← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 102

Sashe 66

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

firgigib ta bud'e idanunta ta mike zaune tana shafa idanunta bai tsaya wata wata ba yaja hannunta hanyar waje yayi daita ,maryam wanda keta rokonsa ya barta a kusa da mami amman bai kulata ba yana kaiwa waje yayi fillinging daita ta zube qasa tana dubansa "yayinda shi kuma yake  jifanta da wani mummunar kallo,"bai ce mata komai ba dan idan ma ya nuna mata yaji ciwon rashin samunta a cikakkiyar budurwa  zata iya cewa kishinta yake wanda shi kuma  har ga allah ba kishinta yake ba, kawai yadda ta munafurci mahaifiyarsa ta nuna mata cewar ita din mutuniyar kirkice yafi damunsa "kiji abinda zan fad'a miki kar na sake ganinki a kusa da mahaifiyata  domin ita din mutun ce mai tsarki "hannuwanta duka ta d'aura bisa kanta tana kiran "wayyo allah na shiga uku dan ko bai fito fili yayi mata dalla dalla ba ta fahimcesa fiyye da haka "shiiiiii  ! karki kuskura ki tasa min uwa daga bacci idan ba haka ba wallahi kinji na ranste sai na d'agawa uwarki da ubanki hankali kin dai san halina, Kinsan abinda zan iya yi dan haka stay a way from my mum ."yana gama fad'ar haka ya juya ya koma d'akin ya zauna kusa da mami yana kallon yadda take sauke numfashi normal ba kmar d'azu ba ."

Maryam kam komawa tayi Kan step ta zauna  ta raku'be jikinta waje d'aya tana tunani yadda zatayi "wani hanya zanbi ni maryam ya fahimci shine mutum na farko da ya fara sanina ya mace ?"babu wata hanya tunda rashin hakurinki ya janyo kika mallaka masa kanki baya cikin haiyacinsa zuciyarta ta bata amsa da haka “amman kuma ai kina da sheida ?tabbas kina dashi sister itace sheidata ta d’an ji natsuwa kad’an amman duk da hk hankalinta ba’a kwance yake ba .a hankali ta mike tsaye ta fara tafiya kamar mara laka ajiki jikinta ba qaramin sanyi yayi ba ganin irin kallon zargin da yake mata duk yadda taso taji haushinsa ko kuma taga laifinsa zuciyarta ta kasa kar'bansa amatsayin mai laifi ko wanda zataji haushi sai ma taga kamar ya fita gaskiya kuma kowaye dole irin kallon da zai mata kenan . idanunta taga suna ganin duhu akan kujera mai zaman mutun uku ta zube ta kwanta tana runtse idanunta ."

Karfe takwas saura maryam  ta farka ta sauke idanunta akan agogo bata sake yunkurin  komawa bacci ba ta tsaya ta gyara ko'ina tare da shiga kitchen da yin abincin da zasu yi breakfast dashi sai dai har lokacin zuciyarta cikin dar dar take  ta kasa jin sukuni dan hango katoton matsala wa rayuwarta take . Karfe goma gabdayansu ya'yan mami suka harllara a gidan kuma a dakin maryam .maryam  din ce kad'ai bata cikinsu tana parlour’n qasa cikin jimami yayinda ATA ke gabana mami yana magana cikin tsananin damuwa "dan allah sweetheart ki bari na fitar dake zuwa kasar Índia a duba min lafiyarki murmushi iya baki mami tayi tana cewa "adamcy kenan baka son na mutu ko ?mami tayi masa tambayar idanunta na kanshi "wallahi banaso sweetheart!"Yayi maganar kamar zai yi kuka kallonsa kawai mami take without saying a word to him sai dai wani irin tausayinsa ne ya mamayeta da sauran yanuwansa  tabbas ta yarda kuma ta amince d'anta na mutuqar qaunarta damuwar dake yawo cikin rayuwarsa ne ya hanashi yi mata biyayya runtse idanunta tayi sai ga hawaye sharr yana sauka akan quncinta ".

hannunta ya riko gam cikin nashi yana cewa "why sweetheart?me yasa zaki zubar da hawayenki "ki daina kuka please idan wani abu kike so ki fad'a min am ready  do anything for you sweetheart idan kuma tafiyar ne bazakiyi ba wallahi na hakura bazan takura miki ba amman dai bana son na rasaki, dan a yanzu idan kika mutu ba iya yan'uwana ba hatta mutane gari ma sai sun min gori akan rayuwata aunty shahida ta kallesa tasan sarai daita yake maganarsa ."an waye gari  wai  yar'uwata ce da kanta tamin gori sweetheart a karon farko naji na tsani kaina duk da nasan tayi min né akan abinda nake miki ,nasan na sakaki cikin damuwa sweetheart ki yafe min lafifukan da nayi miki abaya da wanda zanyi a gaba nasan kina sona da  wannna yarinyar  ne yasa kema kike takura min amman dan allah ki yafe min tsanar da nake fad'a miki inawa yarinyar a gabanki  nasan tana sakaki cikin tsananin damuwa "wallahi sweetheart na sha fad'a miki Kiyi min addua ko allah zai saka min soyayyarta acikin zuciyata amman har yanzu shiru babu wata alama ta qaunarta "ya qarashe maganar muryarsa na rawa mami ta kallesa  idanunta cike da ruwan hawaye tace "tabbas yawon fadar tsanar da kakewa maryam tana bata min rai amamn adamcy na  yafe maka duniya da lahira burina allah ya had’a hankulanku waje d'aya ."

d’aya bayan daya yan'uwansa suka baro d’’akin zuwa parlour suka had'u gabadayansu suna hira har da maryam    nan  aunty shahida take basu labarin abinda ya faru "kai auntynmu dan allah da gaske ?wallahi ga maryam ku tambayeta "gaskiya auntynmu kin gama da yayanmu "inji cewar zabiba maryam ta mike tana mai jin tsananin farinciki yadda yan'
uwanta kuma dangin mijinta suke matuqar qaunarta aunty khadija tace "ai gara da,aka gama dashi baki ga yayi laushi ba duk ya canza kala kamar bashi ba ,yaro sai shegen taurin kai da fadin ran tsiya ai ni wallahi mami tayi min daidai ai da mun san d'an wannan shirin film din zai dawo dashi haiyacinsa da tunin an dade da wuce gurin aunty khadija ta qarasa maganar tana miqawa zabiba hannu suka tafa  ."
“Allah dai yasa buqata ta biya." nana hauwa'u tayi murmushi tare da mikewa tana cewa “in sha allahu ta biya sai fatan alkhairi ta shiga kitchen inda maryam take  qoqarin  gama tuwon shinkafa da
miyar agushi .”

tun daga falo kamshin miyar  ke shiga hancin nana hauwa'u har sai da yasa yawunta  tsinkewa "matar yaya wannan kamshi haka kamar zaa tafi gasar abinci "kai sister yau kuma tsiya zaki min "?”ke mu bar wannan maganar yaya had’uwarku  da yaya ta kasance daren jiya ?"nan da  nan yanayin maryam ya sauya idanunta suka canza kala alamun zatai kuka "babu wani jin dadi sister yayanki wani kallo yake min wanda bazan iya fitowa na bayyana shi ba .nana hauwa'u ta dafa kafad’anta "karki wani daga hankalinki ko sarewa "me yasa zaki fad'i hka wallahi sister a matukar tsorace nake "ba gani ba meye abun tsoro ?nana hauwa ta fad'a cike da kulawa maryam bata san sanda ta rungumeta ajikinta ba tana share hawayenta ."shadaya da rabi  daidai ata ya sauko ya fita daga gidan kuma alokacin maryam ta gama komai har da miya suna tsaye suna hira da nana hauwa’u inda nana hauwa’u take fad’a mata ciki gareta wani ihu mrym tayi ta rungumeta “gsky sister am very happy for you Allah ya hada miki komai da komai “kema sister kiyi ahankali fa dan baki sani ba ko ciki gareki mrym ta zaro ido waje “sister ina jin tsoron abinda zai biyo baya “ina nufin an samu a daren jiya “allah yasa ai da ni kad’ai nasan irin farinciki da zanyi dan ko baya so zan rike abina bare ma da gudu zai kwace suka dariya basu gama rufe bakinsu ba kawai suka jiyo  sautin muryar ATA cikin hargagi da tashin hankali .”

"ku yanzu daku zaa had'a baki ayi min haka "? a she yadda nake qaunarku ku ba haka kuke qaunata ba  ?"daman na dade dasanin haka ,na gode allah ya saka da alkhairi ku tashi ku bar min gidana gabandayanku bana son ganin fuskokinku” ya qarasa maganar adaidai lokacin da su maryam suka fito rike da hannun juna a bakin kitchen suka ja suka tsaya jikin maryam banda rawa babu abinda yake ".dan kwata kwata bata son ganinsa cikin tashin hankali
“Ya kalli inda maryam suke tsaye ya nunata da yatsan hannunsa “kema bazan qara zama dake ba ki  tattara duk abinda kikasan naki ne acikin gidan nan ki bar min gidana na sake ki saki u…”cike da tashin hankali aunty shahida tayi wani Irin qarasowa inda yake ta rufe masa baki tana girgiza masa kai tare da nuna masa yatsanta d’aya alamun d’aya zai furta maryam kuwa tun kafin ta gama ji ta d’aura hannuwanta duka bisa kanta tare da shiga wani sabon tashi hankali"wani laifi suka masa haka ?ta jefawa wankakkiyar kwakwaluwarta tambayar ."

inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shine  abinda nana hauwa'u ta shiga furtawa tana maimatawa wanda yasa maryam ta kama tana yi bakinta na rawa wannan wace irin maseefa ce inji cewar aunty khadija dan gabadayansu babu wanda jikinsa bai d’auki rawa ba maryam kuwa tashin hankalin da take ciki ya hanata kwakwaran motsi a inda take tsaye magana take son yi koda kalmar hakuri ce garesa amman ta qasa furta komai numfashi kawai take ja ta bakinta tana fitarwa dashi da kyar .”
alamarin ATA ya girmi tunanin yan'uwansa suna kallonsa ya buga ma aunty shahida razananniyar tsawa bayan ya cire hannunta “cikin tsananin tashin hankali da fad’uwar gaba take rokonsa "Adam ba’a saki cikin fushi idan kuma ya zama dole sai kayi kayi d’aya wani mugun kallo yayi mata yana mai janye jikinsa daga nata ya sake maida kallonsa ga maryam “tsayuwar me kike yiwa mutane maza ki fara qoqarin bar min gidana ,kuma haka banason ganin kowacce acikinku wallahi na tsaneku sannan na cire kaina acikinku aunty khadija ma tayi karfin halin qarasowa inda yake yayi saurin ja baya "bana son jin komai kawai kuje tunda kunfi son farincikin yarinyar nan akaina shekara nawa ina fama da zazzafar qaddara amman acikinku ko sau d'aya babu wacce ta zaunar dani ta fahimceni amman dan rashin Imani irin naku daku aka had'a baki na kusanci wannan guntuwar yarinyar wallahi kun cuceni .””ai tun daga zuwa d’auko shahida ya kamata ace na fahimci akwai wani abu a qasa amman babu komai kuje na gode .”
Chapter 66 · 0% Book details