Sashe 136
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malam yana daga falon ya qwalawa haliman kira,gama cire lallenta kenan taji kiran malam din,ta goge hannum nata ta sanya hijabinta ta shiga dakin
"kije sittin ro abdur rahman na jiranki" jin maganar tayi banbarakwai sai ta daga kai ta dubi malam
"Ni ko yaya sumayya dai?" Daquwa ya mata
"Dan gidanku na kasa gane sumayyan sai ke zan kira?,ke nace ba sumayya ba" bata sake cewa komai ba ta miqe ta fito ta nufi sitting room din gabanta na faduwa.
Tsaye yake tsakiyar sitting room din hannayensa goye a bayansa ya zubawa qofar shigowar idanu,tana sallama suka hada ido,karom farko taji wata faduwar gaban da bata taba jin irinta ba don ta kalleshi,idanu ya zuba mata yana amsa sallamar,sai yake hango yanayinta da sumayya muraran,ya taba kula da hakan shekarun baya amma ba kamar yanzu ba,ga mamakinsa murmushi sai ya subucewa lebansa,ya zuba mata ido yana ci gana da kallonta har ta qaraso gabanshi,cikim diriricewa tace
"Ya abdur rahman gani.....malam yace wai.....kana jira na"
"Bismillah zauna" babu musu ta taka ta zauna kan daya daga cikin kujerun,gabanta ya iso a hankali ya zube a gabanta wanda hakan ya sake haddasa mata faduwar gaba da,sai ta jita ta takura sabida basu taba zama gab da gab irin haka na,duk a qasa yake zaune a gabanta amma yana kusa da ita
"Halimatus sa'adiya,malam baice miki komai ba?" Kai ta gyada da sauri sabida ta gaji da yadda gabanta ke faduwa,murmushi ya dan saki,wato shi zai yiwa kansa yaqi kenan ko?,daga idonsa yayi ya zubesu a kanga,sai ta janye nata idanuwan
"Halimah kina sona zaki iya aure na?" Taji tambayar babu zato na tsammani,ido ta zaro tana dubanshi,kasa cewa komai tayi har sai da ya maimaita,bakinta na rawa tace
"Yaya abdur rahman.....yaya sumayya.....ita yaya sumayya fa?" Murmushi ya saki
"Bakya gidan ne?,bakisan malam ya bata wani ba?,ni kuma a yanzu malam ya bani ke zaki iya aure na?" Shiru tayi gabanta na faduwa,yayin da kunya ta kamata ta sadda kai qasa qwalla na taruwa a idonta,hakan taji tsoro ya kamata,malam zai aurar da ita kenan itama,jin shiru ya sanyashi sanya yatsunsa ya daga fuskarta,kallo daya tak yayi mata ya fuskanci ta karbi lamarin duk da bata bayyana ba muraran sabida kunya da tsoro
"Kice wani abu mana halimah,koda baki sona ki amince min zan saki ki soni kinji,kada nayi asarar zuriyar malam baki daya ace na rasa ko daya,da wallahi barin garin zanyi" dariya taso qwace mata saboda yadda ua shagwabe mata,kunya ta lullubeta saita qudundune kanta cikin hijabi,dariya ya saki
"Iyeeee,ko baki ban amsa ba ma na gano a bata,ashe dai har kunyar abdur rahman din akeji,lallai na samu karbuwa,koba haka bane?" Shiru tayi taqi amsa masa
"Shikenan tunda ba zaki ce komai ba bari na haqura na tafi,kuma ba zaki sake ganina ba,zan kuma gayawa malam baki amince ba sai na haqura" ya fada kamar mai tafiyar,da sauri ta daga kanta tana shirin cewa wani abu,sai ta ganshi tsaye a gabanta,kunya ta sake kamata tayi qasa da kai suna dariya baki daya.
Komai na Allah ne haka komai nufin Allah ne,sai gashi ya shantake har qarfe tara da rabi yana gidan,halima akwai kunya saidai alamu baki daya sun nuna ta karbeshi,sai goma saura sannan yayi mata sallama,ya zuba hannayensa a aljihu yana dubanta
"Ina wayarki" cirota tayi daga hijabinta,karba yayi yana qoqarim cire layin ciki ya zura a aljihunaa sannan ya ciro daya daga cikin layukansa ya saka mata yana cewa
"Gashinan,ni kadai zan dinga kiranki kafin na siya miki wani layin,ina da kishi bana son wani ya sake jimin muryar mata ta,sai da safe muje na rakaki" har bakin qofar shiga tsakar gida ya rakata sannan ya juya ya fice,zuciyarsa fes yana mamakin lamarin Allah,ya riga ya qaddara sumayya ba matarsa bace shine masanin GAIBU mai rubuta QADDARAR BAYINSA,Allah kenan mudabbirul amri mai jujjuya al'amura a lokaci da baka zata ba,ya shigo gidan cikin tashin hankali da jimami ya fita cikin farinciki da annushuwa,babu abinda zai cewa dattijon arziqi mai karamci sai godiya tare da yi masa fatan kyakkyawan qarshe.
Tana shiga tsakar gidan taga shigar zainab dakin mama wadda ta fito daga kitchen ta dafawa sumayya tea,da sauri tabi bayanta don fatinciki ke cinta,bata da 'yar uwar da take sharing sirrikanta da ita kamar zainab din,tsaye ta taddata tama fifitawa sumayya tea din,sam halima bata kula da sumayya dake dakin ba ta dane bayan zainab wanda hakan ua sanya tea din hannunta tangal tangal zai zube
"Wayyo zainab,yau Allah nima ya bani yaa abdur rahman,zainab mallam ya bawa abdur rahman ni,a gobe nima zanbi sahunku zan zama matarshi" sak sumayya tayi tana dubanta,tun dazun take jira taji wani abu daga wajen abdur rahman din ko malam amma taji shiru,gani tayi zainab tayi shiru kawai saita sake kallonta
"Baki ce komai ba ya kikayi shiru" da idanu tayi mata alama da wani na gun,ta wurga idonta saita hangi sumayya,da sauri cikin jin nauyinta ta juya zata fice,cikin kasalalliyar murya tace
"Zo yaki halima" cikin jin nauyinta ta iso inda take ta zauna,ta karbi tea din da zainab ke miqo mata ta aje gefanta
"Meye na jin kunyata halima kamar wadda ta aikata haramci,wallahi har ga Allah naji dadi da wannan hadin da malam yayi,sannan abdur rahman ya cika mai sonmu tsakani da Allah da son iyalan gidan nan,ki saki jikinki ni yayarku ce har abdur rahman din ba tun yau ba dama,ki manta da cewa abdur rahman ya raba sona,Allah shine dama yasan abinda ya boye shi yasa bai taba darsamin soyayyarsa ba ko qanqani,illa ganin girma da mutuncinsa da nake,babu wani abu da ya isa shiga tsakaninmu,dan uwa ba wasa bane,idan banda Allah babu wanda ya isa yayi maka kyautar dan uwa,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da alkhairi"
"Amin" suka amsa baki daya,taji dadin addu'ar sumayyan sosai,to tsakanin daren zuwa wayewar gari sun sake wata qwaryar
qwaryat shaquwa,kusan kwana sukayi suna waya sumayya na jinsu,wadda tuni ta goge duk wani abu da ya shafi abdur rahman daga wayarta,tayi lamo bisa gado,kewa ta kamata,ta dinga matse hawaye tana tuna mukhtar,mutuwa mai tonon silili,idan banda mutuwa ta dauke mata shi da tuni sun jima da shimfida sabuwar rayuwa,wataqila ma da tuni ta sake haifa masa 'ya'ya,saidai tsarin Allah shine tsari,(Allah kasa mu dace ka cika mana burikanmu kasa mu cika da imani don alfarmar sayyadina rasulullahi S A W)amin.
Washe gari kawu da wansa da qaninsa mahaifin abdur rahman sai gashi da safe yazo nemawa abdur rahman din auren halima,wanda ya bawa malam dariya,yace ai da abdur rahman da halima duka nashi ne,ko basu zo ba sai ranar daurin auren ya riga ya bashi ita,a nan kawun yayi godiya qwarai suka tafi,a nan suka bar abdur rahman ya sake baje kolin soyayyarshi,sai da aka soma nemansa a asibiti sannan ya tafi,binsu sumayya take da kallo,wato bawa bai gujewa Qaddararsa.
*KUNDIN QADDARA*
Rana bata qarya saidai uwar diya taji kunya inji malam bahaushe,wannan haka yake,domin yau take juma'a wadda ta kasance rana ce mai girma da muhimmanci da kuma dumbin tarihi wajen malam sulaiman gombe,wanda zai aurar da duka diyoyinshi mata da Allah bashi cikin mutunci da rufin asirj,wanda abun farinciki ne da godewa mahalicci a irin wannan zamanin namu mai cike da rudi da abubuwan firgici ga 'ya'ya mata Allah ya yi maka baiwar aurar da diyoyinka mata baki daya hannun nagartattun maza da kake saka musu ran zasu musu riqo na mutunci,ta hannu daya baabaa prof shima cike yake da farinciki,domin kuwa tun qarfe tara ya iso wajen a maimakon qarfe goma da za'a daura auren.
Daga cikin gida kuwa tuni zainab ta yi wanka kwalliya irin ta amare,tana sanye da wani lace mai azabar kyau wanda sumayya ce ta siya musu,haka amarya halima na sanye cikin shadda wadda ready made ce abdur rahman ya aiko mata da ita,tayi mata kyau ainun,dukkaninsu idan ka dubi fuskokinsu qunshe take da fara'a sabanin sumayya dake kwance ko wankan ma bata kai ga yi ba,binsu take da idanu tana rayawa cikin ranta,kowa yana rayuwar farinciki banda ita,ita kadai ke fadawa halin jarrabawa cikin yaran gidan nasu?,nafisa ce ta sanyata a gaba wanda tilas ya sanyata tashi tayi wanka ganin tana son qara mata ciwon kai,ta fitar mata da wani dan banzan lace cikin kayan da aka kawo mata dinkin skert da riga mai dogon hannu,kamar yadda ya qawatu lace din haka ya qawatata ta,babu abinda ta shafa banda turare mai da hoda amma sai ta fito cas gwanin sha'awa,fuskar ta tayi fayau ta dashe tare da ramar da tayi,naji ance amarya daban take ko batayi kwalliya ba,to kusan hakanne ya tabbata ga sumayya,komawa tayi ta kwanta abinta,don hayaniyar data cika gidan kadai ma damunta take bare ta waje,wanda tuni layin ya soma dinkewa,tana iya jiyo kwaroroto da muryar maroqa iri daban daban,sun baje hajarsu kowanne yana kwasar rabonsa,basa wasa da bikin daya shafi gidan professor mukhtar muhammad adam,don idan kazo a sa'a wani daga ranar ya daina roqo sai ya samu jarin da zai isheshi sana'a,ballantana yau da sunan almustapha ya bayyana baro baro na cewa shi zai sake aure.
Cikin qanqanin lokaci layin ya cika ya tumbatsa da jama'ar baabaa prof,jiniya iri iri ke tashi wadda ta qusoshin gwamnati ne da jami'an tsaro,kowa yana iya jiyo yadda daurin auren ke kayawa sakamakon maroqan dake bayyana dukkan abinda ke faruwa a wajen,auren zainab sulaiman gombe aka fara daurawa da angonta abulkhairi muhammad bala kan sadaki dubu talatin,sannan aka daura na halimatus sa'adiya sulaiman gombe da angonta abdur rahman Ahmad yusuf kan sadaki naira dubu hamsin,daurin auren qarshe shine na doctor muhammad almustapha professor mukhtar adam gombe wanda aka daura kan sadaki naira dubu ashirin,sai kuma kyautar mota duka cikin sadakinta take,daidai kunnenta nafisa tazo ta rangada guda,jin gudar take kamar ana zaqular qwaqwalwarta,saita dunqule ta cure waje daya,ta saki wani marayan kuka wamda bai fidda sauti,ita kadai yasan me take ji cikim zuciyarta,shikenan yau din ta sake zama mallakim wani bayan mukhtar?,wanin ma da baisan daraja ko qimarta ba,ya zata kaya musu?,ya zata kasance?,bata da amsar wannan.