← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 226

Sashe 127

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Wayarta dake hannunta ta dauki vibration sanda amarya ta samu zama a gurbinta ita da angonta,sunan nafisa ta gani,mamaki ya cikata ganin number dinta ce ta nijeria,qarar lasifiqan wajen bazai barta taji ba,hakan ya sanya ta soma takawa don barin wajen tana duban kiran,can baya inda zata iya jin ta ta tsaya ta soma lalubarta saboda kiran ya riga da ya katse
"Am at home sisi" idanu ta fiddo waje
"Da gaske?"
"Suprise wlh naso baki,shigo gidan anty ki shigo dani yau traditional setting na amira ina lissafe dama"
"Wayyo sis,gani nan" ta fada cikin zumudi da murna ta kashe wayar,daidai sanda kida ya soma tashi daga inda ake gabatar da bikin,tsalle ta dan saki kadan farinciki fak ranta
"Yi a hankali gimbiya kada ki fadi ki batan kwalliyar" abinda taji an ambata kenan,da sauri ta waiwayo,alqasim ne tsaye sanye da shadda ya kawo hula gaban goshinsa yana qare mata kallo yana murmushi,daidaita natsuwarta tayi sannan ta juya da niyyar ci gaba da tafiya,saurin shan gabanta yayi,ya wani karyar da kai
"Haba sumayya,ko gaisawa i kya tsaya muyi ko?" shiru tayi tana dubansa ba tare data ce komai ba,ji take kawai zai bata mata lokaci ne,bata da buqatar wani abu a yanzu,tana cewa ta gama da babinsa,tunda tuni ta gaya masa ita din ba budurwa bace bare ya saka ran zata biye masa,idanunta tarufe tare da yin banza da shi,tana jinshi yana magana ci kanka bata ce masa ba.

       Tunda suka fara tashin kidan ya tashi ya shiga bathroom ya sake wanka,jin kidan yake kamar a tsakiyar kanshi,duk wani abu da zai zama tamkar hayaniya bai qaunarsa,ko qwaqwaran motsi ne ya fiya yawa yanzun zai dameshi,sau tari babban wansi adam kance
"Kai ko mustapha kamar mai aljanu,koyaya motsi yake sai ya dameka" amma hakan bai rasa nasaba da ciwon kan da yake fama da shi tsawon shekaru,wanda idan ya tayar masa baya masa ta dadi.

         Ta baya yabi don bai muradin haduwa da kowa bare a tsaidashi a cikashi da suruti,baki daya yau zucuyarsa a quntace take,saidai ko kai daka sanshi baka isa ka fadi hakan ba,sakamakon yadda ko yaushe haka fuskarsa take a daure koda cikin farinciki yake indai ba girmama farincinkin yayi ba shine zaka ga fuskar ta sake washewa fiye da yadda take da,yatsanshi saqale yake da maqullin motar da yake sha'awar fita cikinta,tun kafin ya shiga wankan ya turawa P.A dinsa ya shirya haduwarsa da mutanen da yace jiya bazai samu damar ganinsu ba qasa da awa daya yana hanya kada su wuce haka,sannan ya turawa driver dinsa shima ya shirya motar da zai fita,kanshi a qasa yake takowa cikin shigarsa ta qa'ida trouser da t.shirt v neck wanda ta fidda structure ta jikinsa sosai,kwata kwata saka manyan kaya bai cikin tsarinshi,duk wanda yasan mustapha cikin duniyarsa yasan ba ma'abocin sanya manyan kaya bane,kana iya gama mu'amalarka kaf da shi baka ganshi da manyan kaya ba,daidai gun da jiya suka zauna wasa ya tuna,yaron ya fado masa,ya tuna shegen wayonsa,wani qaramin murmishi da bai shirya masa ba ya kubce masa,a hankali ya daga kanshi sai ya hangosu,tsaye yake a gabanta yayi kane kane kamar zai hade gaf din dake tsakaninsu,yayin da take tsaye hannayenta harde a qirji tana dubanshi,rashi ya baci,dan salaman da ya samu ta gushe,yana daya daga cikin abinda yasa kenan baison baqin 'yammatan cikin gidansu,yana zaton daga daga cikin 'yan matan family din nasu ne,sauya akalar tafiyar tasa yayi zuwa wajen,sai da yaje dab ya lura alqasim ne
"Itakam haka take,gobe wancan mutumin jibi wannan?" Ya qarasa bayansu,daidai sanda take fadin
"Na riga na gama magana da kai ko?,ba zaka taba samun abinda kake so ba,so don Allah ka qyale rayuwata" ta kammala fadi sannan ta juya a hankali ta soma barin wajen,burinta kawai ta isa ga nafisan gashi ya bata mata rai da lokaci baki daya,binta yayi da kallo har sai data bacewa ganinsa sannan ya juyo yana sakin ajiyar zuciya,sai suka hada idanuwa da mustaphan yana kallonshi,kunya ta kamashi,yana bala'in ganin girman almustapha da mutuncinsa,girmama shi yake qwarai da gaske,ya dan diririce yana fadin
"Barka da fitowa yaya" bai amsa ba ya qara taku zuwa inda yake yana dubanshi,haushi yakeji,hashi ya kamashi,ji yake kamar shi akawa haka
"Kan me ka tsaya mace na gaya maka irin wannan maganar ibrahim?,kai namiji ne ka manta?,so kayi maintaining dignity dinka,akwai mata da yawa a gari ka zabi wata mana,kar ka cusa kanka inda ba'a sonka,ba'a so dole,i hope ka fahimta?,ba ita daya bace mace akwaisu da yawan gaske" kai ya rusuna yana gyadashi alamun gamsuwa,cikin zuciyarshi yana cewa
"Ya mustapha kai baka hango abinda na hango ba,baka hango personalityn dana gani tattare da ita ba,hmmmm ke ka ganin so wani abu mai sauqi ne tunda kullum cikin neman son ake a wajenka"amma a fili sai yace
"na gode,Allah ya qara girma" kai ya jinjina ba tare da yace komai ba ya juya ya bar wajen.

      Kamar ta goya nafisa haka taji lokacin data ganta,tayi ado sosai tana rungume da khalid,ta amshi khalid din kai tsaye suka koma wajen da ake kamu,sanda suka je tuni al'amura sun fara nisa,bayan gabatar da abubuwan da suka dace sannan aka kama amira kafin daga bisani a bada damar yiwa amarya da ango liqi,basu suka tashi daga kamun ba sai qarfe takwas na dare,kamu ya qayatar matuqa da gaske,tafiya nafisa tayi bayan sun gaisa da amira sama sama,taso riqeta tace a'ah tayi haquri abban khalid din ya iso,saidai zata zo dinner insha Allah wanda za'ayi ranar alhamis.

       Washegari akayi arabian night wanda aka gabatar da ita itama cikin gidan baabaa prof,gidane gari guda hakan ya sanya basu da damuwar sai sun kama waje,ba qaramin qawata wajen akayi da kayan ado ba,ranar duk wani ahali da ya shafi baabaa prof sanye yake da abaya ta mata,maza kuma doguwar riga ce da hirami,kai ka rantse a ranar baqin larabawa aka yi a unguwar.

 ******* ****** ********     

Washegari tana kwance tana baccin gajiya,kasancewar alhamis ce ranar babu event din da za'a yi sai gobe idan Allah ya kaimu,ji tayi an daka mata duka,tilas ta farka tana mutstsike idanu,amira ce zaune gefanta
"Sannu,ai wallahi bacci bai ganki ba bai kuma kamaki ba,qarfe hudu zamu lunching na maman saifullahi,kuma ba kowa ne zashi ba,bamu da yawa" zama tayi sosai tana hamma hannunta kan bakinta
"Shine zaki dakamin wannan dukan,badon inajin kunyar idanun saifullahi ba sai na rama" dariya ta qyalqyale da ita
"Ato bismillah,ni kinga ina da mai ramamin,ke kuwa nasan ko na dakeki na daki banza,waccan mutumin da na gani a kano babu abinda zaya iya" ta sani sarai da abdur rahman take,bata san meye hadinta dashi ba data saka masa tsama haka da yawa,harara ta jefa mata sannan ya shiga bandaki ta wanke bakinta ta dawo ta amshi katin tana dubawa,komai a tsare yake harda dress code na maza da mata,mata shigan baqi zasuyi maza shigan fari.

        Kusan baki daya kayanta sai data baje su saman gado,ta rasa wanda zata zaba,a haka anty dije ta cimmata,dariya ta dinga yi mata
"Ato wallahi gwara ki qure adaka,don suma dangin saifullahin ba baya bane"sai data gama ruwan idonta sannan ta zabi wani shegen lace a cikin kayan wanda yake baqi ne an masa adon ja mai daukar idanuwa,zuba kayan tayi a jaka don ta nufi gidan baabaa don amira na can na jira,sanda ta isa an gama mata kwalliya,tayi masifar kyau cikin baqar wedding gown,sumayyan zama tayi itama aka soma yi mata tata.

         Wani irin sihirtaccen kyau ke fita daga kwalliyarta hadi da tsumammen qamshi,kunya ta kamata da mamakin kanta,riga da skert ne wanda suka fitar da baki daya qirarta gaba da baya
" wow"abinda amira ta dinga fada kenan tana qarewa sumayya kalo
"Haka baqin kaya ke miki kyau amiran umman khalipha?,ya Allah" kai ta kada
"Ai kam cire kayan nan ya zamemin wajibi,ina zan iya fita cikin jama'a haka amira" ta fada tana yunqurin cire daurin dankwalin da aka bata lokaci ana mata shi,da sauri amiran ta riqe hannunta tayi kicin kicin da fuska
"Allah idan kika cire sai mun bata,ke komai ma bakison ya miki kyau,kina da kyau kina da aji kina da isar da za'a dama dake,kibar yin haka don Allah" yanayin yadda tayi maganar ta bata dariya,sai ta zame hannunta tana hada mata kayayyakinta data yi amfani da su kasancewar yau cikin dakinta ta shirya
"Bari na maida su sashin anty maamaan ko"
"Godiya namescy na" murmushi tayi ta fice a dakin.

       A shirye ta tadda anty mamman,kasancewar ita zata yiwa amiran rakiya,wani irin biki suke a tsarin familynsu,suna gayyatar amarya ne da manyan yayyenta da iyayenta,inda zasu kawo musu ita suyi mata nasu bikin ma musamman haka sukeyi,ta ajjiye kayan tana saukowa suka sake kacibus da anty maamaa wadda ke kai kawon hadawa baabaa kunun alkama,haka matan suke,duk rintsi basa wasa da cikin mijinsu
"Amiran umman khalipha zo don Allah ki kulamin da kunun nan in qarasa hadawa babanku hadin salad din nan"aladabce ta asawa ta bita kitchen din,cikin sauri sauri take hada komai saboda lokacin tafiya yayi,sau uku amira na aikowa sumayyan tazo su tafi,antyn bata sani ba,sai ana hudu taji aiken da ake mata ta dubeta
"Jeki amira,na qarasa na biyoku daga baya" murmushi tayi tana noqe kafada
"A'ah anty suje kawai,ma taho".

     Cikin mintuna talatin suka gama,babu abinda jikinta yayi,saboda haka goge hannunta kawai tayi,sannan ta fidda kwalakcarta ta goga a hannayenta,ta sake shafe jikinta da turaren humrarta mai fidda wani sihirtaccen qamshi,wayarta dake ruri anty maman ta daga ta kara a kunnenta sannan tace
"Eh na gama,gani nan" ta dubi sumayya tana maqala kyakkyawar jakarta
"Muje ko amira" ta amsa.
Chapter 127 · 0% Book details