← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 102

Sashe 52

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"haba maryam yanzu  sai na tsaya na  koya miki "menene amfanin social media din da kike yi ?group's gareki fa  sunfi ashirin da wani abu sannan ina karatun novels din da kike? uhm maryam ta sauke numfashi da ajiyar zuciya tana cewa " nifa wallahi yayanki tsorata yake, ko nayi niyya yi wani abu  sai tsoransa ya shigeni na fasa .da dabara zaki dinga shige masa kawai Kiyi qoqarin kisan weekpoint dinsa bazai ki ba "sister nasan duk wani week point din nmj ,kunnuwansa nipples dinsa sumar kanshi uwa uba jijiyarsu amman yayanki  baya yarda na ra'bi inda yake bai ma son ya bud'e idanu ya gani bare a kusa dashi ai shiyasa nake fad'a miki yaya hisham mutumin kirki ne ,wallahi sister kin samu miji a yadda kuke gudanar da rayuwarku yanzu bana jin zai auri nuzla .ke babu ruwanki da sheidar nmj na fad'a miki duk nmj dake da mata da buduruwa a waje baki biyu garesu idan ma zai aureta suje can su qarata ni dai a kwantar min da hankali abinda zan fad'a miki Kiyi qoqarin ki rage tsoransa kinji sun jima suna waya kafin sukai sallama ."

Bayan kwana biyu  suna cikin waya da nana hauwa'u taji yana buga kofar d'akin da karfi da sauri tace "sister gashi nan yana buga kofa  ina zuwa ,ta ajiye wayar batare data kashe ba, ta mike tsaye tun kafin ta isa bakin kofar taji yana cewa "gidan ubanki ne da zaki dinga kulle kofa ?maryam najin abinda ya fad'a tayi hanzarin ta bud'e masa kofa tana "cewa duk abinda zakayi yaya adam kayi kuma ya tsaya a iya kaina kawai  amman zagin iyaye bazan sake d'auka ba ATA najin abinda ta fad'a ya gyara tsayuwarsa da kyau abun ya mugun girgizasa  ganin yadda yake kallonta ta juya ta shige cikin d'akin tana cewa "ka zageni kaci zarafina ni naji na gani zan d'auka amman iyaye please kayi qoqarin ka daina sakosu ."ai ko babu komai dady mahaifi ne gareka idan bakayi masa addua ba ai kuma bai cancanci zagi ba  ta fad'a tana rungume hannuwanta duka a qirji ."

A wulakance ya d'auki kallonta daga qasa har sama kafin a hankali  ya shigo har cikin d'akin ya tsaya  yana  kallon yatsun kafafuwansa a hankali ya motsa lip's dinsa "say what you said again ina son tabbatar da najiki da kyau tayi shiru taki cewa komai "gidan nan ba gidan ubanki bane ba kuma da kudin ubanki na gidana shi ba na maimaita abinda na fad'a ina son kema idan kin isa ki maimata abinda kika fad'a yanzu ." ya fad'a mata haka  kai tsaye kamar bashi ba "daman baa sonki   ko digon d'aya baki da matsayi acikin nan ya nuna daidai saitin zuciyarsa da yatsan hannunsa "baa sonki amman kike qoqarin shigo da wani salo rashin kunya to zaki sha wahala akan wahala dan ko ina sonki bazan d'auka  ba bare babu d'igo  sonki acikin nan.ina dai  zaune   dake darajan iyaye ,rayuwar mahaifiyata ke rike da aurenki yau ta fad'i ta mutu kisani aurenki dani ya qare dan rabuwa zanyi dake da huta ."

"yanzu mami na mutuwa zaka rabu dani "?yes of course zaman me zan cigaba da yi dake zan rabu da kwallon mangaro na huta da kuda ,baki san kin  zame min qaya bane  ? ta runtse idanunta she's so much in love with him amman shi kullum tunaninsa  yadda zai rabu  daita , "dan allah meye ribar ka yaya adam da baka son  yiwa mami biyayya   ?ta tambayesa muryarta cike da rauni "ai duk akanki ne na kasa wannan biyayyar kinga kuwa bazan ta'ba sonki ba har na koma ga allah" bazakayi mata biyayya bayan ranta ba "ubanki zanyi ba biyayya bayan rai ba "ya fad'a a zafafe  yana jan tsaki yare da  dafe goshinsa can kuma yace "me keyn d'akina yake ajikin keyn kitchen?tayi shiru tana dubansa a matukar tsorace "me keyn d'akina yake ajikin keyn kitchen?" ya sake maimaitawa  a karo na biyu hankalin maryam ya tashi  sosai ta masa baya da sauri tun kafin ya sauke mata mari ".

"don't let me rept my self wallahi idan baki fad'a min abinda yasa yazo hannunki ba zan baki mamaki yanzu .maryam ta sake tsorata dan tasan zai iya aikata komai tunda ya rantse muryarta na rawa "tace daman saboda na dinga gyara maka d'akin ne "na buqaci haka daga gareki ?"a'a kawai dai ni naga dacewar haka ne shiyasa "tunda nayi tafiya kina sharewa ?tace "eh ina sharewa "kina sharewa amman kuma naji d'akin yana warin mushe ya d'ago yana kallonta tsab  yana nazarinta  "dan allah dan annabi dan darajan iyayenka karka min komai  ta fad'a haka ne saboda kusancin da suka samu komai zai iya faruwa.tunda ya tsura mata tsumammun idanunshi bai sake cewa uhm bare uhm uhm  ba sai dai kana kallonsa zaka fahimci ya gaji da damuwarta
"Dan girma allah Ke wace irin halitta ce ?duk abinda mutun bai so shi kike yi ni wallahi na gaji dake dan hannuna ya gaji da ta'ba jikinki."

"Kayi hakuri nima jikina ya gaji da duka da mari
"To zaman me kike yi ?"ai  sai kin bar gidan  kuma bari na har abada  ba sai kin qara dawowa cikinsa nonsense kawai "yana gama fadar haka ya juya fuuuuuuu naunayen ajiyaar zuciya ta sauke kuma sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta  safa da marwa ta soma kafin ahankali ta tsaya a tsakiyar dakin ta hade hannuwanta duka guri daya bata ta'ba shiga tashin hankali da nadama irin wannan ba, domin har ga allah ta gaji da zama dashi amman kuma zuciyarta na kanshi  sonshi bai ragu acikin zuciyarta ba wayarta ta d'auka nan taga ashe  har lokacin nana hauwa'u na kan layi ta sauke ajiyar zuciya tare da furzar da zazzafar iskan daga bakinta muryarta a sanyaye  tace "sister Kiyi hakuri ashe ban kashe wayar ba kema kuma baki kashe ba "tausayinta ya kamata nana hauwa'u "har zuwa yaushe ne  zaki fita daga cikin wannan matsalar."

" wannann tsana tayi yawa zuciyata karon kanta ta gaji da ganin halin da kike ciki na fahimci qiyayyar yaya mai karfi ce akanki ya kamata mami ta dauki mataki mai karfi a kansa" yanzu sister me kika ga  zanyi domin kawowa kaina sauki "maryam ta tambayeta "son da kikewa yaya yayi yawa gashi kuma baya samar min da kwanyar hankali  ?"bari dai yau na  kira yaya da kaina nayi masa magana ya sausauta miki maryam wacce idanunta suka cika da ruwan hawaye tayi saurin cewa "a'a sister  karki masa magana "dan me yasa zaki ce aa?"kinsan halinsa  yanzu zai dauka kararsa na kawo tsaki taja tayi discounting din kiran  da kukan nana hauwa'u ta kirasa "a zaune  yake yana kallon labarai amman bai sanda ya mike tsaye ba "a'a auta lafiya kike wannan uban kukan ?"me hisham yayi miki auta?"

Cikin kuka  tace "haba yaya me yasa kake wa maryam haka ?au qarata ta kawo miki ko me ?sam sam bata kawo qararka ba, nan dai tayi masa bayani yadda akayi taji "dogon tsaki yaja " ke bazaki gane wannan yarinyar muguwa bace sannan makarya ce gata da siffar munafukai gabad'aya alamunta na rashin gsky ne, nifa ban ta'ba ganin makirar yarinyar kamarta ba ga taka min dokoki da take  "Allah yaya sister nada kirki kuma tana sonka "kinga auta ajiye maganar so wannan yarinya muguwa ce na fad'a miki "wallahi yaya zuciyar maryam a wanke take akanka ,haduwar aurenku daita baku kuka tsara ba allah ne  dan yaya adam kayi hakuri da yadda qaddararka tazo ,sannan sister bazata taka  duk wasu dokokinka ba tana da gudun zuciya gashi ita din mai biyayya ce . Kayi mata sausauci dani ina son naganta cikin farinciki kamar yadda na kasance a yanzu , bata ragewa ATA komai ba akan canjin rayuwar daya kawo a gidan aurenta a sanadiyar matakin da yayi qoqarin dauka akan hisham "

"to yaya ya kake tunani idan maryam tana da yaya ?shima zai dauki mataki kwatankwacin irin wanda ka dauka akaina amman sai ya kasance sister bata dashi  bata da kowa sai allah da kai ,nayi imani yaya a yadda kake son yanuwanka ko wani kaga yayi mata haka sai inda karfinta ya qare dan allah ka sausata mata sister na sonka fiyye da soyayyar kowa da zaka bata dama zakaji dadin rayuwa daita" ata ya kalli tv yana jin haushin maganarta amman dan ya kawo karshen zance yace "naji sai anjima kafin tace wani abu ya katse wayar  yana jan tsaki ko ana soyayya dole tunda nace bana yi a rabu dani mana bata ga wahala bane da qafafuwanta zata arce na huta da jaraba   idan taki  km zan san yadda zan batar daita a nemita a rasa haba wannan naci da maseefa ya isheni kowa maryam idan aunty sajida ta kira maganar kenan maryam duk yan'uwansa  maryam dai maryam shi ko Oho babu wanda ya damu da damuwarsa ."

Bayan kwana biyu maryam ta d'an samu natsuwa sakamakon baya shiga lamarinta sabgar gabansa kawai yake sai dai ita tana iyakar qoqarin na bashi duk wata kulawa idan yana gida kullum kafin ya fita aiki zata kula dashi idan ya dawo ma haka wasu ayyukan yace bai so wasu kuma miskilanci ya hanashi magana sai dai yayita cika yana batsewa.
Yadda take kula dashi  ita bata isa ya nuna mata kulawa ko tausayawa ba idan kaga annuri a fuskarsa to baki yayi  amman ita ko oho kuma rashin mutuncinsa agaban kowa yake yi  wannnan yanayi yana sakata cikin tsananin damuwa sai ta zauna tayita kuka saboda tausayawa rayuwarta idan babu mami a raye tayi imani ko bai rabu daita  kamar yadda ya furta ba allah babu mai kwatarta a hannunsa ."
Chapter 52 · 0% Book details