← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 102

Sashe 28

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan fitarsu maryama  yusif ya tattara hankalinsa kacokan akan shukura ita kuma sai faman zuba masa surutu take ,acikin zuciyarsa baya jin dadin hirarta amman kuma zahiri abun ba haka bane murmushi kawai yake sakar mata yana biye mata ."karfe biyu daidai suka  fito tare da shukura sai ga baba gali ya shigo ."yana ganin yusif tare da shukura ya washe hakora yana cewa "a'a  yusif ashe dai kazo?yusif ya gaishesa , baba gali ya amsa yana tmbyrsa "ina ita maryama take dana ganka da shukura ?yusif ya d'an tsotsa keyarsa  yace "yanzu ta wuce tana kuka  wai dan nace shukurace zabina ita zan aura "shukura kuma yusif ?yayi mgnr Kmr bai san komai ba "kwarai kuwa baba ita zan aura dan haka da zarar na koma gida zan sheidawa dady da mumy agaugauta azo a nemar min aurenta ta zama mallakina ".

"Ikon Allah haka kuma abun ya kasance   ?kai kuwa yusif me yasa zakayi haka?" idan wani abu tayi maka sai ka sanar ayi mata magana  bawai ka canzata da shukura ba ya fad'a haka a fili amman a bad'ani murna yayi yace abu yayi kyau aikin salama yayi tasiri  daman yasan zata iya fiyye da hakan muddin akan biyan buqatarta ne "babu laifin da ta min kawai dai bana sonta ne yanzu shukura zan aura  "to to shikenan allah yayi maka albarka Allah yasa ayi damu ."

Yasuf ya amsa da "ameen !ya tura hannunsa cikin aljihu ya  ciro bandir din yan dubu  ya mika wa baba gali "ga wannan baba "kai yusif har da wata hidima ai  da ka barshi  ni murnar auren shukura ma da zakayi ya wadatar dani sukai sallama da baba gali ya wucesu yana murna yasuf ya kira kausar tana dauka yace "Ke kina ina ne ?ina tare da maryama ne " ta bashi amsa da haka "to ni zan wuce idan kin shirya ki fito mu wuce idan kuma na wuce ne na barki to ?ok minti biyu kawai na baki tare da maryama suka fito tana kwantar mata da hankali "

kausar kenan karki wani damu dani fa idan da sabo maryama ta rigada ta saba kawai Kiyi wa dan'uwanki addua in sha allahu nima zan tayaku yi masa addua ki gaishe min da mum kice ina matukar qaunarta "tana gama fad'ar haka ta juya ta soma taku a natse  kausar ta bita da kallo hawaye na zubo mata ."tunda maryama ta juya hawaye ke turereniyar zubo mata qirjinta  banda bugawa babu abinda yake ta kasa shiga bangarensu ta wuce  bayan d'akinsu tana kuka tun daga kasan zuciyarta " ko kallon shukura kausar batayi ba ta fice daga gidan   cike da tausayin maryama suka wuce ."

alhamdulillah aunty salma ta furta cike da yalwataccen farinciki wannan magana itace mafi dadi acikin zuciyata "wallahi mama kin gama min komai arayuwata kinga yadda ya rikice yace ma nan kusa zaa daura auren "haba wa ai ni din bata wasa bace ai muddin baku auru ba to wallahi babu mai zuwa ya kwashe wannan banzar yarinyar.""baba gali yace "ai baki ta'ba faranta min rai ba kamar yau na dauka fa abun bazai yuwu ba ashe shi yafi komai sauki a wajenki dan allah kisa ayi aikin da zaayi auren kamar yadda ya fad'a "kai dai ka zuba ido kawai kayi kallo wannan auren kamar anyi an gama ."

"Kinga bari na kira fati na sheida mata ta soma shirinta "ya fad'a yana lalubo wayarsa "wani shiri kuma gareta ?aunty salma ta tambayesa "ai muktar dinta ke mutuwar son maryama tun kwanaki  dana je gidanta take sheida min nace ta d'an jinkirta muga me zai faru kinga yanzu dama ta samu",lallai kam dama ta samu  daman shine daidai da aurenta" aunty salma ta fad'a tana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya zaa qare auren dan giya " kai salama baki da dad'i wallahi bakaji dadin da naji ba ai nan duniya bana qaunar maryama yarinyar kamar aljana ga kyau ga shiga rai suje su karata da muktar, shi din ma bazata auresa ba sai ya'yana sun bar gidan nan ."

Cike da murna da farinciki baba gali ya kira aunty fati ya sheida mata komai ai kuwa tayi murna dan muktar din ma ya dameta kullum bashi da magana sai na maryama hatta shaye shayen da yake yace zai daina muddin zaa bashi aurenta" da kyar maryama taja kafafunta ta  shigo parlour'nsu tana  mai danne damuwarta sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci tana d'an cikin damuwa aunty ta dubeta tace "Kuna fita aunty fati ta kira waya wai kizo gobe da safe tana son ganinki "to !kawai maryama ta fad'a ta shige d'akinta dan bata son tayi doguwar hirar da har  zai sã mahaifiyarta ta fahimci wani abu duk da tasan dan dole tasani amman ba da wuri haka ba "safa da marwa ta shiga yi acikin d'akin tare da cure hannuwanta waje d'aya" tsawon shekaru aunty salma na bibiyar rayuwarta ."

"laifin me tayi mata ? me ta tare mata? idan wani laifi tayi mata ta fad'a mata ta nemi yafiyarta ta barta ta huta  "? wasu hawaye masu ciwo suka gangaro mata a yanzu ba kanta kad'ai take tausayawa ba har da  mahaifiyar yusif da yaruwarsa dan ita tsakaninsu dasu aunty salma da baba gali da ya'yanta allah ya isa ne bazata ta'ba yafe masu ba ,domin cirewa kanta damuwa Kan kujerar zanenta ta nufa ta zauna ta zaro farar takarda ta ajiye agabanta ta d'auki pencil ta tura cikin bakinta ta fara tunanin me  zata zana ?".

Babu abinda yazo cikin kwakwaluwarta sai fuskar kausar murmushi mai hade da damuwa ya bayyana akan fuskarta "kausar zan zana domin dai nasan shikenan ni da ita kuma sai wani ikon allah ."ahankali ta soma bada shape din fuskarta tunda ta zauna bata tashi ba sallah laasar né kawa  ya tashita koda ta idar ma Kan aikinta  ta koma ta cigaba ranar a d'akin maryama ta qarasa niyyinta da misalin karfe bakwai   aunty ta shigo d'akin ta isketa tana gabatar da sallar magrib ."

Ta qarasa gaban table din kayan zanenta nan idanunta yaci karo da hoton kausar har da kalar kayan  data zo dashi  yau din nan aunty ta saki murmushin jin dadi  tare da cewa "lallai princess an fad'a soyayya ko da yake yarinyar tana qaunarki ta qarasa mgnr adaidai lokacin da maryama ta sallame ta  mike jiki a sanyaye take kallon aunty dan wallahi sai take jin kamar bata kyauta mata ba tunda ta tabbatar kota fada mata kuka kawai zatayi tayi hakuri sannan ta kwantar mata da hankali "

"kinyi shiru kina kallo meke damunki ?girgiza mata kai tayi alamun babu komai "amman tun bayan tafiyarsu  kausar na lura kike cikin damuwa idan wani abu ne ki sheida min mana ?ajiyar zuciya ta sauke da karfi tace "babu komai "to muje kici abinci ta kamo hannunta suka fito tana cewa "gsky zanen kausar yayi kyau idan tagani zataji dadi sosai tare da aunty suka ci abinci bata wani ci abincin kirki ba tace ta koshi ta sha ruwa ta mike ta shiga bayi ta dauro alwala ta koma d'akinta  sallar ishai ta gabatar byn ta idar ta mike tana nade daddumar sallah ."

Ta ajiye a inda yake ta tsaya shiru  acikin d'akinta tana jin wani irin faduwar gaba ta qarasa ta kakkabe wajen kwanciyarta sannan ta kwanta rigingine ta hade hannuwanta duka a qirji tana tunanin rayuwa ganin zata damu zuciyarta ne kawai a banza ta sauke ajiyar zuciya ta soma karanta suratul mulk ahankali bayan ta gama karantawa  ta shafe jikinta da addua ta kwanta, ahankali bacci ya dauketa cikin baccinta tayi mafarkin umma tace a daura aurenta da yaya sadam har ma ya amince da auren kiran sallah asuba ne ya tasheta daga mafarkinta ta mike ahankali ta zauna ta zuro kafafunta kasa   tare da dafe goshinsa ."

Tayi shiru tana tunanin mafarkinta addua tayi Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi arayuwarta da kyar ta yunkura ta mike tsaye ta fito ta shiga bayi  ta dauro alwala ta dawo daki tayi sallar asuba duk ta rasa meke mata dadi duk da tasan mafarki ne amman sai taji abun ya tsaya mata arai cike da raunin zuciyata  ta koma ta kwanta ahankali bacci ya kwasheta aunty ce ta shigo ta tasheta tana cewa "bazaki gidan aunty fati bane kinfa san halinta  babu hakuri sai ta d'auki abun wani iri azo ana damun rayuwarki “ numfashi ta sauke kawai tare da mikewa zaune tana dafe goshinta "ko baki jin dadi ne  dan tunda kika koma kika kwanta bacci bayan sallahr asuba to baki da lafiya tayi mika tace "kaina ke d'an min ciwo sai dai kuma .."sai tayi shiru ta kasa mgn "sai dai kuma me ?"

"Wallahi umma mafarki nayi wai umma tace a daura aurena da yaya sadam kuma har ya amince ?aunty tayi dariya tana cewa "kai princess wani irin aure kuma bayan ga maganar yusif ? ta kalli aunty tana jin fad’uwar gaba mai tsanani tace “aunty ki bar maganar yusif muyi maganar mafarkina gsky banji dadin mafarkin nan ba " to ai mafarki ne mafi yawon lokuta mafarki baya zama gasky tashi ki sha magani kije tun karfe tara aunty fati take kiran waya "to ni me zan mata ne ?tayi magana Kmr zatayi kuka "ni wallahi bana son zuwa koina idan kaga sun nemeka to aikin wahala ne ga wannan d’an nata mai shegen maseefar kallon tsiya kamar zai cinye mutun ".

"To ko na fad'a mata bakijin dadi bazaki samu damar zuwa ba  ta kira kaulat ko Islam suje idan wani aiki zaa mata sai suyi mata ?maryama tayi shiru can  tace  "yanzu rashin zuwan nawa  zai zama tashin hankali azo ayita kananan magana "shiyasa nake son kije idan ma aiki ne kika ga zai miki yawa Kiyi iya wanda zaki iya ki dawo ,nifa ba aikin bane damuwata kamar matsefaffen kallon da yaya muktar yakewa mutane ".
Chapter 28 · 0% Book details