← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 102

Sashe 33

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi sauri ta d'auka tana "cewa hello suby okay gani nan fitowa mgnr second biyu sukai  ta katse kiran tana cewa "aunty ni zan wuce subai'a har ta fito "kema yanzu zaki wuce ta kai cup din tea bakinta ta kurbi kad'an ta kai bread bakinta a haka ta shanye cup din tea tace "na gode sosai Allah bar min Ke mamana ina sonki ta kai mata kiss a kumatunta ta nufi kofar fita da sauri tana cewa aunty "bye ye sai na dawo "bye ta d'aga mata hannu tana kallon bayanta kai tsaye bangaren ummah ta shiga da sallamarta yaya sadam ta gani zaune  Jiki a sanyaye ta gaishesa "yaya sadam ina kwana?"ya dago idanunshi ya kalleta sannan ya amsa da" lafiya !"

ta nufi hanyar dakin ummah  sai ga umma ta fito"maryama har kin fito ?na fito umma to Allah yasa a dace  tace Ameen " ina zata ?ya tambaya batare daya kallesu ba "interview ! ummah ta bashi amsa da haka "aiki zatayi kenan ?" to meye amfanin karatunta idan batayi aiki ba ya dan yi shiru can yace "nifa gsky bana da wannan raayin yana gama fad'ar haka ya mike yana cewa " ni na wuce tsaya ka sauke  min ita "bai ce komai ba ya fita maryama tabishi da kallon mamaki dan bata ta'ba tunanin zata samu matsala dashi akan aiki ba ganin shima dan boko ne ita kam akan aikinta zata iya hakura da auren dan
sam aure baya ranta a yanzu mutuntakan umma ne ta duba  da tausayin mahaifiyarta bawai son aure take ba ,ganin yadda yanayinta  ya canza  yasa ummah tace "karki wani damu zakiyi aikinki "amman  ummah alamunsa ya nuna baya so "gsky ne sadam bai  son  amman zai yarda kinji  wahalar karatunki bazai tafi a banza ba ,yana ma daga cikin abinda yasa ban bari an daura maku aure ba nafi son  ki  shiga da aikinki". kanta kawai ta gyada mata "maza bishi ya saukeki ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 11

Jiki a sanyaye maryama take taku gabad’aya kuzarin jikinta yayi kasa ,”aiki zatayi kenan nifa bana ra’ayi ? maganarsa ta shiga yawo acikin kwakwaluwa da zuciyarta , tana tafiya tana tunanin maganarsa , a qalla yaya sadam ya kusan minti shabiyar zaune acikin motarsa yana jiranta , ya dubi agogo a karo kusan na shabiyar yaja qaramin tsaki a lokacin da wayarsa ta soma ringing ya kai hannu ya d’auka ya duba yaga sunan ummanshi ke yawo akan screen din wayar. numfashi ya sauke sannan ya d’auka cike da girmamawa “sadam !”ta kira sunansa ya amsa da “na’am “ina son kaso maryama tun daga qasan zuciyarka ,sannan zaka iya zama madadi ko ka cike gurbin abubuwan da maryama ta rasa a rayuwarta na shekaru baya.”

“ina jin ciwon da qunci abubuwan da sukai ta faruwa daita amman ina fatan kai ne zaka wanke min wannan quncin ya dawo farinciki na har abada “naji ummah in sha Allahu zan yi iyakar qoqarin na kawo miki wannan farinciki “dan allah sadam ka son maryama “ yayi murmushi kawai yana sosai keyarsa yayinda idanunshi ke kallon hanyar da maryama zata bullo .”ahankali yaga tahowarta a natse take yin komai nata kamar bata son taka kasa koma yace tausayin kasar take “nayi magana ba kace komai ba ? “duk abinda ummanah take so ya zama dole naso “ya fad’a yana sake tsaida idanunshi akanta “

“na gode maka allah yayiwa rayuwarka albarka yadda kayi min biyayya kai ma allah ya baka ya’yan da zasu maka biyayya “Ameen ya hayyu ya qayyum “
qirjin maryama na tsananin fad’uwa ta qaraso bakin titin unguwarsu har ta tsaya jikin motarsa bai iya d’auke kwayar idanunshi akanta ba ,jikinta a matukar sanyaye ta bud’e gaban motar yaya sadam ta shiga yayinda zuciyarta Ke bugawa da karfin gaske ta zauna tare da rafka tagumi cikin rashin sanin madafa madadin taji yaja motar sun wuce sai taji yayi sallama ya ajiye wayar hannunsa ya kunna music yana bin wakar ahankali .”

Kanta taji ya sara mata ganin bashi da niyyar tafiya ga lokaci na wucewa ya sata kallonsa kamar mai shirin yin kuka tace “yaya sadam !”tamkar ba magana take yi masa ba haka ya cigaba da bin wakarsa babu alamun damuwa ko nadama a fuskarsa hannu ta mika hakan yasa sukayi daf da juna wanda da zata qara matsar da hannunta zata iya yin masauki a jikinsa, a natse ta kashe wakar ta sake kallonsa tace “i am talking to you yaya sadam “.“me kike son na yi ?ya fad’a a sanyaye “kayi hakuri dan allah idan wani laifi nayi maka lokacin na tafiya gashi naga baka da niyyar tafiya wannan aikin shine rayuwata bana son rasashi .”

ya d’an matsota yana cewa “ni dana zauna jiranki tsawon mintuna shabiyar bani da aikin yi ne ?”ko bani da wajen zuwa ne?” ko kuma aikina bashi da mahimanci ne ?”yayi mata tambayar ajere yana sake kunna wakarsa .”sake kashe wakar tayi ta kallesa a marairaice sannan tace “am sorry duk maganarka ce ta rikitani har yasa kuzarina yayi kasa wallahi da kyar na kawo kaina bakin titin nan shiru yayi yana kallonta fuskarsa a d’aure tmkr wanda bai ta’ba dariya ba “ka d’an saki fuska nan dan fushi baya maka kyau “ ta furta cikin wani irin salo da sautin murya mai sanyi huci bakinta da numfashinta duka na dukan wuyansa wanda sanadiyyar hakan ya haddasawa tsigar jikinsa mikewa ya kuma qara bugawar da zuciyarsa take .”

ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani iri a ilahirin jikinsa “saboda nace bana ra’ayin aiki ?”wallahi duk shi ya sanyayyar min da jiki da dai zaka amince zanyi farinciki da hakan “bai sake cewa uffan ba ya kunna motar ya soma tafiya kamar wasu kurame haka suka cigaba da tafiya .”qarfe tara saura wasu mintuna suka isa bakin tafkeken get din Z&A yaja ya tsaya batare daya kashe motar ba cikin siririyar muryarta tace “yaya sadam na gode sosai allah ya kai lafiya “ ta fad’a tana qoqarin fitowa daga cikin motar adaidai lokacin da hancin motar ammar ta sanyo kai “Ameen ki kula da kanki “I will !ta fad’a tana sakar masa murmushi duk da bawani sonshi take ji ba amman taji dadi sosai kuma zata iya rayuwa dashi muddin rai .ammar yana kallo sukayi bankwana “

da sanyi jiki ta shige cikin sadam ya cigaba da tsayuwa yana kallon bayanta har ta ,bace masa sannan ya lumshe idanunshi lokaci d’aya kuma ya bud’e “oh my goodness god “ya furta a can qasan zuciyarsa ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimci abinda yace ba .”murmushi ya kwace masa a saman fuska wa zai same kamar maryam yace bai so ?”sai dai wani dalili na dabam ya haifar da hakan ,sam ya manta a inda yake sai da yaji mutane ana masa hon a she fa motoci ya tare duk suna tsaye suna jiransa murmushi yayi sannan ya kama gabansa yayinda maryama tuni ta shige cikin ma’aikata bata ma san lokacin da yaya sadam ya wuce ba .”

tana shiga sauran abokan aikinta suka qaraso suna mata magana suna shirin shiga inda zaa wa masu neman aiki interview amman ita maryama hankalinta bai garesu yana kan neman inda subia ta shige ,tunda tasan a tun lokacin da sukai waya daita ya cancanci ace tana wajen koma anyi mata interview an gama .”taja ta tsaya tana cewa” kuje zanzo na sameku daga baya “.ta bud’e jakarta ta ciro qaramar wayarta ta shiga neman layin subai’a ,ganin an bud’ewa ammar mota ya fito yana nufota yasa ta sauke wayar daga kunnenta tare da kashewa gabad’aya “ya iso har inda take tsaye yana gama qarasowa wayar hannunta ya amsa ya rike ta kallesa tana murmushi sannan tace “barka da safiya ?

“Barka !
“me ya tsayar dake da sai yanzu kika qaraso ?ya tmbyeta yana duba screen din wayarta sunan wacce ya gani ne yasa ya mika mata wayar “wallahi wanda zan aura ne ya ‘bata min lokaci “ tayi maganar cikin salon jan hankalin duk wanda yake tare daita, ammar kasa magana yayi kafin daga baya da kyar cikin fad’a yace “wato har zaki iya fad’a min wanda zaki aura ne ya ‘bata miki lokaci ? tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta dan batayi tsamanin zai ji haushi maganarta ba ganin babu komai a tsakaninsu sai mutunci da girmamawa “amman ki sani wannan ba mutuncinki bane ko nace zaki zubda mutuncin family d’inku ne .”

“Ai shima family dinmu ne da mahaifinsa da mahaifina the same mother the same father wani irin kallo yayi mata mai cike da tunhuma,itama kallonsa tayi numfashi ya fesar yace “shi kuma mijin da nayi miki fa ya zanyi dashi ?tayi murmushi tana cewa “allah sir ka daina min haka wallahi kana d’aga min hankali ,kai kanka kasan kafi karfina bare wanda kake fad’a wannan sai dai na qara dagewa da aikin ibada wata killa na samu irinsa a aljanna yayi murmushi yace muje “.

Ahankali suke takawa yayinda mutane suke gaishesa wasu ya amsa wasu kuma ya d’aga masu hannu “kefa ko anyi miki interview ko ba’ayi miki ba dole zaki yi aiki damu “sure tunda inda kai ba ,ai sunanki na can tuntuni kinga office dinki can ta kalli inda ya nuna mata “woow gsky naji dadi sosai “kinga ga office dinki ga na mijinki in sha allahu “tayi murmushi kawai tana cewa “subai’a fa ?nifa nafi son naji kana magana kana had’awa daita zai yi magana kenan, wayarsa ta d’auki qara sauti ,ya soma qoqarin d’auka bata tsaya jiransa ba ta cigaba da tafiya dan daman da kyar take iya jirawa dashi da sauri ta qarasa tana shiga aka kira sunanta .”
Chapter 33 · 0% Book details