← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 102

Sashe 86

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryama kam cikin wani jahili gida su jojo suka nufa daita a sume can wajen gari a tsakanin lagos to ile ife , gida ne na sirri wanda ba kowa yasan dashi ba gida ne da mai gidan ya gidana domin taronsa na sirri ko kuma duk sanda zai holewarsa ko kuma wani meeting sannan yana ajiye mahimman abubuwansa agidan ,gida ne mai hawa  daya  kuma   agyare  yake babu abinda babu acikinsa najin dadin rayuwa gida ne wanda babu wanda zai san an shigar da mutun sai su da kansu idan sunyi raayin asani ." a babban parlour'n sukai masauki tare da wanda ya basu aiki shima kuma ba gidansa bane gidan abokinsa ne ya amshi key a hannunsa  kai tsaye ya nufi bedroom suka biyosa da maryama kan  wani makeken bed din dake dakin ya nuna masu suka shimfideta "aikin
ku yayi kyau sosai fa .gabad'aya suka kwashe da dariya shikenan an kashe boss kowa ya huta sosai kuwa suka amsa masa atare tsaye yayi yana kallonta yana sauke numfashi yana lashe lip's dinsa "kusan wani abu ?gabadaya suka girgiza masa kai "da alamun yarinyar nan ta shiga comer?nima abinda na fahimta kenan "idan dare yayi ku dawo ku dauketa ku bar nan daita domin bata da wani sauran amfani agareni , ku dauketa ku kaita duk hospital din da kuka ci karo dashi amatsayinku na sojoji bazaayi wani bincike akanku ba, kuce kun tsinceta ne a hanya cikin wannan yanayin ."an gama!" zuwa gobe zakuji alert dina "okay babu matsala ."

Da misalin karfe goma ba daren ranar mutun biyu acikinsu  suka fitar da maryama wacce bata san halin da'ake ciki ba suka nufi wani hospital daita yadda akace suyi haka sukai suka ajiyeta da wayarta da jakarta suka qara haba taimakon gaugauwa aka fara bata sai dai har zuwa washegari bata farfado ba har sanda aka kira number number wayarta suka dauka tare da sheidawa wanda ya kira halin da'ake ciki ."
Kallo daya zaka yiwa su ummah ka tabbatar da cewa baa cikin nutsuwa walwala da kwanciyar hankali suke ba, tunda suka duro  hospital bayan wayar  da  sukai da  ma'aikatan hospital din ,daman kuma tun ranar farko da tafiyarsu sadam  din basu sake samun isashen bacci da  nutsuwa ba har sai da suka daura kwayar idanunsu akan maryama "me ya sameta haka da har ta fice hayyacinta bata gane kowa?,me ya kawota asibiti "ina sadam da suka ganta ita kadai kwance rai hannun allah? kamar kar su zo ta fara  sambatu tana kuka tana kiran sunan yaya sadam tana fad'ar irin abinda akayi masa aunty   Kuka ta fashe dashi cikin tsananin tashin hankali tana bubbu qasa tana fad'in "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "dan  allah karku kashesa   dan Allah ku fito min dashi daga cikin rami  ,su waye suka sakaku wannan aikin ku fad'amin  wanda ya sakaku zan mika masu  rayuwata dan bana son na rasa yaya sadam .wannan mummunar kissar dani yafi dacewa  bada bawan Allah kamar shi ba dan Allah ku fito min dashi "tana ihun  fad'ar haka sai taji anfasa wani razanannen kuka akanta  mai kukan tana fad'ar "lahaula wala kuwwata " me ya samu sadam shikenan kin kaishi an kashe mana shi"inji cewar aunty hassana ummah kam kalmar  innalillahi wanna ilaihi raji'un  kawai take furtawa "wannan yarinya me yayi miki da zaki sakamasa da wanna muguwar sakayya."?

farkawa maryama tayi ta ganta akan gadon hospital cikin yan'uwanta dana  ummah ,ummah  ta riko hannunta cikin nata tana mata sannu aunty kam kuka kawai take tana furta adduaoi, cikin haka  doctor ya shigo ya sallamesu gabdaya domin  duba jikin maryama sai bayan daya fita suka dawo dakin suka cigaba da zage zage har sai da ummah ta dinga taka masu burki , duk wanda zai yi magana sai ummah ta hana tare da cewa  yaje waje maryama na bukatar hutu a qarshe dai daya bayan daya suka fice sai daga baya suka dawo har dare babu wanda ya sake cewa komai  sai da irin kallon da suke binta dashi babu sausauci ."maryama  dake kwance cikin tsananin tashin hankali ta zuba ma ummah dake  zaune a gefenta ido tana dubanta ,itama umma ita din take kallo duk ta fita haiyacinta yadda idanunta suka kunbura sukai wani irin girma sun bata tsoro matuka  yayinda gabad'aya fuskarta tayi jajur saboda kuka ahankali ummah ke mata nasiha tana tofa mata addua wani irin yanayi maryama ta shiga alokacin da idanunta da kwakwaluwarta suke sake hasko mata komai daya faru ."

a natse ta dinga bin kowa dake gurin da ido sai dai taga wani irin mugun kallo suke mata zuwa can taji aunty hasana na cewa "ji yadda take bin mutane da kallo wannan yarinyar fa muguwar munafuka ce dan allah tashi ki fad'awa mutane inda kika kai mana d'anmu daga rakiya ai wallahi baki isa ba sai kin fito mana dashi dan shi kadai muke kallo a matsayin mahaifinsa ."mikewa maryama tayi jikinta a sanyaye har ga allah tafisu bukatar yaya sadam arayuwarta sannan yadda suke nuna mata baya mata dadi  duk da tasan basa qaunarta amman batayi tunanin zasu zargeta ba kanta ta daura akan cinyar  ummah tasa kuka tare da jin wani kullin  abu ya tsaya mata yaki gaba yaki baya "ummah ce ta dinga rarrashinta tana yiwa aunty Hasana fad'a "wallahi ummah bansan mutane nan ba bazan iya cutar da mijina  kuma danuwana ba wallahi ina son yaya sadam ."
"nasani maryama bazaki ta'ba iya aikata hk ba cikin jin dadin kalaman ummah  maryama tasa kuka tana cewa "ku taimakeni ku nemo min yaya sadam domin ban san inda zan saka rayuwata ba tana kuka ummah na share mata hawaye duk da itama hawayen take sosai hankalin mutane ya tashi kowa kuka yake a wajen ".

"ummah Kiyi hakuri ki yafe min nayi nadamar fita wannan aiki ban san me ya jani na aikata haka ba kuma wallahi na daina  farinciki da iya wannan aiki da nayi arayuwata ummah kuzo muje inda aka binne yaya sadam da ransa zaa iya samunsa a raye ina ji ajikina bai mutu ba hawaye umma ta share amman maryama kwanaki biyar kenan da faruwar wannan alamarin kina ganin zai rayu "?numfashi ta furza mai zafi "ummah !"sai kuma tayi shiru tana wani irin kuka tana tuna kalamansa na qarshe gareta "abinda nake so dake maryama  ki natsu sosai kiyi abinda ya kawoki ina sonki ina kuma alfahari dake na kuma yarda dake a duk inda zaki kasance nasan zaki kame min kanki da kuma mutuncina wani sabon kuka ta fashe dashi  "ummah ta riko hannunta gam cikin nata itama kuka ta fashe mata dashi sosai cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunan allah tana cewa "laifin me d'ana  yayi masu wannan hukuncin yayi tsauri  ga rayuwar sadam babu wanda zuciyarsa batai rauni ba aunty da wasu daga cikin yanuwa hawaye suke dan tausayawa ga umma d'aya bayan suka dinga barin dakin inda dakin ya saura daga aunty sai ummah da maryama "umma muje inda aka binne yaya sadam  a fito dashi jikina na bani yana nan a raye ummah ki tausaya min wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba "ki samu natsuwa maryama in sha allahu zamu je gobe"iya abinda ummah ta iya fad'a kenan bata sake cewa komai ba dan bazata iya magana mai tsawo ba ."

washegari aka kai maganar gurin hukuma aka shigar da qara tare da nuna hoton yaya sadam daga nan aka yiwa maryama tambayoyin daya dace sannan aka saka maryama gaba sai hanyar ogun state tafiya suke tana share hawaye tana addua duk kwanar data gani sai ta rikice tace nan ne . sai an tsaya tace a’a ba nan bane ahaka suka kusan kaiwa cikin ogun state dan daga inda suke suna iya hango sambaod din wel come to ogun state tayi sauri tace “ kamar kafin mu kawo wannna sambaod din ne .”cak direba dake tukasu ya tsaya tare da juya Kan motar suka koma dayan hannun sun sha wahala sosai a qarshe dai ta gane daidai inda sojojin suka sha gabansu saka makon warin takalminta data gani yashe a gefen titi .” jikinta na rawa ta soma kuka tana cewa "ku tsaya nan ne !"batare da bata lokaci ba suka firfito “tabbas anan ne suka sha gabanku “ta fad’a tana kuka .daya daga cikin jami’in tsoro yace a ina aka binnesa nan maryama ta hau zazzare ido “tabbas daga nan suka rufe mana ido amman duk da haka jikina na bani wannan kwayar suka shiga damu basu mutsa mata ba suka shiga mota suka bi hanyar tafiya suke amman jikin maryama rawa yake dan bata son tayi kuskure wajen gano wajen .”

gabad’aya babu inda baa duba ba ko zaa ga alamar tudun kasa amman babu ,jami'an tsoro suka tsaya suna kallonta "kin tabbatar nan ne?tayi shiru tana share hawaye dan gbdy ta rikice ummah Ummah duk ta rude sai zufa take fitarwa ta matso kusa daita tace “maryama ki natsu da kyau a samu a gano inda suka binnesa” tayi mgnr cikin rawar murya maryama ta fashe da kuka tare da zubewa kasa sakamakon ta rasa mafuta.”dan kwakwaluwarta ta cunkushe waje d’aya yadda maryama take kuka haka umma take kuka tana janyota jikinta gabdaya jikknta ya d’auki zafi kamar garwashin wuta yayind jami’an tsaro suka cigaba da dudduba wajen ko zasu ci karo da tudun kasa amman still dai babu wata alama inda aka binnesa ganin suna bata alokacin su ne yasa suka ce su wuce zaa zaa sanar a gidan radio da tv maryama kam duk ta gama rikice masu sai sunan yaya sadam dina kawai take kira “ku nemo min shi dan Allah karku barni haka da kyar aka samu aka saka acikin mota suka kama hanyar gida .”

******
Chapter 86 · 0% Book details