← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 102

Sashe 39

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan shine dalilin da yasa bana son shi yanzu bai son jinina me zanyi dashi "tô ai shi só halitta ne umma amman ina sa rai wata rana zai duba lamarina da izinin allah ki tayani da addua,addua kam muna yi dan tun daakayi auren naku ban zauna ba wajen neman miki taimakon samun 'yanci a gidan miji ,yanzu haka ma ga wani taimakon nasa an amso miki daga zuru zan turo miki ta jirgi kije ki karbo da kanki acikin abinsa zaki zuba masa idan allah ya taimaka yaci wallahi sai dai wani ba wannan adamun ba sai yadda kikayi dashi maryam tayi sauri ta cire wayar a speaker tana waiga bayanta dan datasan mgnr da zai cigaba da fitowa bakin mahaifiyarta kenan bazata saka wayar a speaker ba."

Ta sauke numfashi sannan ta maida wayar kunnenta ta rage murya sosai ta cigaba da magana "gsky ummah bana son nayiwa yaya adam wani abu tukun ya soni nafi son ya soni dan kanshi "tô shikenan zanyi amfani dashi tayi discounting kira tare da soke wayar acikinta ta kawo karshen maganar né da fad'ar haka dan ita bazatayi masa amfani da komai ba , taji ma da tarin zunubin dake kanta ta hada masa abinci akan qarami tray ta fito ta nufi hanyar d'akinsa bynta suka sake bi da kallo cike da tausayawa a hankali ta tura kofar d'akin ta shiga yana zaune a kasan d'akin ya tokare hannunsa yana kallon sama . yana jin motsin shigowa d'akin ya kalli kofar  ganinta yasashi jan tsaki yana kwar da idanunshi gefe ta karaso ta tsugunna kusa dashi jikinta da murya na rawa ta d'an saci kallon hannunsa mai ciwo sannan tace "ga ...ga abinci!

" bai ce komai ba ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa da karfi "kayi hakuri da abinda ya faru wallahi bani da masaniyar faruwar komai da kuma nasan hkn zata faru wallahi bazan bari ba bazan ma sa bakina ba daman nayi haka né dan "ya waigo a fusace ya kalleta a kaskance hakan yasa ta kasa cigaba da magana zuciyarta na bugawa ganin bai yi magana ba yasa ta sake bude baki zatai mgn ya d'aga mata hannun tare da tsareta da idanunshi wanda hkn ya haddasawa zuciyarta shiga rudani da bugawa da sauri "kin kamu da sona ko ?tai shiru tana duban cikin kwayar idanunshi karo na biyu kenan daya furta mata haka sai dai ta kasa bashi amsa tmbyrsa ."

"kina sona kuma shine dalilin da yasa kika dawo abar tausayi haka ba ? nan ma shiru tai masa dan batasan me zata fad'a masa ba "nonsense girl kawai wallahi kin cuci zuciyarki ke yanzu kinga dacewar mu da zaki kamu da sona ?tai saurin girgiza masa kai "ba.." bana só.."you are very stupid shut up iam talking you talking sai na kasheki da mugun duka taja bakinta tayi shiru tana sauke numfashi."
Ya mike tsaye yana dubanta kamar zai had'eyeta da idanunshi "itama da sauri ta mike jikinta na kyar "ni zaki kalla kice baki so ?ta sake girgiza masa kai ."
"better kin taimaki kanki da kanki ,kingan ni nan har abada bazan ta'ba ganganci barin ki zauna acikin nan ba "ya nuna daidai saitin zuciyarsa da d'an yatsansa ."

" zan baki shawara kiyi gaugauwan cire sona aranki kamar yadda na ta'ba fad'a miki adam mallakin mafarkinsa ne idan ban sameta ba mallakin wata ce dabam amman bake ba "tunda ya soma magana tske jin tashin hankali mara misaltuwa" me yasa zakace haka yaya adam? daga ranar da ka zama miji agareni daga ranar na sanyaka acikin abinda yafi zuciyata da gangar jikina ,zuciyata ta haukace akan sonka ina jin ciwon kiyayyar ka gareni amman na kan kawar dashi domin na samu damar dasa soyayyata acikin zuciyarka ta hanyar maka biyayya "enough...! bana son jin maganar soyayya daga bakinki ai tunda kina iya shiga tsakanina da mahaifiyata kin kad'e a wajena domin wannan son wa ni kadai ya dace ban dake amman gashi an kasashi gida biyu "ya fad'a ya fusace ."

"ban kwace maka soyayyarka ba mami tana sonka fiyye da komai kuma matsayinka na nan acikin zuciyarta ,bazata ta'ba canzaka da wata ba, watan ma ni ai ban isa na taka matsayinka a zuciyarta ba kuma duk wannan kulawar da kake ganin tayi karfi yanzu saboda kai ne saboda ..."please let me be alone ya fad'a yana juya mata baya cike da jarumta ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa "out of this room now ya nuna mata hanyar fita ."shiru tai ta kasa motsa jikinta ."ganin hk yayi tunanin bar mata d'akin ya nufi hanyar fita ta biyosa da sauri tana cewa "d'an allah kayi hakuri kaci wani abu sai daya bari ta fita daga d'akin gbdy ya dawo da baya ya rufe kofar.

cike da muryar kuka tace" ka yafe min banyi maka laifin komai ba wallahi ban had'aka da mahaifiyarka ba ni kaina bansan hakan zata faru ba wallahi dana san wanda zai fad'a mata alokacin dana hana bai ce uhmm ba bare uhmm ya bar jikin kofar yana jan tsaki tare da furta "nonsense!wani sabon kuka ta rushe dashi"maza masu sanyin halima baka barinsu haka ,bare miji irin naki dole sai kin tashi tsaye wajen mallakesa sannan zaki samu 'yanci agidan aurenki "maganar mahaifiyarta na karshe kenan a wayar da sukai yi d'azu  nan take taji ta yarda kuma zuciyarta ta amince zatayi amfani da maganin da mahaifiyarta zata aiko mata domin samarwa kanta kwanciyar hankali a gidan mijinta "ahankali taji an dafata ta waigo idanunta cike da ruwan hawaye "Mami ce !

"Mami dan allah ki fad'a masa cewar bani na hadashi dake ba, dan allah mami ki bari ya fahimce hakan " naunayen ajiyar zuciya ta sauke " na rasa me yasa adamcy yake son caza miki kwakwaluwa mami ta fada hk a fili "ita kuwa mrym kuka kawai take tana rokon mami ta fahimtar dashi "kukan ya isa haka zan fahimtar dashi duk da ba rarrashi ya kawo wajensa ba amman zan kwantar da kai saboda ke "yauwa mami na gode sosai dan allah ki lalla'bashi kar kiyi masa fad'a ta fad'a tare da share hawayenta "mrym ki daina yawon kuka ki dinga dauriya mijinki ba mutun bane mai damuwa da kukan mutun ko sanin mahamancin hk, jajurcewarki ita zatasa kiyi nasara akansa  ta runtse idanunta wasu hawaye masu zafi zuka zubo mata ".

"nace kukan ya isa haka "tô mami kice ya bude kofar yaci abincin nasan tunda ya bar gidan bai ci komai ba amman sam sam yaki saurarata"kije for now nasan halin d'ana kema kuma idan da sabo ya kamata ace kin saba da halinsa bazai ce miki komai ba sannan bazai ci komai ba, ki bari zan fada masa komai zan fahimtar dashi baki da laifi kuma zan lalla'ba miki bazan masa fad'a ba ki kwantar da hankalinki naunayen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara janjikinta ta bar wurin mami tai knocking tana kiran sunansa da kyar ya bud'e mata kofa.
Ahankali ta tura kofar ta shiga ta tsaya abayansa bai juyo ba tasan yayi haka saboda fushin da yake daita ."

Numfashi ta sauke tare da d'aura hannunta ta dafa kafad'ansa tana kiran sunansa "adamcy nah !kmr jira yake ya juyo ya zuba mata tsumammun idanunshi yanayinsa kmr zai yi kuka itama mami ganinsa haka ya karyar da zuciyarta domin ya zube ya fita haiyacinsa acikin kwanki hud'u kawai idanunshi duk sun rikid'e sun canza kala alamun shan sigari hannunsa mai ciwo ta kamo tana kallo nan take yanayinta ya sauya idanunta suka fara kawo ruwa .ganin haka ya rungumeta ajikinsa qirjinsa na bugawa da wani irin karfi sai da mami taji tsoron yanayin bugun zuciyarsa . ta zaresa ajikinta tana kallonsa hawaye ta gani a fuskarsa hankalin mami ya qara tashi wannan shine karo na biyu da taga d'anta na kuka a tun tasowarsa lallai adamcy baya son mrym ".

"kiyi hakuri sweetheart ina 'bata miki rai hakika ban rike amanar da dad ya bani ba ki yafe min zuciyata ta kasa son mrym ki bani damar na auro wata please." nasani nasan baka sonta amman ina sa rai zaka sota wata rana ,ni ban hanaka qara aure ba ko kawo zabinka ba amman sai naga irin adalcinka ina son kasan mutunci maryam kasan daraja maryam ka bata kimarta da darajarta ta matarka ,ka bata matsayin mata acikin zuciyarka, ka yarda daita wannan shine burina kafin ka shigo da wata matar gidanka."adamcy maryam na da kirki tana da biyayya da hakuri ban maka zaben tumun dare ba na zaba maka abinda zaka yi alfahari ne ko bayan raina zaka yi alfahari daita fatana ka rike matarka amana na yafe maka na yafe maka na kuma janye fushina akanka allah yayi maka albarka allah ya azurtaku da samu zuria masu albarka ".

Shiru yayi yaki amsawa da ameen "ina son maryam sosai Adamcy kai ma kuma ina son ka koyi sonta .."ya qara tsura mata idanunsa da sukai jazur "zaka min wannan alfarmar?zaka koyi sonta ?shiru yayi ya kasa furta komai "kayi shiru Adamcy ya kamata kace min wani abu ko zuciyata zata samu salama ta fad'a tana d'aura hannunta akan sumar kanshi yayinda hawaye ya cika idanunta ta rasa wani irin baqar zuciya garesa tun yana yaro take fama dashi idan ya tsani abu ya tsana kenan idan yace yana son abu shima haka ne, tasan da wahala ya so maryam kamar yadda take bukata. ta cire hannunta dake Kan sumar kansa ta tsurawa yatsun hannunsa ido hawayenta ne suka dinga diga akan nashi tafin hannun da sauri ya dago kansa ya sanya kwayar idanunshi cikin nata yana furta "why sweetheart me yasa zaki min haka ."?
Chapter 39 · 0% Book details