mr segun ya d'aga sukai magana na second biyu sannan ta fuskanci yaya sadam fuskarta kwance da annurin  farinciki mara iyaka tace "kad'an yi hakuri yanzu za'a yi mana iso zuwa ciki " yaya sadam ya gyad'a mata kai kawai alamun babu komai yana sakar mata tsadaddaden  murmushinsa ,suka  tsaya suna magana kasa kasa kafin ayi masu iso .wani matashin saurayi ne ya sauko  sanye da bakaken kaya ya shigar dasu ciki .
a wani dogo office aka shigar dasu wanda gabad'aya nsa glass ne dan ana iya hango duk wanda yake ciki ,basu d'auki cikakken mintuna goma ba mr segun ya shigo yana tmbyr saurayin daya shigo da
su maryama "niyi ina bakuwar  daka shigo daita ?
"sir itace  a gabanka zaune”  mr segun ya d'an ware idanunshi akan maryama dake zaune yana mata barka da zuwa yana mai sake  masu iso  zuwa wani office din dabam wanda daga shi sai wanda ATA yake cikin zaune zaman jiran qarasowarta  .

     "kusa da maryama yaya sadam ya samu waje ya zauna kamar zai mata numfashi "madam ya hanya ?"
mr segun ya tambayeta cike da kulawa yana kallonta "alhamd sir tunda gamu mun samu mun qaraso lfy amman fa  da kyar dan hanyar nan taku bata da kyau tafiyar da ya kamata ace one to two hour's ne ya kawomu shine ya d'aukemu har four hours amman alhamdulillah "wannan gsky ne mutane na yawon complain akan hanyar nan tamu amman dai  alhamd tunda kun qaraso lafiya tun  mai gida bai gaji da zaman  jiranki  ba dan awaninsa biyu da qarasowa bari nasa akawo maku abun sha, idan kin gama wancan office din dake kallonki zaki shiga kafin nan ma zaki same aciki "yana gama fad'ar haka ya fita da d'an sauri ya barsu zaune maryama ta zuba ma yaya sadam ido har sanda aka kawo masu abun sha ta d'auka ta tsiyaya masa a glass cup ta mika masa ."
ahankali yasa hannu ya amsa cup din hannunta ya kur'bi kad'an yana mai lumshe idanunshi sannan ya ajiye cup din hannunsa yana dubanta a tsanake "ya naga duk kinyi wani iri ?"naji yace idan na gama na shiga  ni kuma nafi son mu shiga tare da kai banason na barka kai kad'ai zaman jirana "
Chapter 80 · 0% Book details