← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 226

Sashe 94

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Waiwayowa tayi inda nafisa ke tsaye bayan ta cikata,sai ta tsinci nafisan na kallonta
"Waye wannan sumayya?" Ta jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba,boyayyar ajiyar zuciya ta saki gabanta na bugawa,hakanan Allah ya dora mata wani tsoronsa
"Nima ban sanshi ba" ta fada tana ci gaba da jan nafisan don su bar wajen,batasan me zata ce mata din ba,saidai baki daya gwiwoyinta sun sare kamar an doke mata su,kamar qafarta ba zata iya kaita gida ba
"Taya zaki ce baki san ko waye ba bayan na shinshino alamun sanayya tattare da ke?"
"Kiwa Allah kada ki qara tambayata,don ban sanshi din ba"
"Ala kyauta" nafisan ta fada ba tare data sake tambayar tata ba,haka suka isa gida tamkar kurame.

Cikin sanyi jiki ranar baki daya ta wuni,girkin ma data fita ta sayo ingredient din bata iya yinshi ba,ta cewa anty dije bata jin dadi,sai ta koma daki ta kwanta kawai lamo,bata fadawa anty dije ga wanda ta gani,to tace mata me?,tace taga wa?,meye hadinta da su da zata sanar mata haduwarsu?,ta tabbata su laila basu ganshi ba tunda bata ji sunyi maganarsa ba.

******* ****** ********

Sannu sannu kwana nesa,yau da gobe kayan Allah,sai gasu sumayya sun fara hada komatsansu waje guda,wasu suna aikowa da su nijeria wasu kuma suna faka su waje daya,wata daya ne ya rage musu wa'adin zamansu a qasar ya qare,wato sati hudu zuwa biyar masu zuwa zasu bar qasar,tuni nafisa ta soma qaguwa suma su koma gida,ta fuskanci lallai idan su sumayyan suka barsu qasar sam ba zata ji dadin zama ba,zulaiha ce abar tausayi,wadda Allah ne yasan ranar komawarsu,zata yi kewa ba kadan ba,saidai tilas ta haqura.

Hutun sati guda uncle farouq suka samu,hakan ya sanya suka zauna sukayi dukkanin lissafinsu na abinda zasu saya wanda zai musu amfani,ranar da daddare suka shirya zuwa wani katafaren mall wanda ke saida dukkan wani abun buqata,kama daga mai qaramin kudi zuwa mai babban kudi,duk wani abu na amfanin dan adam,sutura zuwa abinci da abunsha suna saidawa a wajen,basa bude gurin sai qarfe shidda na magariba har zuwa tsakiyar dare.

Uncle farouq ya kira ya buqaci taxi da zata kaisu ya bada adress dinsa,cikin mintuna qalilan ta iso,shine zaune a gaba shi da minal,su kam suna baya,hira suke sosai cikin motar,wanda ita bata ma san me suke cewa ba saboda tana amsa wayar abdur rahman ne,bayan ta kammala ta maida wayar jaka,dubanta anty dije tayi cikin salon tsokana
"Nafa lura kwanaki biyun nan ana dasawa da abdur rahman,ko yaushe cikin waya,ko dai da shi za'ayi ne?" Kunya ta bata saboda uncle farouq dake cikin motar,sai ta kasa magana ta saki murmushi kawai,dariya ya danyi yana daga gaban motar yace
"Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi kurum"
"Amin" cewar anty dije.

Ta kai kimanin aqalla minti ashirin tana nemansu cikin katafaren shagon bata gansu ba,ta duba anty dije da uncle farouq babu su ba alamunsu,tuni ta soma tsurewa,ta ajjiye kwandon dake hannunta ta soma laluben hanyar fita nan ma ta kasa ganeta,qwalla ta cika idanuwanta jikinta ya soma rawa,ina yaran sukayi?,ina su anty dijen suke?,idan ta rasasu ta yaya zata iya komawa gida?,wannan tunanin ya sanyata qara sauri,data fita daga wannan bagaren saita fada wancan saidai ko qyallinsu bata gani ba.

Wani irin burki ta taka wanda ba don tayi saurin dakatawa ba babu abinda zai hana su yin karo da juna,dubanta yake kamar yadda take dubansa,kamar ko yaushe fuskar nan a murtuke babu walwala,kai kace bai taba dariya ba a duniya,gabanta ya shiga faduwa kamar kullum,ji take kawai tata ta qare,ta rasa da mutumin da zata hadu sai da wannan?,kamar yadda al'adarsa take,saye yake da suit qirar company dolce anda gabbana baqaqe,hannayensa saye cikin aljihunsa kai kace babu abinda yazo siya,daga ita har shi babu wanda ya motsa,ita bata wuce ba tana kallonshu,yayin da shi kuma ke duba turarukan dake jere reras yana karanta sunayensu daya bayan daya,tuni hawayen da take adanawa suka soma samun hanya da zuciyarta ta raya mata su anty dijen sun bace mata fa,wata qila ma sun bar mall din suna nemanta suma,tattaro ragowar qarfin ta tayi da niyyar rabewa ta wuce don yana tsaye ne tsakiyar hanyar,ya raba hanyar gida biyu.

Hannunta guda daya taji an riqo,wata zabura tayi ta waiwayo qirjinta kamar zau fado,taushi da laushin tafin hannun nashi na ratsa jiki da jijiyoyin jininta,bai ko dubeta ba ya soma jan hannun nata,bata da wani qwarin gwiwa da qarfin da zata qwace,ko wacce gaba ta jikinta an zare mata laka,abu daya zuciyarta ke raya mata,yau tata ta qare,don wannan mutumin babu alamu na imani ko tausayi tattare da shi,Allah ne kadai yasan me zai aikata,hawayenta suka qaru tana biye da shi tamkar raqumi da akala.

Wani farin ciki ya mamayeta saboda hango su anty dije da tayi su da yaran bangaren kayan yara,a hankali ya zare hannunshi cikin nata tare da juyawa ya barta a wajen,sai ta waiwaya tana duban yadda yaje tafiyarsa ba tare ko ya sake waiwayowa ba
"Laaaaah,ga anty sumayya can,yaa mustapha ne ya kawota" cewar khalipha wanda shi daya ta hangi isowarsu gun,tuni mustapha ya bace a gun,anty dije ta dago tana dubanta,sai kuna tayi turus ganin hawaye fuskar sumayyan
"Lafiya?,ke kuma me aka yi miki?"
"Amma anty nayi tsammanin kun tafi fa,idan na bace nan gun wa zai maidani gida?" Dariya ma ta baiwa anty dijen ganin yadda sabbin qwalla ke sake saukar mata
"Kina nufin har yau da sauranki sumayya?,ta yaya zamu taho da ke mu koma babu ke?,bakiji sanda nake gaya miki kici gaba da siyayyarki ba zamu zo nan gun ki samemu wajen biyan kudi?,to don Allah ya ma za'ayi ki bace wajen da duka ko ina cctv camera,an fada miki nan irin nijeria ce?,ti waye ya rakoki?" Ta rufe maganar tana dariyar wautar sumayyan ciki ciki,kafin ta amsa khalipha ya bata amsar tambayar
"Hala yaganki kenan kina kuka kamar qaramin yaron da ya bata" laila sau ta sanya dariya,harara sumayyan ta maka mata don kusan itace ta sanya bata ji sanda anty dijen tace mata suna zuwa ba,isowar uncle farouq yana dariya ita ta tsaida dramer da akeyi
"Tom,musty yace mu kula,ya lura yarinyar nan sakarai ce,kada ta janyo mana abinda za'a kamamu kan mu bar qasar nan,kinsan su mai jan kunnuwa akwai kula da haqqin dan adam" dariya suka sanya shi da anty dijen yayin da wani abu ya tsayama sumayya a wuya,ita za'a kalla a cewa sakarya?,aikin banza ita tace ma ya kawota da zai gaya mata magana,ita kadai ke masifarta cikin zuciya ta qulu ta cika tayi fam,siyayyar da bata qara darawa nan da can ba sai anty dije ce ta qarasa zabar mata abinda taga ya dace,gani take ko ya ta matsa zasu sake yin clashing da shi.

Sai da suka shiga mota sannan ta dubi anty dije,shaf ta manta cewa sunyi zata bata kudin da baabaa ya bata randa zasu taho zata siyawa amira wani abun a gift din biki
"Anty,banfa daukawa amira komai ba"
"To me za'a siya mata,su fa irinsu komai suna da shi,amma ki bari idan mun koma gidan kwayi shawara da nafisa sai ki siya mata abinda ya dace"
"To" ta fada tana jingina da kujerar cikin mutuwar jiki hannayenta runguma a qirjinta.

Da sukayi shawara da nafisan sai taga kawai tayi mata danginsu humra,turaren wuta na daki kaya dana tsuguno,collucture tana ganin zasu burge,shawara kam tayi mata,tasan amiran kuwa da jarabar son humra,akwai wani company wadanda ke qera crystal kala kala masu azabar kyau,nafisan tayi oder din kwalaben da sumayyan zata zuba kayan idan tayi,batasan da su ba sai kiranta nafisan kawai tayi ta nuna mata bayn an kawo,kwalaben humra kadai saiti uku uku sai data siya saiti bakwai kusan kwalaba ashirin da biyar,haka ta turaren wuta da wasu dogaye da za'a zuba collucture,kwalaben kansu abun kallo ne,wani irin design aka yi masu masu matuqar tafiya da hankali,kasa magana sumayya tayi,karamcin nafisa ya girmi qwaqwalwarta,sai ta zauna akwai tana kallon nafisan ita kuma tana murmushi,baki ta bude da niyyar hada kalmomin godiya sai tayi hanzarin tararta
"Kada kice komai,kada ki godemin,nima gudun mawata na baki ki baiwa qawarki,duk da bamu taba haduwa da amira ba amma tana da kirki iya gaisawar da muke,kuma taci darajanki sister", anty dije kanta rasa me zata ce tayi,sai albarka take sanya mata tare da fatan dorewar zumuncinsu da addu'ar kade fitina,cikin kaya suka shirya kwalaben yadda ba zasu fashe ba.

********* ****** ********

Randa zasu koma nijeria nafisa na tare da sh,ita da auwal suka suka rakasu har airphort,jirgin dare zasu bi,batasan me ya sauya lokacin tashinsun ba,don da taji uncke farouq na fadin jirgin safe ne,tuni sukayi sallama da zulaiha,har kuka sai data yi,ji take kamar tabi sumayyan,to itama din nafisan tuni ta narkewa auwal ta soma masa qwalla,khalid kuwa ba'a magana jiki duka ya mutu,ya fuskanci anty sumayyan tafiya zata yi ta barsu,ai kam ashe kuka na gaba,sai da suja zo tafiya auwal ne ya janyeta yana rarrashinta
"Is ok dear,muma fa nan da wata daya zamu koma keye ya rage ne?,wata dayan kwanaki nawa ne?,haba momyn khalid,goge qwallar khalid na dubanki" da qyar ta tsaya sukayi sallama auwal yayi dabarar dauke khalid sannan nafisan ta biyo bayansu.
Chapter 94 · 0% Book details