← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 102

Sashe 58

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyar maryam wani irin zafi take mata da tuttukin bakinciki tana jin wata irin tsantsar soyayyarsa na sake ratsata baza ta'ba kuskuren rabuwa da yaya Adam tayiwa kanta wanan  alqawarin suna tare mutuwa ce kawai zata rabusu ,koma yayi qoqarin rabuwa daita baza barshi ba tagumi ta zuba cikin zullumi da rashin sanin madafa dan bazata iya  aikata abinda mami take buqata ba ,duk magiyar da mami take mata amman maryam taki bud'e baki tace zata rabu da ATA." sosai mami ta fahimci soyayyar adamcy din ce mai tsanani ta hana maryam bin umarninta jikin maryam a matuqar sanyaye ta mike batare data kalli fuskar mami ba tace "mami dan allah ki bar maganar rabuwar nan haka ,ni abinda nafi buqata daga gareki shine addua ko kad'an yaya Adam ya soni  acikin zuciyarsa tana gama fad'ar tace "bari naje na kawo miki abun sha har tayi taku biyu ta taya "dan allah mami karki masa magana akaina  tana gama fad'ar haka ta cigaba da d'aga qafafuwanta ."

Mami tabi bayanta da kallo duk ta zube ,duwawukan nan nata duk sun kusan qarewa, ramar da tayi tasa ta qara kankacewa ,ta fito daga kitchen rike da cup da jug  ,kawai taga mutun tsaye kikam tamkar wani jami'in tsaro cikin wani had'ad'den suit ash colour haka ma takalman dake sanye a qafafuwansa ash ne sai sheki suke ,tsintsiyar hannunsa makale da agogon rolex  ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ga sihirtaccen kamshin turarensa mai tsananin kamshi ,nan da  nan kamshi  parlour'n ya canza zuwa na kamshinsa  ."suka tsurawa juna ido shi yana kallonta cike da tsantsar tsana yayinda ita Ke kallonsa cike da tsantsar qauna  satinta uku  kenan bata sanya shi acikin kwayar idanunta ba
bata san tayi kewar ganin kyakkyawar fuskarsa ba sai a yanzu  da take kallonsa tsaye agabanta ,kullum kamar qara masa kyau ake sam bazaka ce 40 garesa ba ,ga kamshin daddan turarensa duk inda ya shiga sai anji wannan mayataccen kamshin nashi  mai tsayawa arai da dagula lissafi,taji kamar tayi wulli da cup din hannunta taje ta rungume shi ajikinta taji d'umin jikinsa ."

Qaramin tsaki yaja ganin yadda take kallonsa kamar bata ta’ba ganinsa ba arayuwarsa baya son yawon kallo ya d'auke kwayar idanunshi  ya qarasa shigowa sosai ya zauna kusa da mami ya baje akan kujera  yana furta "wash allah nah na gaji “yayinda maryam ta qaraso tayi masa sannu da zuwa aciki ya amsa mata shima ganin mami zaune ne ,a natse maryam  ta  fara hidima da mami "sweetheart a she dana  biya ta  gida bazan sameki ba ?"tace uhm bazaka sameni ba amman nasan ko kwanaki nawa kayi zaka zo ka sameni  zaman jiranka  kallonta kawai yayi ya d'an ciza lip's dinsa yana d'aure  fuskasa dan ya fahimci kamar akwai wata a qasa . mami ta kalli maryam dake zaune kusa daita taga ta girgiza mata kai  alamun karta masa maganarta take ta fahimci abinda take nufi numfashi ta sauke inda ATA ya fara jan mami da hira maryam ta tashi ta dawo gabansa ta tsugunna yayi saurin janye qafafuwansa tmkr yaga mugun abu numfashi ta sauke ta sake matsowa ta kai hannuwanta ta janyo qafafunsa saurin runtse idanu yayi yana jin kamar da wuta ta ta’ba shi .”

Ahankali yaji ta soma kwance igiyan takalminsa d’aya kamar ya zare qafarsa ya buga mata takalmin a fuska amman ya share sakamakon darajan mami dake gurin ,tana gama cire masa takalman ya janye qafafuwansa ta kwashe takalman ta nufi hanyar step  ."ya bud’e idanunshi ya cigaba da jan mami da magana acikin hirarsu da mami take fad'a masa kwanakin nan zuciyarta na mata nauyi "wallahi adamcy bana jin dadin zuciyata jiya fa da kyar na samu na runtsa numfashina kamar zai bar gangar jikina "haba sweetheart ya zaki min haka?ya  kina jin ciwo ajikinki amman ki kasa fad'a min ko fad'awa aunty shahida  "yaushe rabona da kai adamcy ?” duk ya’yana suna zuwa su duba lafiyar jikina ,amman kai  yaushe rabon kazo wajena ?idan dai mai rabawa ta rabamu ai shikenan kowa ya huta ko da yake kai ne zaka huta idan na mutu amman sauran zasuji babu dadi "allah ba zai sa naga wannan ranar ba "kema kinsani sweetheart kina cikin raina da bamu raba gida ba ,babu abinda zai sa kiyi rashin ganina a duk lokacin da kika só ,dole duk tsananin aikin daya sakani gaba dole zan dawo gida na kwanta .”

“  wallahi yanayin aiki ne yanzu da kuma d’a nisan da mukayi amman da zaki min  alfarmar rabuwa da auren nan da na huta domin zan dawo gidanki gbdy ta yadda zan dinga kula da duk wani motsinki "kaji dashi idan zaka kare kanka kayi amman babu ruwan aure da rashin zuwanka akai akai "to ma meye amfanin auren?me  zanyi dashi tunda  bana sauke nauyinsa dake kaina shiru mami tayi tana nazarin maganarsa "to ma meye amfanin auren?me  zanyi dashi tunda  bana sauke nauyinsa dake kaina ta sake maimaita abinda ya fad'a tayi wa maganar falla falla domin fad'a dashi dan ta fahimci abinda yake nufi idan dai ta fahimta bayan rashin kwanciyar hankalin da baya bawa maryam har da hakin aurenta baya saukewa  kamar tace ya sauwake wa maryam din kowa ya huta amman maryam din take ji a halin yanzu ,domin dukkanin alamun sun gama nuna soyayyar adamcy tayi mata kamun kazar kuka "sweetheart Kiyi hakuri ki yafe min na kasa miki biyayya na kasa son abinda kike mutuwar so "wannan son ranka ne kake fad'a da nuna baa isa da kai ba "bai sake cewa uffan ba akan maganar da take sai ma canza magana da yayi zuwa ta lafiyarta "sweetheart ki shirya  next week zamuje India a duba min lafiyarki "a'a ni bana buqatar zuwa koina anan ma ina samu kulawar shahida tana iyakar qaoqarinta akaina "dan sweetheart ki amince please ".

“na yafe adamcy abarni anan idan ma mutuwarce na mutu acikin ahlina allah dai ya bamu saar tafiya tunda yaji inda mami ta dosa  ya lalubo wayarsa  ya kira musa yana  bashi umarnin yayi  order abincin mutun biyu "mami ta kallesa a tsanake  tare da katse masa hanzari ta hanyar cewa "mai yasa za'ayi order abinci bayan ga matarka a gida  ?"shiru yayi yana karkad'a qafa "me ye amfanin haka adamcy ?"allah ya rufa maka asiri ka nemi ka tonawa kanka "sweetheart ya kike magana haka kamar baki san shirmen yarinyar nan ba ?"ai cin abincin wannan sakar yarinyar daidai yake da cin guba ai sai ta kashe mutun da yaji da maggie "yayi mgnr  a matuqar fusace yana jan tsaki kana ya cigaba da bawa musa umarni yana gama wayar ya mike da kyar ya hau sama ,a bakin kofar d'akinsa yaga ta ajiye masa takalmansa ,ya bud'e dakin sannan yasa hannu ya kwashe  takalman ya shige dakin,wanka ya shiga bai wani d'auki lokaci ba ya fito bayan ya shirya kansa cikin  kananan kaya ya sauko ya zauna alokacin maryam tana tare da mami tana tmbayarta abinda zata girka mata "ki girka min duk abinda kike dashi  maryam zanci “ata ya zauna adaidai lokacin da maryam ta mike zata nufi kitchen muryarsa can qasan makoshi yace "ke.."!

Ta tsaya cak a natse tare da juyowa ta fuskancesa "karki dafa mata wannna banzan abincin naki “
mami na qoqarin bud'e baki musa  yayi knocking ya bashi izinin shigowa musa ya turo kofar parlour'n ya shigo cike da girmama ya gaishe da mami sannan ya rusuna ya gaishe da ATA ya ajiye ledodin hannunsa ya juya da sauri ya fice ."ATA ya janyo ledar farko dake gabansa  ya bud'e kamshi kifi tilafia ya doki hancin maryam wanda yaji kayan hadi da arish had'in  kabej  da sauri ta had'eyi miyo , ya tura takeaway gaban mami yana cewa  "sweetheart bismillah shiru mami tayi taki ci "tana son yi masa maganar abincin da ya hana maryam girka mata da kuma abincin da babu a gidan amman tana  jiwa maryam tsoron bala'insa dan haka dole itace zata kawo mata komai na bukata ta ajiye mata batare da saninsa ba "sweetheart eat !ni babu abinda zanci gida ma zan wuce mami ta fad'a tana haramar  mikewa nan take   ATA yace"a'a sweetheart  kiyi zamanki babu inda zaki "bangane babu inda zani ba ?"haba sweetheart ya kike magana hk kamar kina jin haushina ?saboda ke nasa akayi order abincin nan amman duk kinki ci komai ,nifa ban gane miki ba “idanu ta zuba masa tana kallonsa ta rasa wani irin mutun ne shi ,babu yadda zatayi magana bai canza mata magana ba dan haushinsa tana ji amman meye na fitowa ya fad'a mata ?"dan Allah sweetheart kici komai da nayi miki order "tunda kake dani ka ta'ba ganin naci abinci order ?"yayi shiru yana furzar iska “da kayi order dan ni nace mka zanci ne ?"kai kafi kowa sani bana cin abinci waje kuma kai ma akan haka na raineka ina da tabbacin ko kana cin abincin order sai dai idan baka qasar nan kai ya langwabar yana dubanta dan gskiya ta fad’a.”

“dan haka kafi kowa sanin bana cin abinci waje kuma kaima haka duk abinda nake so ina yi da kaina ko nasa kuku su dafa min amman dan ka wulakanta matarka kake wani aikawa a siyo maka abinci daga waje idan ma nata ne baka buqata ai zaka iya daukar mata kuku ko wane su girka maka acikin gidanka
Mami na fadar haka gaban maryam ya bada rasss "kuku a gidanta a'a ?ina bazai yuwu ba bata son kowa atsakaninta da mijinta tafi bukata ganin gidanta daga ita sai mijinta gabanta na fad'a uwa ta zubawa ATA idanunta taji abinda zai fad'a."ba d'aukar kuka bane matslata sweetheart" meye matsalarka adamcy fad'a min meye matsalarka?"ko kuku nawa zan d'auka basu ta'ba  min abinda sweetheart dina zata min ba"wani boyayyen ajiyar zuciya maryam ta sauke "haka mami yadda yayi maganar sai kuma taji tausayinsa ya lullubeta “duk abinci nan da nake order nake ci wallahi ina dai turawa cikina ne kawai amman maganr gsky ni abincinki nafi bukata fiye da kowani abinci a duniya, idan kina son na daina order  abinci sai dai idan zaki dinga mana kina aiko mana amman sai ta qara hade rai tana zabga masa harara ".
Chapter 58 · 0% Book details