← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 102

Sashe 64

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“duk iskancinsa yana matuqar shiga tashin hankali idan ya tuna zata mutu ta barshi kuma duk baccin da yake da zarra ya tuna zata mutu sai baccin ya dauke masa bazai manta ba lokacin yana da shekara ashirin da takwas duniya cikin baccinsa wai aka fad’a masa sweetheart dinsa ta rasu da mugun sauri ya farka ya shiga dakinta tana kwance abunta tana bacci ya Kai hannunsa daidai hancinta nan yaji tana numfashi wani naunayen ajiyar zuciya ya sauke gudu motar yake amman sam ATA gani yake kamar motar ba gudu take ba dan gabdaya ya rasa natsuwarsa daga jajayen idanunshi yayi ya sauke akan wayarsa daya har da wasu mintuna tsaki yayi yana jin zuciyarsa kamar zata buga sam baya ganin gudun motocin nasu yaji kamar ya karbi tukin watakila nashi zai fi nasu, tsaki yaketa yi yana qarawa kamar bazasu kai ba haka yake gani duk jikinsa tsuma yake kwakwa luwarsa ta hargitse kamar wanda sabon hauka ya kama a haka suka qaraso bakin get din gidan Aunty shahida tun baa gama daidaita tsayuwar mota ba ya fito da sauri ya shiga buga get din gidan da iyakacin karfinsa domin kana ganinsa zaka fahimci hankalinsa a matukar tashe yake tunda yayi bugun farko kowa dake cikin gidan ya farka a matukar tsorace ,mai gadi ma yayi takansa sai dayaji ya ambaci sunan aunty shahida sannan ya fito ya bude qaramin hujin get din nan take ya ganensa duk da cikin duhu ne .”

ya bude masa get da sauri ya shiga haraban gidan yana kwalla mata kira” shahida shahida !!”wani irin bacci ne haka?” meye amfanin wayoyinsku da karfi ya dinga buga kofar shiga falo masu aiki suka bude masa yaranta da masu aiki ya gani tsaye cirko cirko ya shiga yana cewa “ina shahida taje ?””mumy na sama inji cewar hamdiya second born din aunty shahida ,zuciyarsa duk a jagule ya diga kiran sunanta sai gata ta sauko da sauri “lafiya Adam ?lafiya zaki gani by this time ?” shima ya wulla mata tmby yana mata wani kallo “dan allah meye amfani wayarki data mijinki ?”zatai magana yace yanzu dai dauko kayan aikinki ran sweetheart a hannun Allah zan iya rasata akowani lokaci “ka kwantar da hankalinka zuwa da safe zan zo “ what “?ya fad’a yana mata wani irin mugun kallo sannna yace “dan allah idan wasa mike ki dawo hankalinki ki dauko kayan aiki muje ya riko hannunta .”

“bari na dauko kayan aikina “okay Kiyi sauri please cikin kankani lokaci ta daura hijab akan kayan baccinta ta sauko tare da mijinta yana rike da kayan aikinta yana ma ATA magana “a she mami ce babu lafiya “tsaki ATA yaja Tare kwace qaramin alkwartin kayan aikin aunty shahida dake hannunsa ya ja hannunta suka fice yana cewa “idan kukayi aure shikenan damuwar iyayenku ma bakwa damuwa daita sai ta mazajenku “karka sake ka fad’a min magana “an fad’a miki idan ma akwai abinda yafi haka zan fad’a miki ,nazo miki da matsala sai wani jan jiki kike yi kamar ba mahaifiyarki nace ranta a hannun allah yake ba har da wani jerawa da miji nonsense kawai “kai ne nonsense ai gara ne tun daga farko rayuwata har zuwa yanzu akan mata biyayya nake kai fa a matsayinka na nmj wanda hakinsa ne yayi biyayya ko dole ne ,kuma hatta aljannarka tana qarqashin tafin kafarta amman ka fad’a min meye kake wa mami na farantawa bare yanzu ka d’aga hankalinka akan rashin lafiyarta ?wallahi ko yanzu mami ta rasu alhamdulillah mun gama daita lafiya kai fa ?

“Wallahi sai kafi kowa shiga damuwa da tashin hankali “gori zaki min?” ya tambayeta cikin tsananin damuwa “eh anyi maka idan kayi zuciya ka canza rayuwa kayiwa mahaifiyarka biyayya ,kaso duk wani abinda take so “tana gama fad’ar hk ta shige bayan mota, shima kuma ya shiga gaban mota ya zauna maganarta na ci masa rai “abun har ya kai ayi masa gori ?uwarsu daya ubansu daya ma tayi masa gori inaga mutanen waje ?”allah ne kadai yasan abinda jama’a suke fad’a akansa” ya salam ya furta yana dafe goshinsa ahaka suka kawo gidan da sauri ya fito yana bud’e mata mota kallo d’aya zaka masa ka fahimci yana cikin damuwa da tashin hankali hannunta ya riko cikin nashi suka nufi kofar shiga parlour’n gidan .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 20

Tunda ATA  ya  bar gidan  hankalin mami a matuqar tashe yake ganin maryam rasa  babu wata alamun an kusanceta domin ta lura kamar  babu wani abu daya sauya atattare daita "kar dai qarya adamcy ya girba mata bai aikata abinda tayi masa umarni ba?" hakan yasa taji wani sabon tashin hankali ya shigeta . bangaren ATA kuwa tafiya yake  hannunsa rike dana aunty shahida har suka shigo parlour'n gidan, sauri sauri yake janta suna taka step, kallonsa kawai aunty shahida take zuciyarta cike da matsanancin  bakinciki da tausayinsa ,bakincikinta saboda yadda yake janta, tausayinsa kuma saboda yanayin da yake ciki dan yanayinsa kawai zai tabbatar maka da baya ciki natsuwa da kwanciyar hankalinsa .  kai tsaye d'akin maryam suka  nufa inda suka iske maryam zaune rike da hannun mami tana zubar da hawaye nan da nan hankalin ATA yayi matuqar tashi , jikinsa har rawa yake ganin yadda maryam take hawaye ,ba iya jikinsa ba hatta zuciyarsa rawa take .jin motsin shigowa d'akin ne yasa da sauri maryam ta d'ago tana duban kofa idanunta ya sauka akansu ta share hawayenta da sauri ckin muryar kuka tace  "aunty shahida ina kika ajiye wayarki ?"
“mami tana cikin wani hali  har ta fita haiyacinta numfashinta baya sauka da kyau please aunty shahida ki taimaka banason  wani abu ya samu mami ."ta qarasa maganar tana wani irin kuka ."

Jin ba mutuwa mami tayi ba yasa ATA yayi mata wani mugun  kallo tare da yi  mata alama da ido ta fita ta basu wuri ."babu musu maryam ta mike ta sauko daga kan gadon cikin mutuwar jiki ta  biyo ta ra'ba ta gefensa ta fita tana  kuka .bayan fitar maryam jingina bayanta tayi da bango corriedor  tare da sake  fashewa da wani kuka mai ta'ba zuciyata "mami bana son na  rasaki  ,domin kuwa ke  din babbar jigo ce ga rayuwata da kuma rayuwar aurenta  allah ya baki lafiya allah ya tashi kafad'arki".cikin taku mai tattare da damuwa da tashin hankali ATA ya matso inda mami take kwance numfashin ta na fita ahankali ,kafin ya bawa aunty shahida umarni ya tsurawa mami idanunshi tare da zama a gefenta yana qare mata kallo yana jin kamar ya fashe da kuka ya d'auki zazzafar qaddara rasa mahaifinsa na tsawon shekaru yanzu kuma idan ya rasa mahaifiyarsa a halin da yake ciki na tarin damuwa da matsalolin rayuwa ya zai yi ?"yaja zazzafan numfashi tare da sa tafin hannunsa ya share hawayen daya d'an cika gefen idanunshi . duk yadda mami  take jin idanunshi akanta batayi kuskuren bud'e idanunta ba tana jira daga garesu  ,lallausar tafin hannunsa ya kai saitin wuyan mami yana jin saukar numfashinta yana jin d'umin jikinta  ahankali mami ta bud'e idanunta tana cewa "adamcy nah har ka dawo ?ina shahidar take  ".

kai ya gyad'a mata tare da kallon inda aunty shahida ke tsaye yace "ya kika tsaya dan allah ki fara aikinki mana  "ya fad'a kamar zai fashe mata da kuka  alokacin ya d'auke hannunsa akan  wuyan mami ganin bata da alamun qarasowa yace "wai meye haka dan allah naje na taho dake da kyar yanzu kuma kinzo kin ja kin  tsaya kin zuba mana ido kodan kinsan idan wani abu ya sameta ni ne zan fi kowa shiga damuwa yasa kike min haka ?.yayi mata tamabyar a rud'e yana zufa "wai ..."mami tayi saurin katse shi ta hanyar cewa "adamcy nah zan sha tea "da sauri ya mike tsaye  ya fita  cikin tashin hankali yana fita maryam tayi wuf ta fad'o d'akin ,sai dai abun mamaki mami ta gani ta  dawo haiyacinta ba kamar sanda ta barota ba tana kallon  aunty shahida, bata gama mamakin ta ba taji fitowar muryar mami  rasa. "zo nan maryam" ta yafitota da hannunta ta nuna mata kusa daita tana cewa  "shahida sai kuma kika ga wannan rigimemen yarona yazo d'aukarki ?.

“wallahi kuwa mami ,da yake nasan shirinki shiyasa nayi masa wulakanci, yana fad'a ina fad'a har muka baro gidan   mami tayi murmushi kawai"amman fa ya bani tausayi sosai  ,da fatan dai komai ya tafi yadda muka shirya ? tô ya dai ce min ya aikata amman bansani ba ko karya yayi min duk da nasan karya ba d'abiarsa bace idan bai yi ba ,zai ce bai yi ba " mutuwar zaune maryam tayi agurin   tana dubansu a matuqar gigice saboda tsananin tsoro "kenan ciwon mamai shiri né dan yaya adam ya kusanceta ? “Ita kuwa wani irin só mami take mata haka ?kwakwaluwarta bata kai ga bata amsar tambayoyin ba taji sautin muryar aunty shahida tana cewa "ke maryam !"maryam tayi saurin d'agowa ta kalli aunty shahida a gigice "wani abu ya shiga tsakaninki  da adam né ?maryam tayi shiru alamun kunya "kinga karki 'bata mana lokaci idan kinsan babu abinda ya shiga tsakaninku a canza wani shiri ?"ahankalai ta gyd'a mata kai kawai "ki bud'e baki mana ki min magana ita kam  bazata iya amsa wanan tambayar agaban mami ba fahimtar haka yasa aunty shahida tace "zan yi magna idan wani abu ya shiga tsakninku ki gyada min kai idan bai shiga ba kuma ki girgiza min kai.”
Chapter 64 · 0% Book details