← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 102

Sashe 70

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ATA V.O d Ahmed duk suna inda suke zaune Ahmed ya russuna cikin fara'a yace “nagode sosai sir ! Allah ya kara arziki yasa kafi haka.ATA bai ce uffan ba  tunin musa ya soma daukar buhuhunan  ya nufi  bayan motar ahmed ,atare ahmed da ata suka mike suka biyo bayan musa ahmed ya shiga motarsa , masu gadi suka bude masa get ya fita.ATA  ya kalli kofar fitowa daga falo a tunaninsa zai iske mrym a wajen tunda tasan fita zasuyi yau ya kalli agogon hannunsa ya d'an ja tsaki. “me wannan yarinyar  ta tsaya yi ne tana bata min lokaci ? ya sake jan tsaki yasa hannu a ajihu ya ciro wayar sa ya soma kokarin kiran layinta ya saka a speaker ,wayar maryam dake ajiye a kujera ta soma ringing.ni'ima  dake cin abinci da  maryam wadda ke zaune a kujerar dake fuskantarta suka juyo suka kalli wayar ,maryam ta mike ta karasa ta dauki wayar ta duba sannan ta kalli ni'ima cikin alamun tsoro  "mijinki ne ko? maryam ta gyada mata kai alamun"eh " Kar ki dauka, kyale shi ya karaci kira har ya gaji cikin tsoro maryam tace "saboda me?”wallahi Ina mugu mugun jin tsoron fad'ansa ke bai ma ta'ba kirana ba sai yau fa yau din ma nasan dan fitar da zamuyi ne “ tana rufe  bakinta kiran ya katse cikin jin haushi tace"wai ke baki da 'yanci ne? bai ga kinyi bakuwa bane da zai dameki ? wallahi Ki rage jin tsoronsa haka ,idan ba haha ba bazaki ta'ba yin martaba a idanunsa  ba "haba ni'ima ya kike irin wannan maganar bakiji nace miki fita zamuyi ba ?  gidan mami zamu kuma Ko babu aure a tsakanina da yaya Adam, dan uwa nane fa!"To sai me...?ta fad'a adaidai lokacin da ATA  ya shigo falon fuskar shi a daure yana kallon maryam a kaskance "bakya ji ina kiran wayar ki ne .”?

Adai cigaba da bibiya

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kuɗi ne mai buƙatar karantashi  bayan na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number ɗin 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan Number 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntuɓii chaneel ɗina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 21

Shiru maryam tayi tamkar ba da ita yake magana ba, sai dai ta tsura masa idanunta yayinda acikin zuciyarta tsoro ne daskare muryarsa a tsarƙe ya cigaba da magana. “fito mu tafi karki ɓata min lokaci” jarumta ta aro ta sanyawa jikinta tana faɗin. “kayi haƙuri kafin nayi picking ne kiran ya katse kuma kaga ai nayi baƙuwa bai kamata na tafi in barta ba” ATA ya kalli Ni'ima dake zaune a wulaƙance sannan ya kalli maryam. “Ke ban son iskanci ni zaki faɗawa kinyi baƙuwa ?ina ruwana da ita?” yayi maganar a tsawace wanda yasa hantar cikinta kaɗawa nan da nan tsoro da matsanancin firgici ya bayyana a gbdy ilahirin jikinta. “darajan sweetheart kikaci  if  tace nazo mata dake kema Kinsan har abada bazan taɓa haɗa tafiyata dake ba” yana gama faɗar haka ya juya da sauri ya fita daga parlour'n . “maryam ta dubi Ni'ima cikin  tsananin damuwa tace . “Kinga abinda nake  gudu ko? gashi har yayi fushin nashi zuciyarsa iya wuya ne  kamar jira yake ya hau zubama mutun faɗa” Ni'ima ta miƙe tsaye tanabin ƙofar daya fita da kallo sannan ta  kalleta cikin fushi. “wallahi maryam wannan mijin naki bai ɗaukeki da daraja ba, hatta  komai ma dake cikin gidan mai amfani da mara amfani  ya fiki muhimmanci agurinsa” maryam tayi   shuru  kawai tana kallon Ni'ima da sauraronta “wannan auren  zumuncin da akayi muku gsky ke aka cuta”

Maryam ta karkata  kai tana cigaba da kallon Ni'ima “haka kike gani?ai kinfi kowa sani wannan maimaci ne nayi miki amman kinsan ke aka cuta” “nifa ba cuceni ba ni'ima dan ina son yaya adam tun asali in takaice miki tun kafin mahaifiyarsa tayi tunanin  haɗamu  dan gsky da ban samesa ba da haƙurina  zai gaza domin kuwa ciwon zuciya ne zai kamani”
“ke da Allah rabani da maganar wata shegiyar  soyayya uwarsa tasan duk wannan cin kashin
da yake miki?” “tasan komai kuma tana iyakacin ƙoƙarinta, bata son duk wani abinda zai ɗaga min hankali duk abinda yayi muddin zata gani ko taji labari sai inda ƙarfinta ya ƙare” “dai-dai kenan  idan ya ɗaga miki  hankali ki dinga kirata ki ɗaga mata hankali, idan kuma tsoronsa ya hanaki aikatawa   sai ki zauna da baƙin ciki” Ni'ima ta soma yafa gyalenta tana kallonta “zo mu jera sai mu rabu a titi” maryam ta gyara zaman mayafinta ta ɗauki wayarta tare da sakala hand bag suka nufi kofar fita daga parlour'n .

Mai gadi ya buɗe tafkeken get ɗin gidan motocin ATA  suka  nufo kofar a hankali zasu fita a dai-dai lokacin maryam da Ni'ima  suka fito daga parlour suka ga motocinsa. “lah Ni'ima kinga bai tafi bama ashe, bari in tsaida shi basai naja mota ba kema ki shiga mu rage miki hanya” ta  nufi motar da sauri tana ɗaga masa hannu “yaya Adam! Yaya Adam..!!”  yana  kallonta amman bai bada umarnin a tsaya ba motocin  a guje suka fice daga gidan ."maryam ta tsaya  tana kallon Ni'ima mai gadi ya rufe get din Ni'ima  ta iso gaban maryam cikin fushi tana kallonta. “haba maryam! akan me zakiyi irin wannan zaman rashin darajar kamar wata baiwa?wallahi in baki ƙwaci ƴancinki ba ciwon zuciya ne zai kasheki a banza da wofi” cike da damuwa Maryam  tace.“To ni yanzu ya zanyi? babu abinda ban masa ba tun daga Kan tsafta biyayya duk nayi kamar yadda na fad’a miki hatta taimako umma tasha aiko min akansa amman duk a banza ko kallon arziki ban ishesa ba” “na baki shawara?” da sauri maryam ta gyaɗa mata kai. “Kawo kunneki” maryam ta matso kusa daita sosai tayi mata raɗa a kunne nan take maryam ta girgiza kai “ke kan wannan mutumin fa baya jin komai gara kawai na cigaba da zama haka idan da rabon zai canza ina fatan haka .”

Tare suka jero inda motar maryam take a parking space ni’ima na cewa “ki samu lokaci ki shiga Zuru da kanki yarinyar wallahi sai yadda kikayi dashi duk wannan taurin kan sai kin nema kin rasa “akwai wata tukunya da umma tace zaa aiko min daga can , “eh nasan dashi ai zuwa wani sati zaa aiko zan sa a hado miki da wasu abubuwa ma ,”ta fad’a adaidai lokacin da suka shiga mota suka bar gidan niima na cigaba da magana “ai ina fad’a miki muddin kikayi masa amfani dashi zakiyi mamakin yadda zai rikice ai wallahi sam ya’yan zuru basu cancaci wulakanci a gidan miji ba mu dake juya maza son ranmu amman ace ke kin bigi a wulakance a gidan mini “wallahi ni’ima ni kaina abun na damuna kamar na tattara na bar gidan amman bazan iya ba darajan mami da kuma karfin soyayyarsa “masu aikin mami ne a sunkuye a gaban dinning suna jere food flask.
Mami ta fito daga kitchen Riƙe da tray me ɗauke da lemuka a hannunta ta nufo dinnig dasu.tabawa mai aikinta ta iso gabanta da sauri ta karɓa taje ta ajiye mami ta ɗauki air-frshner ta soma feshe falon sannan ta ɗan tsaya alamun sauraro, ta juyo ta kalli tabawa mai aikinta  tabawa ta juyo ta kalleta sanda take ƙara gyara zaman kujerun. “Tabawa!” “Na'am  mami” “naji tsayuwar mota ina zaton adamcy ne suka iso , hanzarta ki bawa sauran masu aiki umarni su ƙarasa gyara wajen su bar nan tun kafin ya ƙaraso”

ATA ya shigo cikin parlour'n da sallama mami ta amsa da “Amin wa'alaikas salam” ATA  ya iso gaban mami  ya rusuna yana gaisheta “sweetheart  barka da rana” cikin sakin fuska mami tace. “barka da zuwa adamcy Nah ɗan albarka ya gida ya kuma ƙarfin jikin?” “Alhamdulillah” Mami tace. “ka ganmu muna ta shirin tarbanku kamar wasu baƙi ko?” ya miƙe yana kallon ɓangaren dining  sannan ya zauna.
Yana cewa. “sweetheart da kanki kikayi komai?”  “Ƙwarai kuwa, ni da tabawa   muka shirya muku abinci sai sauran masu aiki da suka taimaka ” ATA yayi shiru kawai suna cikin magana suka jiyo sallamar zabiba ta karaɗe falon mami ta ɗago ta  kalleta tana cewa.  “Zabiba har kin ƙaraso?”  Zabiba tace. “Eh mami na ƙaraso suma suna hanya yanzu muka gama waya dasu  ina yini?”  “lafiya lau zabiba ya yaran suke?”  “suna lafiya suna gida tare da babansu khaira ce ta maƙale wai lallai sai ta biyoni taga hajiya mami nace ban zuwa daita tazo takurawa rayuwata”  “ai wannan takwarartawa sai ahankali last time da kuka zo ta dameni da aunty girl”. mami ta faɗa cike da farinciki tana murmushi .”

muryar zabiba  cike da tsoro tace. “yaya ina yini?” bai ce mata komai ba dan tunda ta shigo  ya maida fuskarsa wani ɓangare.  Mami tace. “adamcy ana gaisheka”  a taƙaice yace. “Lafiya” ahankali ta samu waje kusa dashi ta zauna “yaya Adam!” yana jinta yayi mata banza ahankali tace.  “please yaya kayi hakuri ka yafe mana wallahi bazamu sake ba” tsaki yaja yace. “ai daman haka kukeyi idan kuka ɓatawa mutun rai kuyita nacin ban haƙuri kamar bazaku sake ba amman da zaran mutun ya haƙura ƙoƙarin aikata wani kuke yi dan haka gara ku riƙe haƙurinku dan ni tuni na cireku a rayuwata” nan da nan zabiba ta shiga aikin nan wato bashi hakuri da kuka amman ko ajikinsa girgiza kafarsa ɗaya kawai yake zabiba kuwa kuka take kamar ranta zai fita ahaka sauran ƴan'uwanta suka shigo suka isketa gabaɗayasu suka sakashi a tsakiyarsu suna masa magana amma ko motsa laɓɓansa bai yi ba. “ku rabu dashi Ke kuma zabiba ki  daina asarar hawayenki kuna zaune zai huce” cewar Mami dogon numfashi ya sauke yana taɓe baki.aransa yace “ai kuwa zan baku mamaki .”
Chapter 70 · 0% Book details