← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 102

Sashe 69

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaune yake a office dinshi aiki yayi masa yayinda kanshi ke duke yana fama da aiki rubuce rubuce dake gabansa yaji Knocking din kofa , kansa na duke ya bada izinin shigowa batare daya dago kansa ba yaga ko waye ba ammar ne ya shigo cikin office din da sallamarsa ATA ya amsa batare da ya dago kansa ba ya cigaba da abinda yake" ganin haka Yasa ammar ya tsaya abakin window , yana kallon haraban ma’akatan wanda ma’aikata ke kai kawo dan yasan tunda ya iske ATA kan aiki bazai taba sauraransa ba matsawar bagamawa yayi ba dan sanin da yayi masa kenan na maida hankalinsa matuka akan aiki idan yana yi .Kusan minti shabiyar yayi tsaye , sannan ya soma takowa ahankali izuwa bakin makeken tablet din da ATA ke zaune ,yaja kujera daya ya zauna yana dubansa, Sai lokacin ATA ya d’ago tsumammun idanunsa ya dubeshi har ka gaji da tsayuwar kennan ?

“Ba dole nagaji ba dan naga alamun sai nakai ga zama tukun zakiyi lokacina ya fad’a hk yana mikowa ATA hannu suka gaisa ,yaushe ka dawo qasar ? Dariya ammar yayi yana cewa “shekaranjiya na dawo yau km nace nazo naganka ,ko bai yi bane ?
Wani irin farinciki ya lullube zuciyar ATA ya danyi murmushi har dimple dinsa ya lotsa tsantsar kyawunsa ya sake bayyana ,yana son a dinga nuna masa kulawa da soyayya ,ammar yace aboki lfy kuwa irin wannan farinciki haka ?”babu komai nima haka na tsinci kaina ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune yana jujjuyawa dashi , ammar yace “ya mami da dolen dolalo ?sai da ATA ya yamutsa fuska sannan yace “sweetheart tana lfy ita dayar ce dai gsky bansani ba ammar ya sake yin dariya kace zaka qara aure har yanzu shiru ko ka canza shawara né zaka cigaba da zama da dolen dolalo?

“Ammar kafa dawo kenan “ya fad’a yana jan tsaki “dan kaki bin shawarata ne wallahi da kaga maryama zata maka yarinyar abar tausayi ce ga maraici ga rashi “bana jin zan iya auran irinta koda zan yi aure ,kai ina ganin na hakura ma .ok zaka cigaba da zama da mrym din kenan ? ya gyada masa kai kawai ,amman to why not ko sau daya kaga maryama ni ina dalilina son ku had’u da juna “dan Allah ka rabani da wannan shirmen ai tunda sunansu ma yazo d’aya da yarinyar nan naji na tsani had’uwa daita ammar ya bud’e baki zai sake yin mgnr d’aya daga cikin wayoyinsa ya dauki kara 'ahankali Yasa hannunsa ya janyo wayar maganar second biyu yayi ya sauke wayar ammar na zaune yana kallonsa har yagama wayarsa , yana shawarar yadda zai bullo masa yafi son ya ganta yana son yaga rud’ewar da zai yi akanta ,hira suka cigaba dayi kafin daga bisani ammar yayi masa sallama ya wuce .”

Satin mami biyu ta soma tattara kayanta babu yadda maryam batayi ba akan tayi zamanta tace aa “dan allah mami ki zauna banason ki tafi “aa maryam shiyasa nace akawo miki masu aiki bakin kishinki ya hana tayi murmushi “kai mami wani kishi kuma ?aikin gidan bashi da wani yawa fa koma dai menen Ya rage naki ni dai tafiya zanyi gobe .
da daddare da ATA ya dawo ta sheida masa “ in sha allahu gobe zata koma gida “sweetheart kiyi zamanki mana “a’a bazan cigaba da zama ina ganin wulakacin ba dan banga abinda zamana yake tsinana maka a gidan ba hassalima qaro sabon wulakanci kayi lada ya isa haka idan ka ga dama ka duba allah kayi wa matarka adalci idan kuma kaki zakaje ka had’u da allah né sai abu na gaba idan zaka zo qarshen wata kazo min da maryam washgari ta kasance asabar da misalin karfe hud’u na yamma suka rako mami haraban gidan inda ATA ya bud’e mta bayan mota ta shiga ta zauna maryam ta zagaya dayan bangaren ta ajiye mta jakar kayanta mami ta dubi ATA “ka tabbatar kazo qarshen wata sannna kazo da maryam "in sha allahu ya fad’a tare da rufe mata murfin mota yana cewa direbanta ya jata Ahankali mami tayi warning din glass din mota tace “bani wayarka !babu mutsu ya mika mta number mrym tasa masa tayi saving number da sunanta “ga number mrym nan na saka maka ka dinga qoqarin sauke nauyin dake kanka .”

Itama maryam tace mata “nasan kina da numbersa ki dinga kiran mijinki koda kuwa bazai d’auka ba duk runtse ki sauke nauyin dake kanki allah ya had’a hankulanu tace “Ameen tana daga mata hannu suna tsaye har mota data shiga da masu tsoron motar suka bar gida sannan suka shiga ."bayan tafiyar mami da kamar awa d’aya ya sauko sanye da wasu kaya ya ajiye wayoyinsa akan center table  ya samu waje ya zauna ya dauki remut ya kunna tv ya qara karfin ac ya daura kafafunsa  akan center table yana duban tashar labarai ahankali maryam ta fito daga dakinta cikin sand’a take saukowa sakamakon yunwar da take ji dan tun abincin safe ne acikinta ko kallonta bai yi ba ta shiga kitchen ita kuwa tayi haka né dan tasan yanzu sai wani ikon allah tunda mai shiga tsakaninsu bata nan bata ki bin umarnin mami ba kullum tana iyakar qoqarinta na kiransa kmr yadda mami tace wani lokacin ya dauka ya danqara mata bakar magana wani lokacin kum bazai dauka ba ahaka har suka zo qarshen wata .”

******

Alhamdulillah DG m malik ya fara samun lafiya sai dai baya iya magana sosai idan baka matso da kunnenka kusa da bakinsa ba bazakaji abinda yake fad’a ba ,haka zalika sansar jikinsa ba koina yake iya sarrafawa ba yana  kwance yayi wa matarsa  alamar ta d’auko wayarsa ,byn ta dauko ta tsaya kusa dashi kamar yadda ta saba, ganin magana zai yi ta rankwafo daidai bakinsa anatse ya  fara magana sunan wanda ya ambata da abinda yake son tayi masa ne yasa ta soma rubuta text message  ta turawa ATA sakon ya samu ata alokacin da yake zaune a a gurin shakawata a gidansa  tare da yaronsa V.O ahmed ya d'auki wayarsa  ya soma karanta sako Kamar haka "Assalam, mai gida yaushe zaka shigo   saboda ina da magana da kai .  ATA  ya ajiye wayar  cikin jin haushi yana kallon Ahmed "M Malik na yi  maka uzuri saboda tunaninka ya canza idan ba hk ba zakayi magana dani me yasa bazaka fad'a min ba ko ta hanyar text message ne tunda zaka iya rubutu ya qarasa mgnr tare da yin shiru "ranka ya dade wannan gsky ne DG m malik yana cikin wani hali sai dai addua kawai  "to allah ya bashi lafiya amman ni ko zan shiga wannan kasar ba yanzu ba watakilla ma har su dawo qasar nan bazan samu damar shiga ba ya juya ya kalli Musa. "musa  Kai !"musa ya qaraso da sauri ya iso gaban ATA cike da  ladabi "dauki buhunhuna  nan na Ahmed ka kai masa bayan motarsa "to yalla'bai!ya juya da sauri suka cigaba da tautaunawa ."

"Gaskiya kema maryam  da laifinki, taya zaayi ace har wata shida cikin na bakwai da yin aure amma ki kasa shawo kan mijinki ku zauna lafiya bare har wani abu ya shiga tsakaninku maryam ta girgiza kai tana cewa “ya kusanceni sau d’aya bayan nan ne dai har yanzu shiru gashi nayi duk abinda zanyi dan mu zauna lafiya dashi amman yaki bani lokacinsa "ki bude masa aiki kawai ko zama ko rabuwa maryam tayi saurin zaro ido tana cewa "kai ni’ima bazan iya ba gskiya ai sai ma ya kasheni da duka ."ni’ima diyar yayar mahaifiyar maryam ce da suke ciki daya aikin soja né ya kawota lagos daga zuru “duka ?”Ke kuma sai ki tsaya ?”idan dai zai huce idan ya dakeni sai na tsaya mana "to dama fa an fada min bakya son laifin mijinki,kowa yaga wannan abun yasan mijinki baya sonki kuma bakya gabansa amman ke har wani side dinsa kikeyi maryam ta zauna a kujera a sanyaye  ko da yake " illar wani auren zumuncin kenan “wallahi ni’ima ba side dinsa nake ba kawai soyayyarsa ce tayi min yawa shiyasa nake hakurin zama dashi dan ko na bar gidan nan gangar jikina ne ya bar gidansa amman ruhina yana gidan nan “.

“Ai kuwa kina da aiki ta yaya ma kike bashi kulawa muji idan akwai inda kuskure yake ki gyara ?babu abinda banayi masa na kyautatawa duk ta zayyane mata amma duk a banza ko kallona fa baya son yi “amman maryam kuma bakya tunanin ko wata ce take dauke masa hankali a waje ? maryam ta  girgiza mata kai tana cewa “bana tunanin haka! dan miskilancinsa bazai bari ya kula mata ba abinda na fahimta kawai shine, yaya Adam yana son wata yarinyar mafarkinsa amman azahiri bai san meye so ba "ta yaya zaace mutum kamar wannan bai san meye so azahiri ba ?"To in ma dai ya sani banga hakan a zahiri ba sai a mafarkinsa ya sani , amma ina fatan wata rana ya dandani radadin so irin wanda nake dandana a zahiri ko hakan zai sa ya tausaya mini ya bani kulawar data dace. " ina zai dandana tunda kince bai san meye so a zahiri ba ?ni’ima ta fad'a sannan  ta soma cin abincin da maryam ta kawo mata maryam tayi shiru dan itama bata san mai zata sake cewa ba .”
Chapter 69 · 0% Book details