← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 226

Sashe 41

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Kafin gari ya waye tuni komai yayi tsaf daga uwar har dan har gurin da akayi naqudar,maman ce ta shigo da yaron dake nannade cikin shawul ruwan sararin samaniya bayan sunqufe shi da akayi cikin lallausan kayan sanyi suma ruwan bula din,malam ta kaiwa shi bayan ya dawo sallar asubahi ya ganshi,ya sha addu'a kuwa bayan wasu sirrika da ya hada ya dangwala masa a baki,sumayyan na gefan gadon mamam riqe da kofin shayi mai kauri da maman ta hada mata kan ta fita da yaron,har yanzu ta gaza shanyeshi saboda bacci dake dibarta
" karbeshi ki ganshi sumayya ki masa addu'a"maman ta fada tana dora mata shi saman cinyarta bayan ta karbo kofin shayin data samu ta shanye.

     A hankali kamar mai tsoron tabashi ta sanya hannu ta tallabeshi,take idanunta suka cika taf da qwalla,a sanyaye ta sanya hannu ta yaye rufin fuskarsa idanunta suka sauka kan fuskar tasa wadda idanunsa ke rufe ruf yana ta sheqar bacci cikin lumana da kwanciyar hankali,kallo daya tayi masa ta hango kamanni na kai tsaye da yaje da babansa duk da ba idanunsa biyu ba,a kallon farko taji wata iriyar qauna da soyayyar yaron ta mamayeta,irin qauna ta da da mahaifi,tausayinta kuma ya samu gurbi cikin zuciyarta karon farko data tuna irin siradin da rayuwarsa ta tsallake kafin ya kai ga isowa zuwa ga wannan fili da muke kira da duniya,sai gashi Allah ya nuna ikonsa,yaro qato kyakkyawa mai cike da qoshin lafiya,wanda ko cikin mafarkinta bata taba tunanin zata haifi kamarsa ba
"Bawan Allah" ta furta ba tare da tasan a fili ta ambaci hakan ba qwalla na kwaranyo mata,daga shi tayi zuwa fuskarta ta karkata kunnensa na dama ta karanta masa kiran sallah ta karkata na hagu ta karanta masa iqama sannan ta ambata masa sunansa *ABDALLAH* bawan Allah.

     Murmushi mama tayi ta dubeta
"Amma kya jira babansa yazo ya zaba masa suna ko?" Kai ta girgiza
"Kiyi haquri mama,ni yafi kamata mama na sa masa suna,ni kadai nasan wahalar da nasha,daga ni sai ubangiji na ma......." Sai ta kasa qarasawa saboda karyewa da zuciyarta tayi
"Kukan ya isa haka,yau ranar murna ce,ajjiyeshi kusa da ke,maza so nake ki kwanta kiyi bacci sosai" bata musa ba din tayi yadda maman tace,tun tunaninnika na bijiro mata har wani nannauyan bacci mai dadi yayi gaba da ita.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣5⃣

_______________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wallazi yumutuni summa yuhyi,wallazi adma'u ay yagfirali khadi aty yau maddin*

______________________________

A makare ya tashi yau wanda hakan ya sabba ba masa yin sallar asubahi cikin gida,tunda ya idar da sallar yake zaune saman daddumar bai tashi ba kamar yadda bai aiwatar da komai ba,tunanin sumayya ne fal zuciyarsa yau ya wayi gari da shi,hakanan yake jin wunin yau ba zai iya qarewa ba ba tare da yaje ya ganta da lafiyar abinda ke cikinta ba,kusan tunda ta shiga watan haihuwarta da ita yaje kwana yake tashi.

Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzari,ya juya bangaren da take ya jawota ya duba,baquwar lamba ce,ya latsa sannan ya kara a kunnensa,runtse idanunsa yayi zuciyarsa ta soma quna saboda muryar wadda yaji,bai taba jin ya tsani wani abu tsana mai tsanani ba irin na mamallakiyar muryar,zainab ce take magana cikin maqale murya da wani irin salo nason tafiyar da hankali,tun a daren jiya bokanta wanda take kira da malam ya bata wannan sa'ar ya kuma tabbatar mata bayan sallar asubahi ne zata sameshi,sanda ya daga wayar zuciyarta sai ta cika da farincikin samun nasara,don dama ya sanar mata bayan sallar asubar a gobe bazai koma bacci ba,jin tana ta magana ya mata shiru ya sanya ta fashewa da wani makirin kuka
"Habaa my mukhtar,dama laifin wani kan iya shafar wani?,mene laifina ni a ciki?,duk iya yina nayi don inga abinda ke cikin yarinyar nan ya kubuta,duk tarin hidima dana dinga yi da ita rana daya duk ka mance ka watsar da alkhairi na a gareku ka sakeni,kuma ma tunda an samu cikin na nan ba shikenan ba komai ya wuce sai ka maidani daki na ko?".
Kamar garwashin wuta haka yaji kalaman nata,cikin harzuqa ya dakatar da ita
" ke wacce iriyar jahila ce wai?,shin kin manta zama ni dake a yanzu ya haramta ne sau nawa zan nana ta miki,ke koda kuwa ma zamanmu ya halatta bazan iya zama da kowacce mace ba a yanzu,tunda sumayya da na raina da kaina ta iya min haka babu wata diya mace da ba zata iya aikata min makamancin haka koma fiye da shi ba,saboda haka gargadina dake na qarshe,kada ki sake gigin kiran layi na ko tarar hanyar da kika san zan bi,idan kuma kinqi ji ba zaki qi gani ba"daga haka ya katse kiran ya ajjiye wayar a fusace.

Daga daya bangaren nata itama ajjiye wayar tayi tana huci sannan ta dubi qawar tata
"Wannan wanne irin mutum ne haka?,duk zama da wuyar da muka sha wajen malam ta tashi kenan a banza,kinji maganganun banzan da yake gaya min?,to wallahi wannan karon babban aikin zan saka a masa koda duniya zata zageni,ko zanyi yawo babu zanin daurawa" kafada ta daga tana fadin
"Au ho sai yanzu kika gane kenan?,tuntuni ai malam din ya gaya miki ki saki naira kiga aikin da ko uwarsa dake kabari ba zai ganta a gabansa ba sai ke" miqewa tayi ta fice daga dakin fuuu tana fadin
"Ai anzo gurin kuma".

A hasale ya kuma waiwayowa ga wayar tasa jin ta sake tsuwwa a karo na biyu yana zaton ita din ce ta sake kiransa,sai jikinsa yayi sanyi gabansa ya fara faduwa ganin sunan abubakar kan screen din,cikin sanyi da sallama ya amsa wayar,lumshe idanuwa yayi wata rahama na sauka cikin zuciyarsa lokacin da abubakar ke furta masa albishir mafi dadi da ya taba sauraro tsawon rayuwarsa,sumayya ta haihu ta haifa masa yaro,baisan adadin lokacin da ya dauka ba cikin duniyar madaukakin farinciki shidai ya farka yaga har kiran na abubakar ya katse.

Faduwa yayi saman a bin sallar yayi sujudush shukur yana mai tasbihi ga ubangiji,bai wani jinkiri ba ya miqe ya fada makewayi ya shiga wanka,cikin mintina talatin ya fito,kai tsaye gaban sif dinsa ya isa bayan ya tsane jikinsa,ya bude yana kallon kayan,a sanyaye ya sauke hannayensa yana duban kayan kala bakwai da suke sababbi dukkansu,ba zai manta randa ya bada dinkinsu ba,tun cikin sumayya na da wata uku a lokacin tana gidan,musamman ya tanadesu ya dinkasu saboda ya sanyasu tun daga rana ta farko da aka haifa masa yaronsa har ranar suna,baya iya manta lokacin da take dariya tana tsokanarsa da cewa gandoki,sai ya koma bakin gadon ya zauna yana yarfa hannu,yana jin yadda bacin rai ke taso masa yana son danne farincikin da yake ciki,baisan mai yasa har yau zuciyarsa ta kasa daina jin ciwon abinda tayi masa ba duk da cewa an cimma nasarar tsallakewar cikin gashi har yau Allah ya nufa ya iso duniya.

Da qyar ya samu ya hadiye wani dunqulen abu mai daci sannan ya miqe ya shirya cikin wani yadi mai kyau na maza fari sol wanda ya masa kyau sosai,ko abinda zai sawa cikinsa bai nema ba ya fito don dama ba ko yaushe yake samun damar karyawar safe ba,yana shirin tada motarsa ya kira ya yahansu ya shaida mata,hamdala ta dinga yi matiqa da gaske tana jin dadi a zuciyarta,ta kuma shaida masa lalle ya biyo gidan nata kafin ya wuce.

Kafin sha daya na safe tuni gidan ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan arzuqi,kowa barka yake mata tare da tayata farincikin wannan rana da aka jima ana saka ran zuwanta,sam ita bata san me ake ba ma,bacci take sosai ita daya a dakinsu,yaron shima nashi baccin yake,sai da ya farka ya fara kuka alamar yunwa sannan mama ta baro dakinta wanda suke zaune da mutane ta shigo dakin ta tasheta,sai data sake hada mata shayi mai kauri ta sake sha sannan ta dora mata shi saman cinyarta ta fara koya mata yadda zata shayar da shi,runtse tayi sannan ta fara qorafin zafi maman tace
"A haka zaki daure har ki saba".

Sallamar da kunnuwanta ya jiyo shi ya sanya jikinta saki,sai ta zubawa bakin qofar dakin ido tare da barin qorafin da takeyi,halima ce ta shigo
" mama ga yaya mukhtar"
"To ya shigo mana" ta fada tana gyara mayafin jikinta,qasa sumayya tayi da kanta tana duban yaron dake saman cinyarta yana tsotsar nono a hankali,sallama yayi cikin dakin sannan ya qaraso a nutse hannunsa dauke da qatuwar baqar leda,baki daya idonsa na kan sumayya da yaron wadanda kowannensu yake jin mabanbantan yanayi a kansa cikin zuciyarsa,wata qauna ta musamman yaji ta dirar masa tun kafin yayi tozali da gudan jinin nasa,yayin da tausayi da kuma wata daraja ta sumayya ta daban yaji ta ginu a ransa,a mutunce suka gaisa da maman sannan ta miqe ta fice,shiru ya ratsa dakin bayan ficewar tata,shi yana zaune yana aukin kallonsu ya rasa daga inda zaya fara,yayin da itama taqi motsin kirki dukkan idanunta na kan yaron nata tana dubansa,tana jin yadda yake zuqar mama har cikin ranta,ci gaba yayi da dubansu wani yanayi na ratsashi,sai suka burgeshi sosai,karo na farko da yaji zai iya yafewa sumayyan kome tayi masa,yana ji a yanzu ta cancanci yafiyarsa.

Cikin qwarin gwiwa da karsashi yayi gyaran murya tare da muskutawa yace
"Sannu sumayya"ta dan cije lebe kadan sannan ta amsa can qasa
" yauwa"
"Sannu da qoqari,Allah ya saka miki da alkhairi,na yafe miki sumayyan duk wani abu da kika yimin" da sauri ta daga kai ta dubeshi sannan ta kau da kai
"Bana buqatar yafiyarka tunda ni din ban aikata maka ko wanne laifi ba,hasalima ni nafi cancanta da a nemi yafiya ta" mamaki kalaman nata suka bashi,bai kai ga furta komai ba mama ta sake shigowa hannunta dauke da kofi cike da kunun kanwa yana tururi
"A'ah,baki bashi shi ya ganshi ba,ki cire shi haka idan ya gama ganinsa yaci gaba da sha ko" ta fada tana dire kofin tare da ficewa.
Chapter 41 · 0% Book details