← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 102

Sashe 67

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mamaki da matsanancin tsoro suka kama maryam “daman akan ya kusanceta ne ya zartar da wannan hukuncin akanta? ganin maryam bata da niyyar bar masa gidansa ya qarasa inda take ya kamo hannunta yana ja bata iya ce masa komai ba sai ma binsa da take har ya kai bakin kofa ya bud'e tare da hanka d’ata waje ya maida kofar ya rufe da karfi wasu hawaye masu zafi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta tana gogewa wasu na sake biyowa kuncinta ."ATA na gama juyo idanunshi ya sauka akan mami tsaye ,cikin tsannain tashin hanakali take kallonsa muryata na rawa tace "me ka aikata  haka adamcy ?yanzu sweetheart har za’a had’a baki dake a cutar da rayuwata ?ban shirya yin rayuwata da wannan yarinyar ba saboda me zaa min karya da ciwonki ?numfashi mami ta sauke tana kallonsa "dan haka na saketa saki uku dan bazan qara zama daita ba gabad’aya babu wanda bai furta kalmar “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ba har mami dan kam sai data dafe qirjinta dan wani luguden bugu yayi .”

nana hauwa'u ta qaraso inda yake cikin rud’ewa da rawar jiki ta riko hannunsa ya fixge "har ke ban cireki acikinsu ba kuyi rayuwarku nayi tawa tunda bakwa sona nima na hakura daku har abada zabiba ta bud'e baki ta soma  magana cike da in ina "ni ..ni dai yaya wallahi banda ni dan ba dani aka shirya komai ba hasalima yau din nan nasan komai aunty kahdija ta ta'bata alamun tayi shiru amman ta zame jikinta "dan allah yaya karka mana haka wallahi muna tsananin sonka muna qaunarka ta durkushe kasa tana jan gwiwowinta zuwa garesa ya tsaidaita ya juya ya haye sama a matukar fusace yake taka step ."wani irin naunayen ajiyar zuciya suka sauke atare "mami ta kallesu daya bayan tace "garin yaya kuka yi wannan kuskuren ?yaakayi kuka bari yasan komai ? tayi masu tambayar ajere cikin tsananin tashin hankali,gbdynsu sukai shiru dan basu da bakin magana ta sake sauke ajiyar zuciya "ina maryam take ? tana waje ! nana hauwa’u ta bata amsa cikin kuka kai tsaye kofar mami ta nufa ta bude inda taci karo da maryam durkushe tana zubar da hawayen mami ta kai hannunta ta d'ago ta ta rungumeta ajikinta tana shafa bayanta .”

jinta ajikin mami yasa ta sake fashe da wani sabon kuka mai ta’ba zuciya " dan allah mami ki fad’awa yaya bani da masaniya akan komai ,kuma allah danasan shiri ne ciwonki da bazan ta'ba amincewa ba gara na cigaba da rayuwata haka dashi "kukan ya isa haka abinda ya faru ya wuce ba kuma zai gogu ba ta zareta ajikinta suka koma parlour'n ta zaunar daita akan kujera sannna ta zauna a gefenta tana rarrashinta "yanzu mami ya zaayi kenan ? "ku da kuka tona asirin komai sai kusan yadda zakuyi dan babu ruwana ,ban da son jawa mutane tashin hankali meye abun baje hira a gidansa alhalin kusan halinsa? Kiyi hakuri mami ki yafe mana inji cewar aunty shahida "mami dan allah kije ki shawo kansa ya janye sakin ya maidashi d’aya Ke kadai ce zaki iya shawo Kan yaya nana hauwa’u ta fad'a tana share hawayenta "da sauri maryam ta kalli inda take zaune “sister saki ukun yayi min kenan ?nana hauwa’u ta gyad’a mata kai alamun “eh!ahankali ta runtse idanunta gam tana jin wani irin rad’ad’i da ciwo acikin zuciyarta wallahi tayi wa kanta alkawari muddin ba ita ce acikin gidansa ba babu wacce zata zauna cikinsa cikin jin dadi, duk inda ake zuwa dan biyan buqata zata domin ta hanashi jin dadin rayuwa kuma duk runtsi sai ta dawo gidan zaman lafiyarsa ya janye sakin kamar yadda sister ta bada shawara bata gama fita daga wannan tashin hankalin ba taji muryar aunty zabiba ta karad’e parlour’n “.

“gsky mami ya kamata mu ajiye son rai a tsaya a duba lamarin yaya shima tunda ya nuna baya son aurenta kar a wani maidashi a hakura kawai allah ya hada kowa da abinda yafi zama alkhairi .” da sauri maryam ta bud’e idanunta ta kalli inda take zaune qirjinta na wani irin bugawa "bayan ya gama maidaita qaramar bazawara zaki fad'i haka ? aunty khadija ta fad'a a  fusace "to meye amfanin wannna auren tun kafin ayisa yace bai so ?tunda akayi auren nan ku fad'a min rana daya wanda muke da kwanciyar hankali ?”kullum zuciyarmu cikin fargaba take, yin aure halal ne haka barinsa halal ne idan ma zai gare rayuwarsa haka abarshi mana matsawar bazai dinga biye biyan mata ba ,”tunda suka fara magana a tsakaninsu mami bata ce uffan ba har Qarfe uku ATA bai sauko ba gabdaya cikin damuwa da tashin hankali suke most especially maryam wacce har wani rama tayi nana hauwa’u dake kusa da maryam ta dinga kwantar mata da hankali “sister karki d’aga hankalinki yaya zai janye sakin da yayi miki yanzu fa kin rigada kin zama jinin jikinsa jininsa gauraye yake da naki wata killa ma akwai ajiyarsa ajikinki shiru kawai tayi dan bakinta bazai iya furta komai ba dan hatta miyon bakinta ya qafe idan tayi qoqarin had’iye wa jinsa take tmkr mad’aci ."

Da misalin karfe biyar ne mami ta mike ta haura sama ta shiga dakin ATA ta iske shi zaune akan kujera kwaya d'aya dake dakin yayi baya da kujerar yana kallon saman d’akin ganin shigowarta ya runtse idanunshi  gam .da sanyin jiki mami take qarasowa inda yake stood ta janyo ta zauna gabansa ta zuba masa ido tana kallonsa tana nazarinsa dakin yayi shiru tamkar babu kowa aciki  har tsawon minti goma mami na zaune agabansa yadda batayi magana ba haka bai bud’e idanunshi ba ta kira sunansa "adamcy nah! shiru ne ya sake biyowa baya ta kai hannunta ta kamo hannunsa ta kai bakinta tana sheshekan kuka saukar hawayenta yaji a hannunsa ya d’an bud'e idanunshi akanta tabbas hawaye ya gani yana sharara akan kuncin mahaifiyarsa abinda ya tsani gani kenan naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske sannan ya kai dayan hannunsa yana d’auke mata hawayen fuskarta dake kwarara sannan ya motsa lips dinsa da kyar "why sweetheart?Bata ce masa komai ba illa cigaba da zubar da hawaye "da fatan ba Adam bane yayi sanadiyar zubar hawayen nan ?ahankali ta gyada masa  kanta alamun shine.”

numfashi ya sauke yana son sanin dalilin kukanta "adamcy kana son saka sweetheart dinka  kuka,baka jin damuwa yadda kake  saka sarauiyar dad dinka  kuka ?mami ta furta tana  dago da idanuwanta ta zuba masa da matuqar damuwa "ina cikin damuwa adamcy !"nima acikin damuwar nake” jin sautin muryarsa cikin tsanani bacin rai ya qara d’aga mata hankali ya zame hannunsa ya mike ya qarasa qarahen dakin ya tsaya rike da kugunsa yana jin zafi da ciwon abinda mahaifiyarsa da yan'uwansa suka masa "."Adamcy na !ta sake kiran sunansa a karo na biyu yana jinta yaki juyawa mami ta cigaba da magana "ka sake min wani alfarma a karo na biyu adamcy .” ya d’an juyo a natse ya kalleta "kayi hakuri ka janye sakin da kawa maryam ka maidashi d’aya sannan ka maida maryam d’akinta saboda allah da girman mahaifinka da darajan haihuwarka da nayi "ya bud'e baki yi zai magana "karka ce aa adamcy ta katse shi ta hanyar fad’ar haka “kayi dan allah da mahaifinka da kuma ni da nayi silar zuwanka duniya domin muddin ka rabu da maryam zata shiga damuwa mai tattare da tashin hankali idan ta kasance cikin damuwa nima zan shiga domin nice silar komai .”

ya juyo sosai ya fuskanci mami "abu na farko tana rayuwarta batare da kai ba na shigo daita cikin rayuwarka, abu na biyu yanzu kun zama abu daya wayasani ma ko rabo ya shiga tsakaninku "gaksy ni sweetheart bana son abinda kike min akan yarinyar nan ban gama fita cikin matsala ba zaki sake shigo min da wata damuwa "ba zancen shigo da damuwa bane adamcy naji hakan ajikina akwai rabo a tsakaninka da maryam .”yayi shiru kawai yana mamakinta a ransa yace “ai kuwa badani ba dan bazan sake gigin kusantarta ba kuma ni bana jin haka ajikina domin spam din daya fitar ba d’a bane dan duk spam din da zai zama d’a fitarsa nada matuqar wahala daga jikin d’an adam mami ta d'an yi gyaran murya "ni mahaifiyarka ce zan iya sakaka kayi min abu dole koda kuwa ranka bai so amman a wannan karon banason na maka dole alfarma nake sake neman da baka hakuri saboda dalilai masu yawa dan allah ka janye ka kuma maida maryam iska ya fesar mai zafi daga bakinsa sannan yace "shikenan naji na janye na maida ita ."iyakar abinda ya fad'a kenan ya fice daga dakin domin idan ya cigaba da tsayuwa zata nemawar yanuwnasa afuwa abinda bazai so ba kenan shi dasu har abada .”

“Alhamdulillah! mami ta dinga furtawa tana nemammansa afuwa da sauki a wajen Allah suna zaune jugun jugun ya sauko ya nufi kofa "zabiba ta zabura ta mike zata bishi aunty shahida ta dakatar daita tana cewa "da alamun kin fara manta waye adam arayuwarki wallahi zamanki matar aure da ya’ya bazai hanashi yi miki mugun bugu ba mu barshi har ya sauko da kanshi "ni dai zan wuce gida dan bazan bari wannan fuskar ta sake shigowa muyi ido hudu ba inji aunty khadija gabdaya suka kwashe da dariya ban da maryam wacce idanunta sukayi jajur tsabar kuka” nima tashi zanyi na wuce nasan mami zata shawo kansa suna shirin mikewa mami ta sauko "mami ni zan wuce gida inji cewar aunty khadija itama zabiba ta gyara zaman mayafinta nima zan gudu dan yau sai wani ikon allah ,allah yasa dai ya sauko "kun gama hadasa mana tashin hankali shine zaku gudu daya bayan daya ?"dan allah mami Kiyi hakuri bamu san zai dawo ba tunainmu fitarsa yayi nisa "ai shikenan tunda ya janye sakin .""
Chapter 67 · 0% Book details