← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 102

Sashe 81

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gajiyayyun idanunshi ya ware sosai akanta kafin ahankali ya hadiye wani abu daya tsaya masa a makoshi sannan yace "karki manta aikinki  kika zo ,kuma kema Kinsan ke kad'ai zasu bukaci  gani banda ni  ?" duk da haka idan a son raina ne mu shiga tare "ta fad'a tana mai tsareshi da narkakkun idanunta ." suna zaune wnn saurayin da yayi masu iso  ya  shigo yana cewa "madam ki shiga ke kad'ai mai gida yake jira "ok but dan allah ko zamu iya shiga mu biyu ?cike da jin haushin maganarta yace "tare zakuyi aikin ne ?no ni kad'ai ce !to ke kad'ai ake buqatar gani aciki dan mai gida baya son hayaniya "ya qarasa maganar tare da ta'be baki sannan ya fice ya shige wani office ."
hankalin maryama ya tashi matuka dan har ga allah haka nan taji bata son shiga ita kad'ai qarara damuw ta bayyana acikin kwayar idanunta da shi kad'ai yaya sadam yake iya gani har ya fahimci halin da take ciki ,ahankali yaya sadam ya tsiyaya mata drik ya miko  mata ta girgiza masa kai alamun bazata sha ba ,"why ?! ya tmbyeta yana sake tsareta da idanunshi dafe goshinta tayi tana cewa "bana jin shan komai a yanzu ,tun daya ga haka yasan ko me zai yi 'bata lokacinsa  kawai zai yi dan bazata kar'ba ba, dan haka ya mike tsaye suka fito tare tana gabansa yana take mata baya har suka fito dogon hanyar da zata kai su office din ATA wanda alokacin yana tsaye  acikin tangamemen office dinsa  ya hard'e  hannuwansa duka a faffad'an qirjinsa idanunsa kyam  akan maryama da yaya sadam ta cikin glass door ,har  ta fara taku domin qarasowa zuwa  inda office dinsa yake yaga ta tsaya  ta koma baya kad'an tana magana da wani da bai san ko waye ba ,sai dai idanuwanta  yana kansa ,kwakwa luwarta na hasko mata fuskarsa daga nesa kamar tasan fuskar yayinda shi din ma  kallonta yake cikin shigarta ta mutunci kamar ranar farko daya fara d'aura kwayar idanunshi akanta ."doguwar riga ce sanye ajikinta har qasa  mai dogon hannu  da qaramin hijab dinta mai zip a gaba,sai  nikaf kalar hijab din da take sanye dashi wanda iya kwayar idanunta kad'ai ake iya gani ,tsaki yaja da karfi fuskar nan tashi babu wani annurin kirki dan babu abinda ya tsana arayuwarsa kamar 'bata lokaci ,yana wasa da komai arayuwarsa amman baya ta'ba wasa da lokacinsa ,ita kuma abinda ya fahimta kenan daga gareta  tana da matukar wasa da lokacinta da kuma damarta  ".

"ya kuma kika tsaya  madam bayan  an fad'a miki ke kad'ai mai gida yake jira ?"ta jiyo sautin muryar segun  daga bayansu ta juyo a natse idanunta kyam akan  yaya sadam sannan tace  "yanzu zan shiga na d'an tsaya muna magana da mijina ne "miji kuma alokacin aiki ? yayi mata tambayar da mamaki akan fuskarsa dan shi a tunaninsa bata da aure tunda ta amsa gayyatarsu a weekend mutumin daya gansu tare kuwa ya d'auka d'an rakiya ne ko kuma saurayinta ."a natse ta gyad'a masa kai tana cewa "Eh mijina ne kuma yayana ne   ". ATA wanda yake tsaye yana ciza lip's dinsa da karfi  cikin zafin rai  bai san wainar da'ake toyawa ba amman haka nan yake jin matsanancin bugun zuciya da kuma 'bacin rai mara misaltuwa "any way kiyi sauri ki shiga kiyi abinda ya kawoki dan mai gida baya wasa da lokacinsa ,akan lokacinsa zai iya aikata komai kafin ta bashi amsa  yaya sadam yayi murmushi ya matso kusa daita sosai tare da zuba hannuwansa duka cikin aljihu wondonsa fuskarsa a sake  "karka damu yanzu zata shiga  kuma zata maku abinda kuke so "ya fad'a masa haka sannan ya maida hankalinsa kan maryama  kamar zai mata numfashi"k'anwata kuma amaryata karki wani damu da jiran da zan miki ni kad'ai abinda  nake so dake ki  natsu sosai kiyi abinda ya kawoki ina sonki ina kuma alfahari dake na kuma yarda dake a duk inda zaki kasance nasan zaki kame min kanki da kuma mutuncina "nan take idanuwanta suka cicciko  da ruwan hawaye "yaya sadam na gode sosai ,na gode da yarda daka min ya allah ka yarda dani kamar yadda mijina ya yarda dani "ameen ya hayyu ya qayyum "ya fad'a tare da ciro handkey fari daga gaban aljihun rigarsa ya goge mata hawaye  then ya kai bakinsa yayi kissing foring head dinta yana mai karfafa mata gwiwa murmushin gamsarwa ta sakar masa sannan tayi gaba tana d'aga masa hannu ."

bayanta yabi da kallo  cike da tausayawa take taka kasa kamar bata son takawa yana tsaye har sai daya ga ta tura kofar office din ahankali ta shiga kusan second biyar ya d'auka tsaye yana kallonta ya kasa d'auke idanunshi akanta ,ATA wanda yake rike da  waya a daidai bakinsa da hananu d'aya  yayinda d'ayan hannunsa  ke rike da wata farar takarda yana magana yana  kai kawo acikin office din hakazalika segun na tsaye a gefe guda cike da girmamawa bai kalli inda take ba .”
ahankali yaya sadam ya  juya ya fara taku zuwa kasa jikinsa a matukar sanyaye ya bud'e mazauninsa na direba ya shiga ya zauna yana sauke wani irin naunayen ajiyar zuciya sannan ya d'auki wayarsa ya rike yana dubawa missed call's din nadiya  ya gani rututu ya sauke numfashi sannan ya kirata tana d'auka ta fashe masa da kuka "menene kuma abun kuka ?"na fad’a miki zan cika miki alkwarin da nayi miki bazan ta’ba cin amanarki ba nan da wasu watanni masu zuwa zamu kasance tare amatsayin ma’aurata ,oh my god dan an d'aura aurena shi yake nufi me ?kinga nadiya banason abinda kike min wallahi kukanki yana mugun 'bata min rai ."

"a natse ATA  ya juyo mata fuskarsa sosai tare da tsayawa ya tokare hannunsa dake rike da farar takardar a makeken table din gabansa yana cigaba da wayarsa ."idanun maryama  suka sauka kan kyakkyawar fuskar ATA wanda zuwa lokacin ya  runtse  idanunsa gam zuciyarshi da bakinsa ne kawai ke aiki ,ta tsura masa idanuwanta sosai tana cigaba da kallonsa " tabbas ba gezo idanuwanta suke mata ba shine  shararren d'an kasuwan nan data d'auki tsawon lokaci wajen  zanashi wanda a qarshe ta kai zanensa ma'aikatansa babu wata gamsashiyar magana mai dadi daga ma'aikatansa ."tayi shiru tana dubansa a tsanake tana shakar kamshn turarensa mai sanyi da ratsa zuciya "tun daga ranar data kai masu zanensa suke nemanta a waya "to mai yasa suke bibiyarta ?"mai yasa suka jawota zuwa nan ?"
ta yiwa kwakwaluwarta tambyr da bata da mai bata amsa wani irin mummunar fad'uwar gaba take ji  babu abinda kwakwaluwarta bata hasko mata akansu  ba amman tai qoqarin sharewa  ta cigaba da tsayuwar jiransa ."bakinta na furta  hasbiyallahu la ila a illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim sakamakon wani sabon tsoro da ya shigeta ."

maryama na tsaye har kusan mintuna shabiyar  ATA bai gama wayar da yake ba haka zalika  bai bud'e kwayar idanunshi ya bata umarnin zama ba haka ma segun na tsaye bai zauna ba adaidai lokacin da qarfe d'aya na rana ta buga  wanda a daidai lokacin wasu masallatan sun tada sallarsu dan haka ranta ya soma 'baci ta soma tunanin an janyota ne kawai dan a sake wulakantata a karo na biyu ji tayi kamar ta juya ta wuce shi da segun ta kama gabanta ,ta kalli inda segun yake tsaye  shima ya kalleta haka nan ya tsinci kansa da shafa mata qirjinsa alamun tayi hakuri "segun !yes sir ya fad’a cike da girmamawa ya mika masa farar takardar dake rike a  hannunsa batare daya bud'e idanunshi ba "ina bukatar copy's dinsu "okay sir ya amsa ya fita da sauri  ."ko bayan fitar segun ata bai bud'e idanunshi ba bare yayi mata magana sai kuma taga bai kamata ace tana jiran sai shi ne zai fara mata magana ba   dole dai  sai itace zata fara masa magana kafin ya saurareta ,dan haka ta qara taku d'aya ta tsaya daidai saitin kunnensa  cikin muryar dake nuna alamun gajiya "ta gaishesa bai amsa ba sai ma ya matsa baya ransa a 'bace yayinda zuciyarsa na tafasa dan ya tsani yazo jira duk abinda zaayi masa dole shi  zaa jira karo na farko kenan daya zauna jira jiran ma akan itace zata qaru dashi .”

wulakanci da yayi mata yayi mata ciwo, dan ta tsani disgi da wulakanci kamar taja masa tsaki ta fice daga office din sai kuma tayi wani tunani su manyan nan haka halinsu yake kafin kayi nasara akansu dole sai ka kwantar da kai dan haka ta sanyawa zuciyarta hakuri tayi kasa da muryarta da kanta tana wasa da yatsun hannunta "ranka shi dade lokaci na tafiya yana da kyau abani aikin daya kawoni nayi ga kuma lokacin sallah yayi ina buqatar nayi sallah "sake jin sautin zazzakar muryarta ya sanyashi bude idanunshi ahankali tamkar mai tsoron ganin wani abun agabansa  ,ya zuba mata tsumammun idanunshi masu mugun rikitarwa  yana kallon cikin  qwayar idanunta dake d'auke da zara zaran gashi ido itama shi take kallo tana jira daga garesa ".
shiru yayi yana cigaba da kallon cikin kwayar idanunta gabansa na wani irin luguden bugu da karfin gaske,kallon da yake wa kwayar idanunta kallon né na sani "jiki a sanyaye ya  nuna mata wata kofa dake manne da office din "ki shiga kiyi alwala  "yana gama fad'ar haka ya juya mata baya .”
Chapter 81 · 0% Book details