← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 102

Sashe 19

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ata kuwa tunda ya   fita yana wajen wani abokin kasuwancinsa  daya sauka a kasar yau din nan  sun jima suna tautaunawa akan kasuwanci shi kanshi banda coffee babu abinda yasanyawa cikinsa karfe bakwai daidai a haraban family house dinsu tayi masa, yana qoqarin fitowa daga mota yaga direban mami na fitowa daga gidanta hannuwansa duka rike da wasu hadaddun kuloli “ aransa yace “shegiyar yarinya sarkin rashi hakuri har ta kira akawo mata abincin ,ai da baki kira ba yau haka zaki kwana da yunwa nonsense girl kawai .”

massalaci dake cikin esate din ya shiga yayi sallah bai fito ba har sai daaka idar da sallah ishai ya zauna yana azkar yana nadamar abinda ya fadawa mahaifiyarsa wanda yayi haka ne cikin zafin zuciya gashi yanzu yana dayasani ."ahankali ya dinga jin rashin kyautatawar da yayi mata , nan da nan kyakkyawar zuciyarsa ta dinga umartanshi da yaje ya bawa mahaifiyarsa hakuri ya nemi tafiyarta yayinda bakar zuciyarsa ke gargadinsa har ma da bashi karfin zuciyar nisanta kanshi daita .”

wayarsa dake ringing ya katse masa tunanin da yake ya ciro yana duba wayar sunan ammar ya gani ya dauka yana cewa  "yaakayi ammar ?eh mun gama magana dashi yanzu haka ina family hausa ,ok  bani minti biyar yanzu zaka ganin a gaugauce ya fito ."
Kai tsaye  rufar da yake zama da bakinsa ya nufa inda ya iske ammar yana ganinsa ya washe baki yana cewa ango !ango !! angaishe da ango kasha kamshi"
"A ina kenan na sha ? A wajen ama... "kaga dan Allah malam ka barni naji da abinda ke damuna dan ni babu wani kamshi dana sha kuma bana saka rai zan sha shi har abada ".

“kai dai anyi mai cutar kanshi kai muguntar ma har da kanka zakayi wa ?"har kuwa karshen rayuwata zan cigaba da zama haka ban sha wannan kamshin ba ya fad'a yana zama acikin daya daga cikin kujerun dake ajiye agurin ."ai ni an gama da rayuwata an cuceni wallahi amman   I think kawai zan samu wata  in aura dan bazan iya  rayuwar aure da wannan  yarinyar  ba dan sam sam attitude dinta  is something else..." ya fadawa ammar yana jan dogon tsaki .”

"hmmm amman da kayi hakuri ka d'an sake daita kad'an  kagani  ko tafiyarku zatai daidai  "no it can be possible ammar "okay  idan haka ne  na hadaka da wata sabuwar mai bautar qasa dake karkashin kamfaninmu yarinyar tana da kirki sosai , koni bancin bani da wata matsala da salima dana  shiga sawun masu nemar aurenta  dan yarinyar akwai natsuwa  da kirki ga kamun kai .”

shuru ata yayi without saying a word."Ko baka  sonta ?.."ammar  ya tambayesa, ahankali yace
" ammar I don't really know tunda banganta ba  amman bani da zabi tunda na rasa princess zan iya manage da wata "ya qarasa  mgnr yana duban fuskar ammar" to kayi hakuri da mrym din kawai madadin ka qara da wata tunda itama wacce zaka aura din ba sonta zakayi ba manage ne ai kaga gara kawai ka dinga rage zafi da mrym kawai zai fi ga tarin ladan aure gana biyayyar mahaifiya" over my dead body ni fa I can't let the woman  I hate touch my fingers balle hannuna har azo ga jikina gaskiya ammar bazan ta'ba Iyawa ba ."

“Bama zan barta ta ta’ba ni ba bare ni na kai kaina dan rage zafi tayi zamanta haka nima nayi rayuwata haka amman batun rage zafi ma duk bai taso ba “
ATA sai hakuri fa kuma wallahi irin wannan auren ma ya fi dadi gashi da alamun mrym din ma tana sonka zakayi   yadda kakeso  daita har Allah yasa ka fara sonta  “ammar  ya fada yana dariya, da sauri ATA ya daga Kai yana cewa "me yasa kace tana sona ?ai mace idan bata son mutun da wahala ta yarda a daura aure ka duba nuzla misali ce guduwa tayi har sai byn daaka daura auren hisham da nana hauwa'u ".

“wannan ba gskiya bane , nana hauwa'u ta auri hisham ne ba dan tana son shi ba hakazalika nima na auri yarinyar nan ba dan ina sonta ba "anya kuwa wata killa fa nana hauwa’u tana son shi ta boye ne kawai dan bata damar samunsa a wannan lokacin dan hk kawai ka rike marym dinka kamar yadda hisham ya hakura da nana hauwa’u ."I can't" ya fada atakaice, dariya ammar  yayi yana cewa "Ka  bani dariya,irin ku né da anyi mistake kun kusanci matan da baku so sai ciki."duk fa zaka gama cika bakin  kiyayyar  ne ka gama zaka zo ka nemi hakinka ".

“Allah ya tsareni da ganin wannan bakar ranar "kai  dai sai idan babu rabo a tsananinka  daita  amma wallahi in da rabo komin kiyayyar dake tsakaninku sai kun jone anyi ciki "  ammar  ya fada masa hk cike da zolaya ."yanzu ya batun yarinyar da nayi maka maganarta yanzu zaka aureta na hadaku dan gsky idan dai da gaske aure zaka qara gara wannan yarinyar ?” wallahi kawai sweetheart nake tunani nasan ma da wahala ta barni “bayan  ta matsa maka ka auri zabinta sai kuma ta hanakali qarawa gsky ta barka ka qara tunda kana so .”

“Kai dai bari kawai ammar abinda nasani ko banyi acikin lokacin nan ba zanyi a gaba ko nan da  shekara goma ne sai na qara  aure "Gsky abun naka na gaske ne "kai dai ka tayani addua Allah ya bani wata  mai kyau kamar irin mace da nike so “da gudu ma kuwa zaka sameta dan wannna yarinyar da nake maka mgn akanta ta had’u sosai” ata ya girgiza kai "da wahala haduwarta ta burgeni nifa ina da test "okay kenan ya kamata ka hakura ka rungume matarka amman kuma wallahi maryama ta had’u matar manya irinku ce ".

"Maryama !"?ya furta sunan a tsanake yana duban ammar yana jin sunan na ta'ba ranshi wanda bai kamata yaji hkn akan kowa ba sai akan princess dinsa ,muryarsa a kasalance yace "sunansu daya da wannnan dolen dolalon yarinyar "wacce kuma haka ? wannan yarinyar daaka aura min mana“yayi mgnr yana jan tsaki ammar yayi murmushi yace” eh sunansu daya ko bazaka aureta bane sbd sunansu daya ?kai ban son iskanci ya kake wani tursasa ni kamar dole to bazaa aureta ba muyi abinda ya kawoka nan da nan yayi qoqarin canza mgn zuwa ta business dinsu.”

Ammar kuwa sai faman dariya yake “wallahi ata kabani dariya ” wai dolen dolalo kai ata wallahi baka da kirki nifa ina jiye maka tsoron ruftawa karkazo kana rokonmu muje maka rarrashin dolen dolalo tace sam bata san da wannan ba “wani tsaki yaja yana maka masa harara .”bai sake cewa komai ba ya mike tsaye yana cewa “ina ganin baka shiryawa kasuwanci ba “ko kafin ammar yayi magana tuni ata ya soma taku “ata tsaya mana dan allah ka dawo muyi mgn tsaki yaja ya shiga bayan mota dan tuni masu tsaranshi sun bude masa gidan baya .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 7

Ahankali motocinsa suka fice daga cikin abdullahi estate ,mr ATA zaune a bayan mota yayi shiru yana sake tariyo tautaunawarsu da ammar shi dai baya jin zai auri mai kamanceceniya da harafin sunan maryam ma bare mai sunanta, sai kace babu mata a duniya masu sunan arziki sai nata , tabbas shi yasan dan dole ya qara aure kuma acikin tsakankanin wannan lolacin amman kuma ba mai irin sunan yarinyar ba .”wani dogon tsaki yaja sanda ya tuna dole zai koma ya kwana gida d’aya da yarinyar da yafi tsana .”

Qarfe goma daidai suka qaraso bakin get din gidansa wanda sai alokacin ya tuna daya sallami masu tsaron get din gidan, hakan yasa ya lalubo wayarsa ya kirasu su dawo bakin aiki kuma alokacin wanda zuwa wannan lokacin motocinsa sun kutsa zuwa cikin haraban gidan kai tsaye parking space suka nufa .”sukai parking suka firfito da sauri ata na qoqarin bud’e murfin kofar motar mutun d’aya acikinsu ya bud’e masa cike da girmamawa . “

cike da natsuwa ya fito daga cikin motar ya tsaya yana magana can kasan makoshi “gobe da wuri zan bar gida “ ya fad’a atakaice “okay sir duk suka had’a baki gurin fad’ar haka, daga haka bai sake cewa komai ba ya soma takawa .”maryam dake zaune tana cin abinci tana kallon series na turanci my husband my destiny ,title din series din ne ya d’auki hankalinta har ma yasa ta cigaba da kallo, ahankali taji ana qoqarin bud’e kofar parlour’n,zumbur ta mike tsaye tabar cin abinci da kallon da take sbd jin motsin shigowarsa .”

tsumammun idanunshi ya zuba mata masu matukar firgitarwa cikin salo na harara , gabad’aya maryam ta gigice da sauri ta d’auki remut din tv ta rage volume ,shi kuwa wani kallon tsana ya cigaba da binta dashi tun daga sama har kasa “tabbas zaton shi ya tabba manu direban mami ita zai kawowa abinci .”yadda yake kallonta yayi mugun d’aga mata hankali dan bata san abinda zai biyo baya ba , jikinta ya saki sosai yayinda qirjinta ke wani irin bugawa da karfin gaske a sanda ya qara taku biyu ya qaraso tsakiyar parlour’n ya tsaya still kwayar idanunshi yana yawo ajikinta .”

“tsoro da matsanancin firgici ne duka suka kamata alokaci d’aya zuciyarta ta cigaba da bugawa da karfin gaske,yayinda gefe gudu kuma sanyayyen kamshin turarensa ke neman buwayar hancinta ,nan da nan hankalinta ya sake tashi jikinta ya kama rawa rawa “wayyo allah nah me yasa na zauna a parlour’n ban koma d’akina naci abinci ba gashi zan jawa kaina maseefa da tashin hankali?” ta fad’a tana dungurin kanta .”da kyar ta sanyawa jikinta jarumta tace “san ..sannu da zuwa “.ya jita sarai amman yayi tamkar bai ji ba .”
Chapter 19 · 0% Book details