← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 102

Sashe 30

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanakin dari   kenan da auren su maryam wanda yayi daidai da kwanakin sabain da tarewar maryam a gidan ata acikin lokacin babu wani abu da yayi sauki acikin zaman auren mai dadi a tsakanin maryam da ata duk abinda maryam zatayi domin ta cire kiyayyarta a zuciyar ata tayi amman ko a jikinsa domin dai yaki sakewa daita ."shiyasa damuwarta ta qaru zamansu babu wani shaawa  dan ata yaki rungumar marym sai ma kyma da nuna ko in kula ."

Sosai motocin  jami'an tsaro guda hud'u dake gaba da bayan motar da ata  ke zaune aciki ke falfala gudu akan titi kamar suna gasar tsare baka jin komai sai jiniya mai tsanani domin a kauce abasu hanya sosai motocin dake Kan titi suka dinga komawa gefe suna basu hanya wanda adaidai wannan lokacin maryam na can tsaye   acikin kitchen tana kwashe abinci tana zubawa a kuloli ."

Bayan ta gama ta jerasu akan table duk abinda take cikin hanzari take yi kar oga ata ya shigo bata gama ba  duk da ba abincinta yake ci ba sai maakatan gidan ke ciki kuma idan tayi lattin ganawa yaci ubanta ,qarar jiniya taji alamar dawowarsa dan zaro ido tayi tare da daga kai ta kalli agogon dake manne a parlour'n karfe takwas da minti ashirin cikin sauri ta haye sama ta shiga dakinta  wanda ya sha gyara gwanin burgewa.  ta cire kayan jikinta ta daura towel sannan ta nufi bayi ."

Cikin  jin isa  ya turo kofar parlour'n tare da shigowa babu kowa a parlour'n jakar dake hannunsa ya ajiye akan kujera da wayoyinsa sannan ya nufi sama yayinda zuwa wannan lokacin maryam ta fito tana tsaye a gaban madubi tana shafa lip's dinta byn ta gama ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka can zuciyarta ta bata umarnin ta saka marasa nauyi tun sanda ta tare a gidan tsawon sati tara kenan atamfa da dogayen riguna take sakawa ta sanya kaya marasa nauyi masu yanayi dana bacci yana tsaye a dakin yaji an turo kofa bai juyo ba ."

cike da faraa ta tsaya a gabansa tana cewa "oyoyo baby sannu da zuwa "wani kallo yayi mata a dage yana sake tamke fuska tmkr yaga wani mugun abu cike da sanyin jiki ta kallesa ganin yadda yayi mata kallon kaskanci "leave my side “ya fad'a yana nuna mata kofar fita yayi maganr cikin bacin rai bata wani damu ba tunda idan da sabo ta saba da halinsa "ga abinci "bana ci kina tunanin zanci abinncikin ne ko me ?”kayi hakuri please kaci ko kadan ne na sha wahala sosai kafin na gama bai ce mata komai ba ya juya ya bar parlour'n.”

Wani bakinciki ta dinga ji acikin ranta "oh ni maryam me zan yiwa wannan bawa naka na canzashi?gani bata da abinda zatayi yasa taja kafafunta ta koma dakinta ."ta fad'a kan katifa wasu hawayen bakinciki na zuraro mata nasihar sister ce ta fado mata "maryam kinsan yadda akayi auren nan hakuri zakiyi da Adam idan kina son kici riba ,auren da kayi dan soyayya ma hakuri kake yi bare wanda iyaye suka had'a zaman aure dan hakuri ,gidan aure makaranta ce mai girma ba zaka gane hakan ba sai ka shiga, akwai darussa kala dabam dabam sai kin zauna acikinsa zaki fahimta."wasu hawaye suka qara tsiyayo mata yanzu haka zata qare rayuwarta cikin hakuri "tunda kina son shi dole zakiyi hakuri dashi ."zuciyarta ta bata amsa da hakan .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 10

Ahankali ta yunkura ta mike tsaye kamar wata mahaukaciya ta soma zariya acikin d'akin  tana sambatu "yanzu me  zan masa na  kawowa kaina  kwanciya hankalin acikin gidan nan ?tayiwa kanta tambayar tana mai qara shiga tashin hankali "babu abinda zaki iyawa wannan mai shegen taurin kan da zaki burgesa ,komai zaki  masa a banza ne a wajensa "tayi shiru na minti biyar tana tunani kafin ahankali ta qarasa inda wayarta take ajiye, ta kai hannu ta d'auka tana  tunanin kiran d'aya daga cikin yan'uwansa wani tunani tayi sai kuma  ta fasa kiran  domin dai tasan kowa a cikinsu abu d'aya yake fad'a mata shine hakuri hakuri !! kuma yanzu da zata kirasu  hakurin dai zasu bata ."

     "bana son wannan hakurin  gashi kuma hakurin dole zanyi  tausayin kanta ya kamata tana mai jin kamar duk ita ta jefa rayuwarta cikin matsala a dalilin zunzuruntun qaunar da take masa da taki auren tun farko data zauna da rayuwarta lafiya ."yanzu me zanyi ?ta sake tambayar kanta tana cure hannuwanta waje d'aya "idan da hali ki sake zuwa wajensa ki kwantar da kai tunda kece a kasansa "da sauri ta girgiza kai alamun shawarar bata yi mata ba  "wallahi da zan  cire kulafucinsa nayi hakuri na  bar rayuwarshi da komai zai zo min  da sauki "ta sake bawa kanta wannan shawara  "amman ina bazata iya ba dan tana da kulafucinsa tana mutuwar son shi kamar yadda yake mugun kinta murmushin takaici  maryam tayi tana cewa "Allah kasani ina wa  adam wani irin so mai girma, allah ka nuna min ranar da zai soni kamar yadda nake sonshi dan zan só faruwar haka."

"burina a koda yaushe mu kasance a matsayin miji da mata kamar sauran ma'aurata dan haka maryam karki gaji da halin mijinki kije ga mijinki baki san abinda allah zai yi ba  wata rana sai labari ga kuma alqawarin da kika d'aukarwa mahaifiyarsa kuma mami ta yarda dake shiyasa ma ta baki amanarsa
da wannan shawar ta fito daga cikin d'akin cike da sanyi jiki ."bayansa ta hango yana taka step ahankali yayinda hannuwansa duka ke cikin aljihun wandonsa kunnensa manne iPod ."kai tsaye bayansa tabi yo tana kallon yadda yake taka step yana wani rangaji." alamun taku yaji abayansa ya  waiwaya ya kalleta sannan ya juya ya  cigaba da taku ,yana gama sauka  ya samu waje ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun parlour'n ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya yana cigaba da wayarsa "karka qara min damuwa ammar akan wanda nake ciki, ina ruwa da wata yarinya ta gama bautar qasanta mana ina ruwana ."

"idan zanyi aure dole sai ita zan aura ?" kaga dan allah malam mu bar maganar nan ta isheni haka
yes of course ni na furta zan qara aure amman ba lallai sai wannan yarinyar ba .""Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryam ta furta a kasan zuciyarta qirjinta na dukan uku uku  sakamakon jin maganarsa ,ta tsaya nesa kad'an dashi tana kallon yadda yake motsa bakinsa  tare da sauraron maganarsa .shiru ATA yayi can yace "ammar ba lallai tayi min ba ka dai san halina  ba duk abinda yayiwa mutane yake min ba ina da test "maryam ta runtse idanunta qirjinta ya cigaba da beating very fast amman kuma ta d'an ji sausauci jin abinda ya fad'a dan haka ta taka ta shige kitchen tana mamakin yaya ammar ."

"In da wani ne ya fad'a mata zai kasance cikin masu bawa mijinta  goyon bayan ya qara aure zata musa sai gashi taji da kunnenta sosai taji ciwon abun aranta   ta had'o masa shayi irin wanda tasan yana so ta qaraso inda yake zaune jikinta a sanyaye ta mika "ga shayi !".ya d'ago tsumammun idanunshi ya zuba mata batare daya kar'ba ba ya cigaba da wayarsa "kasan Allah da nayi niyyar naga yarinyar nan ko sau d'aya ne  amman jin yadda kake wani  zuzutata naji bazan iya ganinta ba ." wani naunayen ajiyar zuciya maryam ta sauke najin dadin abinda ya fad'a dadinta dashi akwai ra'ayi kuma ra'ayinsa nayi mata dan ba duk abinda mutane ke so yake masa ba "ga shayi ka sha " ta sake furtawa a raunane kwayar idanunsa ya sake d'agowa ya zuba mata wanda yasa ta sake shiga tashin hankali  "nasan kana da d'abiar shan shayi a duk lokacin da ka dawo daga aiki ".

wani dogon tsaki yaja yana  d'auke kwayar idanunshi akanta "abinda ya kamata tayi tun a farko shine dan shirme irin nata ya dawo karshe" ya sake jan tsaki ."
Daga can bangaren ammar  kuwa cewa yayi  "haba ATA kaji da madam mana ,dan allah kayi qoqarin kabi mahaifiyarka shine kawai zai samar maka kwanciyar hankali da natsuwa "na sani ammar ina iyakacin qoqarina the girl  always doing nonsense wai abinda ya kamata ayi da farko dan hauka irin nata shine ya dawo karshe "haka zaka d'aure kayi hakuri kuma da zaka d'aure ka .."enough ammar ! ya fad'a tare da amsar qaramin cup din hanunta ya  ajiye akan table  ya mike ya  nufi kofar fita ya barta a wajen tsaye  bayanshi tabi da kallo tana furta "oh ni maryam naga takaina."

Haka taja kafafunta ta koma d'aki duk yadda taso kin kiran kowa acikin yan'wansa amman zuciyarta ta gaza hakurin haka sai data kira nana hauwa'u "tana dauka ta fashe mata da kuka tana cewa "sister me  na tsarewa yaya ammar da yake son yaya Adam ya qara aure?" "aure kuma ?wallahi da kunnena naji suna hirar inda allah ya taimakeni yayanki yana da raayi yaki yarda da maganarsa "to ki godewa allah da bai yi raayin qarawa ba dan koni bazan so akawo miki wata matar gidanki a halin da'ake ciki  ba ciwo zaa qara miki  akan ciwo "."Sister wai taya zaayi na shawo Kan yayanki ne ?ina ji ajikina hakurina ya kusan qarewa acikin gidan nan "na sani sister kina hakuri sosai da yaya Adam amman ki qara akan wanda kike yi sannan karki gaji dashi ki cigaba da bashi duk wata kulawa da mata ke bawa mijinta  idan babu mutuwa akwai rabuwa  wata rana zai ga amfaniniki sai abu na gaba " ki dage da addua abinda na fahimci kina sakaci dashi kenan sister wallahi idan kika rike allah zai isar miki ,dogaro da allah shi ke yaye wa mutun damuwa sosai nana hauwa'u ta ajiye damuwarta ta dinga kwantar mata da hankali ."

******
Chapter 30 · 0% Book details